Manomin Kenya ya lashe kyautar Naira miliyan 350 na Facebook

A makon jiya ne wani manomi dan kasar Kenya ya samu shiga cikin mutum biyar da suka yi nasara a  fadin duniya, wadanda kamfanin Facebook ya ba kowannensu Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 350). Manomin mai suna Noah Nasiali ya bude wani shafin Facebook ne mai suna Africa Farmers’ Club, wato Kulob din Manoman […]

Manomin Kenya ya lashe kyautar Naira miliyan 350 na Facebook

Noah Nasiali yana nuna yabanyar gonarsa

A makon jiya ne wani manomi dan kasar Kenya ya samu shiga cikin mutum biyar da suka yi nasara a  fadin duniya, wadanda kamfanin Facebook ya ba kowannensu Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 350).

Manomin mai suna Noah Nasiali ya bude wani shafin Facebook ne mai suna Africa Farmers’ Club, wato Kulob din Manoman Afirka, wanda ya samu tagomashi da karbuwa mai yawa a tsakanin al’ummar kasar.

Manomin shi ne kawai dan  Afirka da ya yi nasara aka zabe shi cikin jerin mutanen da suka samu kyautar Dala miliyan daya da Facebook din ya ware ta hanyar Shirin Jagoranci na Al’umma.

Kungiyar da Noah ya kafa tana taimaka wa manoma a sassan Afirka da dama wajen yada ilimin dabarun noma daban-daban da suka kai ga kara yawan albarkatun noma da riba.

Baya ga Mista Nasiali, akwai wadansu ’yan kasar Kenya biyar da suka shiga cikin jerin mutum 14 daga wasu kasashen Afirka da kowannensu zai samu Dala dubu 50, kuma sun bude shafukan Facebook ne da suke kokarin magance wasu matsaloli da duniyar manoma ke fuskanta a lokuta daban-daban.

A cikin wannan wata na Oktoba ne Facebook din zai shirya wani gagarumin biki ga wadanda suka yi nasarar a Jihar Kaliforniya da ke Amurka, kuma zai taimaka musu da karin horo da kayan aiki don inganta ayyukan nasu a Intanet da ma zahiri.