Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (8)
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jin kai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina […]
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jin kai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne. Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, mun dakata bayan mun gabatar da bayanin cewa ba a shar’anta azumi na musamman ba a watan Rajab ko wata ibada ta dare kebance. Bayani ya gabata, wanda, in Allah Ya so, zai kasance ya wadatar dangane da kore abin da mafi yawan gama-garin mutane suke dauka game da muhimmancin yin azumi a cikin watan Rajab. Wani lamarin ma shi ne da yawa, mutane sukan kama azumi tun farkon Rajab din, ba za su daina ba, sai karshen Ramadan, wato su yi azumin watanni uku a jere. Ba wata shari’a da ta ba da damar yin wannan irin aiki na ibada, balle har a yi zaton za a samu wata lada, musamman ma da yake Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya aikata wani aikin da babu umurninmu a cikinsa, to an mayar masa.” (Muslim ne ya ruwaito shi).
Yau, kamar yadda muka fada a makon jiya, za mu yi magana ne a kan:
Hukuncin kebantar ranar Asabar da azumi
An samo daga Abdullah bn Busr daga ’yar uwarsa (Allah Ya yarda da su) cewa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Kada ku azumci ranar Asabar, sai dai abin da aka farlanta muku, kuma ko da waninku bai samu abin da zai ci ba, sai ganye (lingabu) ko wani bawon itaciya to, ya tattauna shi.” ‘A’imma’ (magabata) sun illanta wannan Hadisi, wanda Abu Dawud, Hadisi na 2,421 da Tirmizi, Hadisi na 744 da Annasa’iy a cikin Alkubra, Hadisi na 2,762 da Ibnu Majah, Hadisi na 1,726 da Ahmad, mujalladi na 6, Hadisi na 368 suka fitar. Kuma Malik ya ce, “Kazibun” -karya ne. Kuma Abu Dawud ya ce, “Mansukhun” (An shafe shi -wato ba a aiki da shi). Kuma Hafiz ya ce, “Muddaribun” (Mai raurawa ne). Kuma Addahawi ya ce, “Shazun” (wato akwai wanda ya fi shi karfi). Haka nan ma Shaihul Islam (Ibn Taimiyya) ya ce da kuma waninsu. “Ni ma (Abu Malik) na yi magana a kansa a cikin ta’alikin da na yi wa littafin ‘Sharh Almanzumat Albaikuniyyah’ na Bn Usaimin, a shafi na 24.
Lallai ma’abuta ilimi sun yi sabani a cikin fikihun wannan Hadisi a cikin zantuttuka biyu:
Na Farko: Halaccin azumtar ranar Asabar a matsayin tadawwu’i ko da an kebance ranar ne. Wannan kuwa mazhabar Malik ce, kuma an fahimci haka daga kalamin Ahmad. Kuma Ibnu Taimiyya da Ibnu kayyim sun zabi wannan ra’ayi. (Al’insaf, mujalladi na 3, shafi na 347; da Iktisadus Siradil Mustakim, mujalladi na 2, shafi na 575; da Mukhtasar Assunan, mujalladi na 3, shafi na 298). Su wadannan malamai sun raunana Hadisin, kuma suka gabatar da hadisai sahihai wadanda suke kwadaitar da azumtar Arfa da azumin shida a watan Shawwal da Ashura da kwanukan haske kowane wata (wato 13, 14 da 15 ga wata) da wanda yau a yi azumi, gobe a sha (azumin Annabi Dauda, Alaihis Salam). Suka ce, babu makawa wani daga cikin wadannan ranaku su dace da ranar Asabar.
Haka nan sun kawo Hadisin yin azumi gabanin ranar Jumu’a ko ranar da ke bin ta a zancen da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi wa Juwairiyya (Allah Ya yarda da ita) cewa, “… Kina da nufin yin azumi gobe..?.” Dukan wadannan dai bayaninsu ya gabata a cikin mukalolin da suka wuce.
Na Biyu: Karhancin kebance ranar Asabar da azumi. Wannan kuwa mazhabar jamhurun malamai ce, wato a Hanafiyya da Shafi’iyya da Hambaliyya. (Almajmu’u, mujalladi na 6, shafi na 347 da Albada’i’i, mujalladi na 2, shafi na 79 da Almughni, mujalladi na 4, shafi na 428).
Su kuma sun dauki wannan Hadisin a matsayin hani ne wajen kebantar Asabar da azumi, saboda yin hakan ya yi kamanceceniya da Yahudawa, kuma sun karfafa wannan magana da abin da aka ruwaito daga Ibn Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa Ummu Salama ta ce, “Lallai mafi yawan abin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana azumta daga cikin kwanuka, su ne ranakun Asabar da Lahadi.” Kuma ya kasance yana cewa, “Su (Asabar da Lahadi) ranaku ne na Idi ga mushrikai, kuma ni ina nufin in saba musu ne.” Da’ifin Hadisi ne da Annasa’i a cikin Alkubra, Hadisi na 2,776 da Ahmad, mujalladi na 6, Hadisi na 323 da waninsu suka fitar da isnadi mai rauni.
“Na ce (Abu Malik, Sahih Fikhus Sunnah, mujalladi na 2, shafi na 131), “Amma Hadisin Abdullah Ibn Busr, lallai zantukan magabata sun yawaita a kan illanta shi, saboda haka babu damuwa (abin zargi) a kan azumtar ranar Asabar, musamman dai idan ta yi muwafaka da ranar da shari’a ta soyar da azumtarta. Allah Shi ne Mafi sani.”
Karhancin azumin sabi-zarce
Azumin sabi-zarce makaruhi ne da kuma biyar da wani a bayan wani, ba tare da yin sahur ko buda-baki ba, saboda zancen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), “Ina gargadinku da sabi-zarcen azumi” – ya fadi haka sau uku. Sai (sahabbai) suka ce, “To ai kai kana yin haka ya Ma’aikin Allah?!” Sai ya ce, “Ku, a cikin wannan al’amari ba kamar ni kuke ba, ni ina wayar gari Ubangijina Yana ciyar da ni Ya shayar da ni, ku wadatu da ayyukan da kuke da iko a kansu.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,966 da Muslim, Hadisi na 1,103 suka fitar daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi).
Sai dai idan mutum ba zai samu matsuwa ba, to yana iya yin sabi-zarcen har zuwa lokacin sahur kadai, saboda fadin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), “Kada ku yi sabi-zarcen azumi. Duk wanda yake son ya yi sabi-zarce to, ya yi har zuwa lokacin sahur.” Sahihin Hadisi ne na Buhari, Hadisi na 1,967 da Abu Dawud, Hadisi na 2,344.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya kawo mu karshen abin da za mu iya gabatarwa dangane da bayanin azumin nafila bayan na Ramadan. Allah Ya sa abin da aka gabatar ya zama mai amfaninmu nan duniya da kuma Lahira don girman ZatinSa. Sai kuma makon gobe, in Allah Ya kai mu, za mu yi tsokaci kan Layya da abin da ya shafi Sallar Idi, saboda abin da ya fuskanto mu.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!