Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya — Tinubu

Shugaban ƙasa ya kuma ce kasafin kuɗin 2025 zai mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci.

Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya — Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin arziƙin Najeriya na samun farfaɗowa sakamakon manufofin gwamnatinsa.

Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zauren majalisar dokoki ta ƙasa.

Ya ce gwamnatinsa tana ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙi ta hanyar kashe kuɗaɗe a wuraren da suka dace ba tare da haifar da hauhawar farashi ba.

“’Yan Najeriya za su shaida an samu ci gaba a tattalin arziƙi kuma nan ba da jimawa ba abubuwa za su sake daidaita,” in ji Tinubu.

Hakazalika, ya jaddada cewa akwai alamu masu kyau da suka shafi ci gaban tattalin arziƙin duniya da kuma ƙaruwar ajiyar kuɗin kasar waje.

Ya ce an yi hasashen samun bunƙasar tattalin arziƙin duniya a 2025, wanda zai kasance kashi 3.2 cikin 100, amma Najeriya ta zarce wannan hasashen.

“Tattalin arziƙinmu ya ƙaru zuwa kashi 3.46 cikin 100 a zangon uku na shekarar 2024, idan aka kwatanta da kashi 2.54 cikin 100 a zango na uku na 2023,” in ji shi.

“Ajiyar kuɗinmu na ƙasar waje ya ƙaru zuwa kusan dala biliyan 42, wanda ya bayar da kariya mai ƙarfi ga Najeriya daga matsalolin tattalin arziƙin duniya.

“Bugu da ƙari, ƙaruwar kayayyakin da muke fitarwa zuwa ƙasashen waje ya sa mun samu rarar cinikayya mai darajar Naira tiriliyan 5.8, kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana,” in ji shi.

Ya bayyana waɗannan nasarorin a matsayin hujja ta yadda tattalin arziƙin Najeriya zai bunƙasa ta hanyar tasirin manufofin gwamnatinsa.

“Wannan sakamakon na nuna tasirin manufofin da muka ɗauka tun daga farko,” a cewarsa.

Shugaban ƙasa ya kuma ce kasafin kuɗin 2025 zai mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci, irin su tsaro, samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa, ababen more rayuwa, da kuma inganta ƙasa.

“Wannan kasafin kuɗin ba kawai zai magance matsalolin yanzu ba ne, zai kuma gina ginshiƙin ci gaban Najeriya nan gaba,” in ji shi.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja