Manya dibar fari: Tarihin Rupert East, tsanin Adabin Hausa (1)
Sunan Littafi: Rupert Moultrie East 1898-1975: Tarihinsa Da Sharhi A Kan Gudunmawarsa Ga Adabin Hausa (Juzu’i na 1) Marubuciya: Aliyah Adamu Ahmad Kamfanin Wallafa: Whales Adberts Limited, Kaduna Shekara Wallafa: 2017 Yawan Shafuka: 360 Kowa ya san Alhaji (Dakta) Abubakar Imam. Idan ba ka san shi ba, ballantana […]
Sunan Littafi: Rupert Moultrie East 1898-1975: Tarihinsa Da Sharhi A Kan Gudunmawarsa Ga Adabin Hausa (Juzu’i na 1)
Marubuciya: Aliyah Adamu Ahmad
Kamfanin Wallafa: Whales Adberts Limited, Kaduna
Shekara Wallafa: 2017
Yawan Shafuka: 360
Kowa ya san Alhaji (Dakta) Abubakar Imam. Idan ba ka san shi ba, ballantana kuma a ce ba ka taba jin sunansa ba, to ba ka san tarihin Adabin Hausa ba; sannan ba ka karanta littattafan Hausa irin su ‘Ruwan Bagaja’ da ‘Magana Jari Ce’ ba, wadanda Imam din ya rubuta.
To amma ba kowa ba ne ya san wani mutum mai suna Dakta Rupert Moultrie East; wanda ma ya san shi din, to sanin shanu ya yi masa. Shi dai R.M. East, kamar yadda aka fi saninsa, Bature ne dan kasar Ingila wanda ya zauna a Najeriya a zamanin mulkin mallaka. Ya yi aikin koyarwa tare da rike mukamai a Ma’aikatar Ilimi. To amma ban da aikin da ya yi a fagen ilimi, inda ya fi yin tasiri da suna shi ne fagen talifi da adabi. East shi ne malamin Abubakar Imam a wannan fage, domin kuwa shi ne wanda ya koya masa dabarun rubuta kirkirarren labari da ma wanda ba na kirkira ba. Shi ne tsanin da Imam ya hau ya kai kololuwar daukaka ta yadda ya kasance babu marubucin Hausa kamarsa har ya zuwa yau din nan.
Marubuciyar wannan littafin, Dakta Aliyah Adamu Ahmad, malama ce a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar Jihar Sakkwato. Shi littafin, ya samu ne sakamakon aikin nazari da ta yi na neman digiri na uku a Jami’ar Bayero, Kano kuma Hukumar Tallafin Ilmin Gaba Da Sakandare ta Kasa (TETFund) ita ce ta dauki nauyin buga shi.
Littafin ya ba mu cikakken labarin yadda East ya kasance marubuci, shugaban kamfani kuma manazarci. Yana dauke da tarihin East daga haihuwa har zuwa mutuwa, da sharhi kan ayyukan da ya yi a fagen adabi, musamman yadda ya taimaka wajen rayar da rubutaccen Adabin Hausa na zube da na wasan kwaikwayo da tarihi da kimiyya, kai har ma da aikin jarida. Littafin zai sa duk wanda ya yi wa East sanin shanu ya san shi da kyau yanzu, kuma ya nuna mana asalin rayuwar mutane irin su Imam da dimbin marubutan Hausa ’yan zubin farko.
Littafin ya bayyana mana cewa shi dai East, haifaffen Landan ne. Ya yi karatun firamare har zuwa na digirin digirgir a Odford. Abin da ya karanta shi ne ilimin hada magunguna (Chemistry) da kuma harsunan Larabci da Latin da Girkanci. Ya dan taba aikin koyarwa, sannan ya shiga aikin soja a zamanin Yakin Duniya Na Biyu.
Daga nan ya bi ayarin Turawan da ake turowa Afrika domin taimaka wa Birtaniya ta cin ma burukanta na mulkin mallaka. Shi sai aka lika shi a Ma’aikatar Ilmi domin a nan ne ya fi wayo. Da farko, an tura shi yankin Binuwai na Arewacin Najeriya, inda ya yi aikin koyarwa a makarantu da ke garuruwa daban-daban. Sai yankin Adamawa, inda ya shafe shekaru. Ta dalilin haka ya ji yarukan Tibi da Fulatanci radau. Daga bisani aka tura shi Kwalejin Horon Malamai ta Katsina, inda ya koyar da dalibai wadanda daga baya suka zama mashahurai a Najeriya, wato irin su Firaminista Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) da Alhaji Abubakar Imam da sauransu.
Kofar da Dakta East ya bi ya zama babban tsani ko ma mu ce gagarabadau a fagen adabi, an bude ta ne a cikin 1929, lokacin da gwamnati ta kafa Hukumar Fassara (Translation Bureau) a Kano amma a 1931 aka maida ita Zariya, aka nada East ya zama shugabanta. Aikin hukumar shi ne fassara wasu takardu da littattafai irin su dokokin gwamnati da makamantansu daga Ingilishi zuwa Hausa, sannan ta shirya takardun jarabawar iya harsunanmu na gado, wadda ake yi wa Turawa masu son zuwa Arewacin Najeriya domin kama aiki.
Bayan shekara bakwai, bisa shawarar East, sai aka sauya wa hukumar suna zuwa Hukumar Talifi (Literature Bureau). domin ya lura aikinta ya wuce fassara kadai, ya fadada zuwa samar da littattafan da za a yi amfani da su a makarantu, ganin cewa ana da karancinsu. A matsayin East na shugaban wajen, a cikin 1945 sai ya bukaci gwamnati ta ba hukumar kudi ta sayo injinan buga littattafai, maimakon a dogara ga kai aikin dab’i a wasu garuruwan kamar Kaduna da Jos. Dalili ke nan da aka samar da Kamfanin Gaskiya (Gaskiya Corporation) a Zariya.
Duk da yake ayyukan da East ya yi a Najeriya suna da tarin yawa, amma an fi kula ne da ayyukansa a fagen adabi domin a nan ne ya fi yin tasiri. Misali, a cikin 1933 ya shirya gasar rubuta littattafan hikayoyi, inda aka samar da littattafai biyar da aka buga, wato ‘Ruwan Bagaja’ da ‘Gandoki’ da ‘Idon Matambayi’ da ‘Shehu Umar’ da ‘Jiki Magayi.’
Sai dai wani abin lura shi ne, Dakta Aliyah ta sanar da mu cewa ba wannan ba ce gasa ta farko irinta, an yi wasu gasannin har sau biyu a baya, wadanda ba East din ne ya shirya su ba. Amma bambancin ita wannan gasar da wadancan biyun shi ne, ita ce aka buga littattafanta, domin kuwa su wadancan na farkon ba a buga littattafan ba kuma ma littattafan da aka shigar a gasar duk sun bace.
Babban tasirin wannan gasar da East ya kawo shi ne yadda ta sa ‘dan ba’ a fagen rubutaccen adabin kirkira na zube na Hausa da haruffan Romanci ko mu ce boko. A da, rubutaccen Adabin Bahaushe a cikin ajami yake kuma ya kunshi wake ne, sauran zube na kirkira yawancinsa Turawa ne suka yi shi, ba ’yan kasa ba.
East ya ci gaba da aiki gadan-gadan wajen bunkasa wannan adabi da aka kawo mana daga waje, ta hanyar agaza wa marubuta da dabarun rubutu da kuma buga abin da suka rubuta. Ta haka ne hukumarsa ta samar da dimbin littattafan hikaya da na addini da na wake da na wasan kwaikwayo da na kimiyya. A kokarinsa na gina wannan adabi, East ya rike Abubakar Imam, ya yi masa jagora wajen rubuta littattafai da suka hada da ‘Magana Jari Ce’ da ‘Karamin Sani Kukumi Ne.’
Shi kansa East, bai sa ido ga wasu su rubuta ba, shi ma ya shiga an dama da shi dumu-dumu. Misali, tun a gasar 1933, shi da John Tafida Wusasa ne su ka rubuta ‘Jiki Magayi.’ Bayan haka, East ya rubuta kundin wasannin kwaikwayo na farko mai suna ‘Sid Hausa Plays.’
Bayan haka, East ya rubuta wadansu littattafan wadanda ba su shafi adabi ba. Ya yi littafi kan tarihin yankin Adamawa, ya yi wani kan yadda ake yi wa Turawa jarabawar sanin makamar harsunan Arewacin Najeriya, ya yi wasu littattafan kan Nahawun Hausa, shi da Imam sun hadu sun rubuta littafin farko kan kimiyya da harshen Hausa mai suna ‘Ikon Allah’ (kundi na 1 zuwa na 5), sannan ya yi wa wani mutum dan kabilar Tibi mai suna Akiga. Sai juma ya yi jagoran rubuta littafin farko kan tarihin ita kabilar tasu mai suna ‘Akiga’s Story: The Tib Tribe as Seen by One of its Members.’ Bugu da kari, East ya rubuta makaloli da dan dama kan harshen Hausa, wadanda aka buga a mujallun nazari a lokuta daban-daban.
Littafin na Dokta Aliyah A. Ahmad, ya nuna mana wata gagarumar rawar wadda East ya taka a fagen aikin jarida a Najeriya. Wannan kuwa shi ne yadda ya jagoranci kafa jaridar Hausa da ta fi kowacce tasiri tare da dadewa a kasar nan, wato Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda aka kafa a cikin 1939. East ne Babban Edita, yayin da Editanta shi ne Mr. Giles, sannan Imam ya zama Editan Hausa na jaridar, wanda ya kasance kamar mataimaki ga Giles kafin daga baya ya zama cikakken editanta. Abin mamaki shi ne, yawan kwafen jaridar da ake bugawa a kuma sayar da su tatas; a bugun farko an buga 5,000, a bugu na biyu an sayar da 8,900.
A fagen aikin jaridar dai, East ne ya kirkiri jaridar Turanci mai suna Nigerian Citizen, wadda aka yi wa lakabi da “Kanwar Gaskiya.”
To sai dai kuma ga wani abu: Bahaushe mai ban haushi! Wai ka dubi duk hakilo da East ya yi wa kasar Hausa, amma sai da Hausawa suka taru suka tsinka shi a idon duniya. Me ya faru? A cikin 1951, wasu mutanenmu suka kafa kwamitin bincike a kan East, har suka zarge shi da rashin iya gudanar da Kamfanin Gaskiya. Suka ce wai ya kasa kawo riba, don haka ana so ya yi murabus ko a kore shi! Bai da zabi, domin bakin mutum ya fara sunsunar iskar ’yanci, Bature ya fara daina ba kowa tsoro. To, haka kuwa aka yi, tilas East ya bar kamfanin da ma Najeriyar baki daya, kuma tun da ya tafi grainsu da sunan hutu bai sake komowa ba har ya rasu a 1975.
Za mu kammala