Manufar Zakzaky tabbatar da tsarin Allah: Martani ga Tanko Mani

A makon jiya, TANKO MANI ya baje kolinsa da mukalarsa mai taken ‘Makomar ’yan Najeriya a mahangar almajiran Malam Zakzaky.’ A yau kuma sai MALAM ABDULLAHI ISAH WASAGU (08074101247) ya aiko masa da martani kamar haka: Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah da Ya ba ni damar maida […]

Manufar Zakzaky tabbatar da tsarin Allah: Martani ga Tanko Mani
Manufar Zakzaky tabbatar da tsarin Allah: Martani ga Tanko Mani

A makon jiya, TANKO MANI ya baje kolinsa da mukalarsa mai taken ‘Makomar ’yan Najeriya a mahangar almajiran Malam Zakzaky.’ A yau kuma sai MALAM ABDULLAHI ISAH WASAGU (08074101247) ya aiko masa da martani kamar haka:

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah da Ya ba ni damar maida wannan martani.
To zan muhimnatar da jawabaina ne a kan kalmar “Siyasa” da shi Tanko ya zama jigon rubutun nasa na son rai, wanda har yake ganin wai shi ne ra’ayin almajiran Malam Zakzaky a kan makomar siyasar kasar nan.
Ina so mai karatu ya san cewa, ita wannan harkar ta tsiro ne tun bayan da shugabanta yana dan makaranta, wato tun bayan juyin-juya-halin Musulunci na Iran, kimanin shekaru 66 suka shude. Hakika wannan harka tana kan tafarki na jagoran juyin-juya-hali na kasar Iran a wannan karnin, wato Ayatullahi Khumaini. Hakazalika, harkar tana kan tafarkin nan da Shehu Usman danfodiyo (r.a) ya bi, ya jaddada tsarin Allah a wannan nahiya, kimanin shekaru 200 da suka shude. Ta haka ne ma makarantun da ke karkashin harkar suka dauki suna daya tilo na “Fudiyya” domin koyar da usulubin Shehu danfodiyo din.
Sannan babban hadafin da wannan harka ta Musulunci a Najeriya ta sanya a gaba shi ne, nenan mafita da uzuri wajen Allah Ta’ala. Wato neman yardar Allah da kuma sauke taklif shi ne babban hadafin wannwn harka, kamar yadda ya zo a Alkur’ani mai girma cikin, kissar Bani Isra’ila.
Don haka lokacin da mutum ya sami kansa cikin al’umma wadda ta bar tafarkin Allah kuma ta koma wata hanya ta daban, to lallai akwai amri-bil ma’aruf da nahyi anil munkar… gwargwadon halinsa da kuma mukaminsa. Wannan kuwa shi ne hadafin da wannan harka ta sa a gaba.
To amma da yake Tanko ya jahilci harkar kuma ya jahilci addininsa da kuma tarihin addininsa, sai ya fito yana fadin ra’ayinsa na cewa wai wannan siyasa ita ce kawai hanya daya tak da ta rage wa dan Najeriya, wanda zai iya kwato wa kansa ’yanci daga bakuncin da yake ciki. Har ma ya kawo wasu ka’idoji guda biyar na samar da sauyi na juyin-juya-hali irin na Musuluci.
To Tanko ya manta da tarihin Shehu Usman danfodiyo ne? Kashi nawa na ba’adin al’umma a zamaninsa suka mika mai bai’a? Sannan tsawon shekaru nawa ya kwashe yana kira zuwa ga bin tsarin Allah, kafin daga karshe Allah Ya ba shi nasara a kan dagutan zamaninsa? Idan da Tanko yana da ilimi da sanin tarihi, to da ya ji kunyar kawo wadannan ka’idoji biyar a rubutunsa.
Sannan fadinka na cewa, lallai sai mun shiga siyasa ne za mu iya ba da wata gudunmawa da yawanmu da muke da shi wajen kawo sauyi a wannan kasa. A nan ka ga ke nan, jahilcinka ya dada fitowa fili game da ka’idoji biyar din da ka kawo. Dalili kuwa, idan har yawa ne ke jawo nasarar juyi, to da Annabi Musa (a.s), Annabi Muhammadu (saw), Shehu danfodiyo (r.a), Imam Khumaini ba su samu nasara a kan dagutan zamaninsu ba.
Annabi Musa (a.s) da ya zo ya samu Fir’auna, ba shiga gwamnatinsa ya yi ba don ya kawo gyara, wa’azi yai musu a kan kaurace wa dagutu da kafircin zamaninsu, ya kira su a kan daukaka kalmar Allah da bauta masa Shi kadai.
To abin da ya kamata ku yi ke nan, ku da malamanku, ba bin azzaluman shuwagabannin wannan zamani ba da amsar miliyoyin Naira da nufin murguda fatawa, tare da goyan bayan zalinci ba. Kowa ya shaida yadda malamanku suka yi layi suna amsar miliyoyin Naira, wanda har daga baya ya kawo sabani a tsakaninsu. Ka ga ke nan, kowa ya shaida su waye dagutai tsakanin waziran Malam Ibrahim Zakzaky da kuma malamanku.
Ka ga a nan Annabi Musa bai shiga Gwamnatin Fir’ana ba don ya kawo gyara. A’a, komawa gefe ya yi, ya ja da shi kuma ya ci nasara a kansa. Kamar yadda manyan bayin Allah irin su Shehu danfodiyo da Imam Khumaini suka yi, kuma nasara ta kasance tare da su. Wannan kuma shi ne Usulubin Malam Zakzaky da waziransa suka tsaya kyam a kan wannan tafarki na kin goyan bayan zalunci da barranta daga zaluncin har lokacin da Allah zai tabbatar da al’amarinSa, ba kamar yadda azzaluman wannan kasa ke tafiya da malaman naku ba.
Idan muka koma zamanin Manzon Allah Muhammad (saw), za mu yi koyi da wani abu. Ai shi bai shiga gwamnatin su ba Abu Jahal ba, kai har ma sun yi tayin ba shi wani bangare na mulkin don kawai ya bar abin da yake yi, na kira amma ya ki yarda da haka. Kuma kin yarda da shiga gwamnatinsu bai hana shi kafa Gwamnatin Musulunci ba. Wannan haka yake ga Shehu Usman danfodiyo (r.a) da Imam Khumaini. Irin azabtarwar da dukkannin almajiransu suka sha a wurin azzaluman mahukuntan zamaninsu bai hana su tabbatar da tsarin Allah ba.
Kamar yadda ka ce, wai al’ummar kasar nan suna cikin yunwa da kishirwar samun sauyi, ga kuma irin yadda siyasar ta bana ta canza fasali amma duk da haka almajiran Malam Zakzaky suka yi kememe suka tubure. Ka ce, “To ko almajiran na Malam Zakzaky suna da wata hanya ta sauyi da ya dama wannan ya shanye? Ba su da shi. Kuma tsawon shekaru 36 harkar na ikirarin kawo sauyi amma har yanzu ba su da kammalalliyar manhaja wadda zai zama musu alkiblar bi idan sun samar da sauyin.”
To a nan ma ka ga jahilcinka ya dada fitowa fili, domin ka jahilci addininka ma ballantana ra’ayin almajiran Malam Zakzaky.
Shin mene ne siyasa ne? Mene ne ma’anar siyasa a ra’ayin masana siyasar?
Babban abin da ya kamata mu tambayi kanmu, ni da kai da kuma masu karatu shi ne, to don Allah a wannan siyasa da ake yi a kasar nan ta Musulunci ce? Kuma ta yi daidai da tsarin Allah? Kuma ita Allah ya ce a yi? Kuma mene ne hukuncin wanda ya yi wani abu da ba Allah Ya ce a yi ba, musamman siyasa?
Na’am, mu alamajiran Malam Zakzaky ba wai mun ce babu siyasa ba ne a Addini. A’a, hasali ma sai da siyasar ake iya tafiyar da wasu al’amura da suka shafi addini. Amma mu za mu yita ne bisa tsarin addini ba bisa tsarin irin siyasar Najeriya ba.
Duba littafin ‘Al-Imama Wassiyasa’ mana, na magabatan malamanmu na Shi’a dangane da yadda siyasa take a addini. Ba kamar yadda ka gandara karyar cewa wani wai Malam Jafar Nasir yai ta kawo mana misalan da za mu ba da gudunmawa a siyasar Najeriya, har da kara karya a kan karya cewa, wai har Malam Jafar Nasir ya kawo mana hujjoji na maganganun malamanmu na Shi’a cewa, “Sun yarda za a iya yin siyasa wadda ba ta tafarkin addini.” To ka ga a nan, kai da malaminka Jafar Nasir, duk duhun jahilcinku ya dada bayyana.