Manufofin Gwamnatin Tinubu ne silar taɓarɓarewar rayuwa a Najeriya —ACF
Kullum suna fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi.
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta koka kan yadda wasu manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke haddasa taɓarɓarewar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi a Najeriya.
ACF ta kuma yi gargaɗin cewa Najeriya na iya fuskantar ruɗanin zamantakewa, musamman a yankin Arewa idan ba a yi wani abu ba don magance taɓarɓarewar tattalin arziki.
Ƙungiyar ta ACF ta bayyana hakan ne bayan yin taron majalisar zartarwa ta ƙasa da ta gudanar a Kaduna ranar Talata.
Ta ce ta lura cewa ana a ci gaba da rayuwa cikin wahala da ƙalubale, inda kullum talakawan Najeriya ke fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi, da saurin taɓarɓarewar rayuwa tare da tashe-tashen hankula, aikata ta’addanci da kuma barazanar ‘yan bindiga.
- ’Yan kwadago sun yi watsi da tayin mafi karancin albashin N54,000
- Yakin aiki: Ba gudu ba ja da baya —Kungiyoyin Kwadago
A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar kuma ya sanya wa hannu, ya koka da yadda matsalolin suka ci gaba da taɓarɓarewa a wasu wurare musamman a Arewa.
Ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a kan cire tallafin man fetur, da kuma haraji da gwamnatin tarayya ta yi, yana mai cewa waɗannan manufofin ne ke haifar da raguwar walwalar yanayin rayuwar ’yan ƙasa.