Manuniya kan ladubban yin addu’a (3)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallaahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallaahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun kwana bayan mun gabatar da ladubban addu’a guda biyar daga cikin goman da Imamu Abu Hamid Alghazaliy ya jera a cikin littafinsa Al’ihyaa’u. Yau za mu fara ne daga ladabi na:
(6) Shi ne mutum ya kasance yana nuna tawali’u (marairaita) da bayyana khushu’i (kankan da kai) da nuna kauna da tsoro da bege da nacewar kwadayin bukatuwa don kaiwa ga cin nasarar samun abin da ake nema wajen Mai abin (Allah).
Allah Ta’ala Ya ce, “…Lallai ne su, sun kasance suna tsere zuwa ga ayyukan alheri. Kuma suna kiran Mu a kan (cikin) kwadayi da fargaba (tsoro). Kuma sun kasance, gare Mu, suna masu khushu’i (kankan da kai).” Surar Ambiya’i, aya ta 90.
Haka nan kuma Allah Ta’ala Ya ce, “Ku kirayi Ubangijinku da kankan da kai da kuma a boye…” Surar A’araf, aya ta 55.
(7) Ya dage a kan neman biyan bukatarsa, kuma ya ba zuciyarsa tabbacin samun karbuwa, kuma ya gaskata kwadayinsa a cikinta (karbuwar da addu’ar), alhali dalilan haka din suna da yawa kuma sun shahara.
Sufyan bn Uyainah (Allah Ya yi masa rahama), ya ce, “Kada dayanku ya hanu da yin addu’a dangane da abin da ya sani ga kansa (bukatarsa), domin Allah Ta’ala Ya karba wa mafi sharrin halitta – Iblis – a lokacin da ya ce, ‘(Ya Ubangiji), Ka yi mini jinkiri zuwa ranar da ake tayar da su.’ (Allah) Ya ce, “Lallai ne, kana daga wadanda aka yi wa jinkiri.” Surar A’araf, aya ta 14-15.
A karkashin wannan aya, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma (Hausa) a shafi na 221, ya ce, “Wannan ya nuna cewa, kowa ya roki Allah wani abu, to Zai ba shi gwargwadon yadda Yake so (Shi Ubangijin).”
(8) Ya nace cikin addu’ar kuma ya (rika) maimaita ta sau uku, kada ya yanke kauna wajen (fatar) a karba masa.
(9) Ya bude addu’ar da ambaton Allah, Madaukaki, ta fuskar yabonSa da girmama Shi da yi maSa kirarin da ya dace da Shi.
Na ce (in ji Imamun Nawawiy), “Haka nan kuma da yin salati ga Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam), bayan godiya ga Allah Ta’ala da yabo a gare Shi. Sannan kuma ya kare (kammala) addu’ar da yin salatin da kuma godiya da yabon Allah Ta’ala din dai.
(10) Wanda shi ne mafi muhimmanci a cikinsu kuma shi ne ma asali ko tushe wajen samun karbuwar addu’ar. Wannan kuwa shi ne tuba da mayar wa duk wanda aka zalunta, kayansa da kuma ainihin fuskanta (komawa, dogaro) zuwa ga Allah Ta’ala, Wanda Shi kadai ake nema daga gare Shi, domin Shi kadai ke da abin bayarwa. Duk wanda ba Shi ba, sanadi ne na bayarwar ko hanawa.
Addu’a tana sanadin tunkude bala’i: Daga nan sai Al’imam Abu Hamid Alghazaliy ya ce, “To, yanzu idan aka ce, ‘mece ce fa’idar yin addu’a, alhali duk abin da aka kaddara, ba a mayar da shi ko a gusar da shi, yaya ke nan?”
Ya ce, “To, ka sani, cewa cikin dukkan abin da aka kaddara aukuwarsa (wato abin da Allah Ya hukunta), akwai korewar bala’i cikinsa, idan an yi addu’a. Saboda haka ita addu’a tana zama sababi (sanadi) wajen kore (tunkude) bala’i da kuma samar da rahama (jinkai), kamar dai yadda garkuwa take sanadi wajen kare ko tunkude makami; kuma kamar ruwa ne da yake sanadin fitar tsirrai daga cikin kasa.
“Haka lamarin yake kuwa, domin tunda garkuwa ko kwalkwali ko sulke suke hana makamai (kibiya da mashi da takubba ko makamantansu) su kai ga samun jiki, to kamar haka ne tsakanin addu’a da bala’o’i. kuma babu wani sharadi dangane da ganewa ko sanin abin da Allah Ya hukunta (wato kaddara), cewa mutum ba zai yi amfani da garkuwa ko makamantanta, don kare kansa daga farmakin makamai ba.
“Kuma lallai Allah Ta’ala Ya fadi (dangane da rikon garkuwa ko abin da zai kare mutum daga wani farmaki), cewa, “….Kuma su riki shirinsu (kayan kariya) da makamansu…” Surar Nisa’i, aya ta 102. Kuma alhali duk da haka Allah Ya kaddara aukuwar kowane al’amari (dangane da abin da zai auku), kuma Ya kaddara sanadinsa.
“A cikin wannan dangane na daga fa’idojin da muka ambata, akwai al’amarin halarto da zuciya da tabbatar da natsuwa da fuskanta zuwa ga abin da ake nema da nuna kwadayi da kuma kankan da kai ga Wanda ake nema daga gare Shi, wadanda su ne matuka wajen ibada da bin abin da aka sani na shari’a. Allah Shi ne Mafi sani!”
Ana Tawassuli da aikin alheri: An ruwaito cikin sahihin Hadisin da Buhari da Muslim suka fitar daga Abdullah dan Umar, Allah Ya yarda da su, dangane da wasu mutum uku matafiya da suka fake a cikin kogo, dutse ya toshe musu bakin kogon. Ya ce, ‘Na ji Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Wasu mutum uku, daga jam’ar da ta gabace ku, sun yi tafiya har sai da suka kai wani kogo, suka shiga cikinsa don su kwana, amma sai wani katon dutse ya gangaro ya toshe bakin kogon, sai suka ce, ‘Lallai ba abin da zai fitar da ku cikin wannan kogo, sai dai kowanenku ya roki Allah Ta’ala da kyawawan ayyukansa’…. Sai kowanensu ya yi roko da mafi kyawun aikin da yake ganin ya yi shi don Allah, sai ya ce, “Ya Allah, in na yi wannan aiki don neman yardarKa, Ka bude mana hanya mu fita.” Da haka aka yi ta gusar da dutsen nan har ya kai yadda za su iya fita, suka fita suka ci gaba da tafiyarsu.”
Wannan Hadisi shahararre ne, kuma ya tara al’amura da darussa masu yawa a cikinsa, wadanda suka hada da nuna rangwame da tausayi ga iyaye da tunkudewar abubuwan da aka hana (haram), musamman ma a yayin da ake da iko da damar yin su, amma aka hanu da falalar yin biyayya ga iyaye da halaccin yin ijarar aiki (wato yin kwadago) da kyautata cika alkawari da mayar da amana ga mai ita da yin sauki da rangwame a cikin mu’amala. Kai, a cikin Hadisin akwai abin da ke nuni zuwa ga karamomin waliyyan Allah da dai wanin wadannan fa’idoji da darussan da malamai suka fitar a cikinsa. Idan wata dama ta samu, in Allah Ya so, za a gabatar da Hadisin kamar yadda yake.
Nan za mu dakata, sai wani makon, in Allah Ya kai mu, za mu gabatar da wani abin da ya saukaka na daga nasiha ga Musulmi. Allah Ya ba mu dacewa, amin!
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!