Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Madalla da Allah, Wanda Ya sanya laushin zukata a cikin yawaita yi maSa da’a, kuma muna neman tsarinSa daga kutsawa cikin saba maSa, wanda ke sa kekasar zuciya.Tsira da Amincin Allah su […]

Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya
Manuniya Kan Sinadaran Da Ke Tausasa kekasar Zuciya

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Madalla da Allah, Wanda Ya sanya laushin zukata a cikin yawaita yi maSa da’a, kuma muna neman tsarinSa daga kutsawa cikin saba maSa, wanda ke sa kekasar zuciya.Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau, cikin yardar Allah, mukalarmu za ta leka ne cikin littafin nan dai da Dokta AbdulMuhsin bn Muhammad Alkasim, limami kuma mai huduba a masallacin Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasallam), a Madina kuma alkali, ya wallafa mai sunan Khuduwatun Ilas Sa’adah. Za mu ga wani abu daga cikin sinadaran da za su taimaka a warware kekasar zuciya, su sa ta yi taushi da laushi. Allah Ya taimaka mana,Ya ba mu ladar abin da yake daidai, Ya gafarta mana abin da yake kurkure ne, amin.
Warwara game da kekasar zuciya:
Ita zuciya tana jujjuyawa ne a cikin wannan rayuwa tamu, a tsakanin kekashewa (bushewa) da kuma laushi (sanyi). A duk yayin da ta gangara wajen kekasar da kuma sabo, sai ta kasance a bushe, ba ta ko waigawa wajen abin da yake rangwame ne da tausayi da sanyayawa, amma kuma idan bawa ya kutsa cikin al’amarin yin da’a wajen bin umarnin Mahaliccinsa, to sai (zuciyarsa) ta yi laushi ta karkata wajen jin tausayi da rangwame a cikin dukkan al’amurran mu’amalarsa ta rayuwa.
Shi sanadin kaushin zuciya da daskarewarta da kekasarta, yana kasancewa ne daga nisantar Allah, Mai girma da daukaka. Idan zuciya ta fada cikin wahalar zunubi (sabon Allah), lallai wajibi ne a kan bawa kada ya amince wajen sallama mata ta fuskar kasancewa cikin wannan dagwalo da kazanta. Abin da yake tilas (wajibi) a gare shi ne yin gaggawar wanke wannan dauda da kazanta, wadda ta liku da zuciya, ta fuskar komawa ga Allah da kusanta zuwa gare Shi da neman yardarSa. Lallai Allah Ya yi yabo ga abokinSa, saboda dabi’arsa ta dauwamammiyar komawarsa gare Shi; da kuma yawaitar hakuri da mayar da al’amari gare Shi, cikin addu’a; sannan da kusanta zuwa gare Shi, a cikin kowane halin da yake ciki. Allah Mai girma da daukaka, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, Ya ce, “Lallai Ibrahim, hakika mai hakuri ne, mai yawan addu’a, mai tawakkali (dogaro da Allah).” Suratu Hud, aya ta 75.
Yana daga cikin mafi gaggawar sabubban magance bushewar zuciya, abin da yake biye kamar haka:
(1) Yawaita Zikirin  Allah:
Shi wannan zikirin Allah (ambato, tunawa, kiyayewar Allah) sau da yawa yana jawo farinciki da walwalar zuciya da arziki da muhabba (tsoron-kauna, ta yadda mutum zai guji abin da zai bata wa wanda yake kauna din), kuma ya wajabtar da kiyaye Allah da ji a jika cewa ko’ina mutum yake Allah Yana jinsa da ganinsa, a kodayaushe kuma a kowane irin hali (abin da ake kira murakaba).  
Haka nan (zikirin Allah) yana taimakawa wajen yawaita bautar Allah da neman kusanta zuwa gare Shi da fadanci don a samu shiga da karbuwa a wajenSa, Subhanahu Wata’ala, kuma shi zikirin Allah wani sanadi ne na samun kubuta daga azabar Allah.
MalamMakhul (Allah Ya yi masa rahama), yana cewa, “Zikirin (ambaton) Allah magani ne, kuma ambaton mutane cuta ne.”  Wani mutum ya je wajen Hasan Albasriy ya ce masa, “Ina kawo maka karar kekasar zuciyata.”  Sai (Hasan Albasriy) ya ce masa, “Lausasa (jika) ta da zikirin Allah.”
Ana samun daukakar darajoji da zikirin Allah; kuma ana gafarta kura-kurai (zunubai); kuma ana tunkude cututtuka da bala’o’i; kuma ana kuranyewar bakin ciki da takaici; ana saukake masibobi masu tsananin zafi da radadi. Haka nan ana yalwata kiraza, wato zukata na budewa su karbi abubuwa masu yawa cikin nishadi da walwala, ba tare da an samu wata damuwa mai cutarwa ba, kuma a samu natsuwar zuciya din a cikin mafi yawan al’amurran rayuwa. Wannan kuwa ya dace da abin da Allah Mai girma da daukaka Yake cewa, a cikin Surar Ra’ad, aya ta 28, “Wadanda suka yi imani, kuma zukatansu sukan natsu da ambaton Allah. To, lallai da ambaton Allah zukata suke natsuwa.”
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, (Allah Ya jikansa), a cikin littafinsa Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma Zuwa Harshen  Hausa, a karkashin wannan aya, a shafi na 367, ya ce, “Ambaton Allah shi ne hukunce-hukuncenSa ga komai. Umar dan Khaddaab (Allah Ya yarda da shi), ya ce, ‘Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umarninSa ko haninSa. Wanda yake yin zikirin baki ba da yana aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibadarsa da mu’amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sunan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.’”
Sannan shi yin zikirin nan, wata wasiyya ce ta Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ga wanda ya nemi (shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi masa wasiyyar, inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce masa, “Kada ka bari harshenka ya bushe daga zikirin Allah, wato manufa koyaushe ka kasance harshenka yana jike da ambaton Allah.” Imamut Tirmiziy ne ya ruwaito wannan Hadisi.
Da ambaton (zikirin) Allah zukata suke rayuwa (su bunkasa), su yi walwala da yabanya da huranni masu ban sha’awa, babu kunci, babu kyashi da sauran munanan abubuwa. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Kwatankwacin wanda yake ambaton Allah da wanda ba ya ambaton Allah, kamar rayayye ne da matacce.” Imam Buhari ne ya ruwaito Hadisin.
Kuma lallai duk wanda ya san girma da daukakar Allah, to shi ne wanda yake yawaita ambaton Allah (zikirinSa), kuma shi yawaitawa a cikin zikirin Allah wata alama ce ta kasancewar mutum mai gaskiya tare da Allah.
Idan kana son yalwatattar magana dangane da muhimmanci da matsayin zikiri wajen gyara da tausasa zukata, sai ka koma ga wasu daga cikin littattafan da Ibnul kayyim Aljauziyyah ya wallafa kamar Jami’ul Ulum Wal Hikam ko HilyatulAuliya’i ko Jala’al Afham ko kuma Mi’atu Fa’idatin Min Fawa’idiz Zikri. Allah Ya ba mu dacewa!
Ina  ganin bari mu dakata a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya nufe mu da kaiwa, za mu ci gaba da wannan mukala da sinadaran tausasa kekasar zuciya.
 Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh!