Manuniya kan ladubban yin addu’a (2)

  Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da […]

Manuniya kan ladubban yin addu’a (2)
Manuniya kan ladubban yin addu’a (2)

 

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.  
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa data ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun kwana a karkashin wannan mukala, a daidai inda muka gabatar da bayani kan abin da shaihin malami  Al’imamu Abiy Alkasim Alkushairiy, Allah Ya jikan shi, ya yi nuni a kansa, inda ya ce, “Yana daga sharuddan (samun karduwar) addu’a, ya kasance abincin mutum halal ne.” Sannan aka kawo dalili a kan haka na daga hadisin da Imam Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa, hadisi na 1,015, cikin zakkah, babin kardarta daga abin da aka samu mai tsarki (na halal). Sai kuma manuniyar da wani daga cikin magabata, Yahya bn Mu’az Arraaziy, Allah Ya jikan shi, ya yi, inda yake ce wa Allah, “Yaya za a yi in rokeKa, alhali ni mai sado ne? Kuma yaya za a yi ba zan rokeKa ba, alhali Kai, Mai karimci (Kariimi) ne?”
To, yau ga ci gaba:
Haka nan yana daga cikin ladubban addu’a, mutum ya halarto da zuciyarsa (a kan abin da yake addu’ar kansa, kada ya koma kan tunanin wani abu daban).
Wani sashe na magabata ya ce, “Manufa game da addu’a shi ne bayyanar da bukatuwa ga abin da ake nema, in kuwa ba haka ba, to da ma dai Allah, Mai tsarki, Madaukaki, Yana aikata abin da Ya so.
Al’imam Abu Haamid Alghazaaliy, a cikin littafinsa ‘Al’ihyaa’u’ ya ce, “Ladubban addu’a guda goma ne,”:
(1) Mutum ya tsinkayi lokuta masu martaba, kamar ranar Arafah; da watan Ramadan; da ranar Jumu’a; da sulusin (dayan ukun) dare na karshe; da kuma lokacin sahur.
(2) Ya ganimantu (yin amfani da dama da ake samu) a yayin da yake cikin halaye masu martaba da daukaka da daraja, kamar lokacin sujada (yayin da bawa ya fi kusa da Mahaliccinsa); da kuma lokacin da rundunar mayaka (don daukaka kalmar Allah) ta yi arangama da abokan gaba; da lokacin saukar ruwan sama; da (kafin) tsayar da sallah (tsakanin kiran sallah da ikama) da kuma bayan tsayar da ita (addu’ar bude sallah).
A karkashin wannan gada ne sai Malam Nawawiy ya ce, “Na ce, ‘da daidai lokacin da zuciya ta yi laushi’ (ta yi tawali’u, ta halarto da girma da matsayin Allah, Wanda ake da bukatuwa zuwa gare Shi).”
(3) Ya fuskanci alkibah (wajen da Ka’aba take) da daukaka hannaye (na roko) kuma ya shafa fuskarsa a karshen addu’ar. [Kodayake duk hadisan da suka yi nuni da a shafa fuska bayan addu’a masu rauni ne – Allah Shi ne mafi sani!]
(4) Ya kankanta sautin addu’a, wato ya yi ta tsakanin doyewa da bayyanawa – wato rada-rada ke nan!
(5)  Kada ya yi ta da ‘saja’u’, wato sauti mai kamar karatu-karatu, waka-waka. Kuma lallai an fassara wannan manufa da ‘I’tida’i’, wato ketare iyaka a cikin addu’a, saboda haka ana ji wa mai yin haka tsoron sada wa ka’ida.
Wani sashe na magabata ya ce, “Ka roka da harshen kaskanci da nuna bukatuwa, ba da harshe na fasaha da wata kwaskwarima ko iya-yi ba”. Kuma ana cewa, “Lallai su malamai da masu shiryarwa zuwa ga alheri, ba su karawa, a cikin addu’a, a kan kalmomi bakwai. Wannan kuwa yana samun shaida daga abin da Allah, Mai tsarki, kuma Madaukaki Ya ce, a karshen surar Bakarah…“Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu da laifi in mun yi mantuwa ko mun yi kuskure (1).  Ya Ubangijinmu! Kuma kada Ka dora mana wani nauyi irin yadda Ka dora shi a kan wadanda suke kafinmu (2). Ya Ubangijinmu! Kuma kada Ka dora mana abin da ba mu da iko a kansa (3), kuma Ka yi mana afuwa (4), kuma Ka yi mana gafara (5), kuma Ka jikanmu (6)! Kai ne Majidincin lamarinmu, don haka Ka taimake mu a kan mutanen da suke kafirai (7).” Aya ta 286.
“Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, bai ba da labari a wani wuri na dangane da addu’o’in bayinSa, abin da ya fi wadannan kalmomi bakwai ba.”
Na ce (inji Imamun Nawawiy), “Kuma kwatankwacin wannan shi ne fadinSa, Mai tsarki, Madaukaki, a cikin Surar Ibrahim, Alaihis Salaam, inda Yake cewa, “Ka ambata, a lokacin da Ibrahim ya ce: Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari amintacce, kuma Ka nisanta ni, ni da ’ya’yana daga bauta wa gumaka (1). Aya ta 35.
“Ya Ubagijina! Lallai ne su, sun datar da masu yawa daga mutane. Sa’an nan wanda ya bi ni, to lallai shi, yana daga gare ni, kuma wanda ya sada mini, to lallai Kai Mai gafara ne, Mai jinkai (2).” Aya ta 36.
“Ya Ubangijinmu! Lallai ne ni, na zaunar da zuriyyata ga rafi wanda ba ma’abucin shuka ba, a wurin dakinKa, mai alfarma (3). Ya Ubangijinmu! Domin su tsayar da sallah. Sai Ka sanya zukata daga mutane suna gaggawar begen zuwa gare su, kuma Ka azurta su daga ’ya’yan itace, mai yiwuwa ne suna godewa (4).” Aya ta 37.
“Ya Ubangijinmu! Lallai ne Kai, Kana sanin abin da muke doyewa da abin da muke bayyanawa.  Kuma babu abin da yake doyewa ga Allah, daga wani abu a cikin kasa, kuma babu a cikin sama (5).” Aya ta 38. Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya ba ni, ina a cikin tsufa, Isma’ila da Is’haka. Lallai ne Ubangijina, hakika, Mai jin addu’a ne.” Aya ta 39.
“Ya Ubangijina! Ka sanya ni mai tsayar da sallah, kuma daga zuriyyata. Ya Ubangijinmu! Kuma Ka karda addu’ata (6).” Aya ta 40.
“Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara gare ni, kuma ga mahaifana, kuma da muminai, a ranar da hisabi yake tsayawa (7).” Aya ta 41.
Na ce (inji Imamun Nawawiy), “Kuma abin da yake zadadde a wajen jamhurun (mafi yawan) malamai shi ne babu wani hani ko takaitawa a kan lamarin. Hasali ma babu wani karhanci (hani, abin ki) a game da kari a kan jeri bakwai din nan, sai ma dai abin so ne (mustahabbi) a yawaita a cikin roke-roken da ake yi wa Allah, a yanke, ba tare da kaidi ba.”
(6) Ladabi na shida shi ne mutum ya kasance yana tawali’u (marairaita) da khushu’a (kankan da kai) da nuna kauna da tsoro da bege da nacewar nuna bukatuwa don kaiwa ga cin nasarar samun abin da aka sa a gaba, ana nema wajen Mai abin.
Bari dai mu dakata a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya nufe mu da kaiwa za mu ci gaba.  Wassalamu alaikum warahmatullaahi wabarakaatuh!