Manyan alamomin tashin Alkiyama
Daga Hudubar Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan Masallacin NASFAT na kasa da ke Abuja Fassarar Salihu Makera Huduba ta Farko: Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa muna neman shiriyarSa muna yi maSa shukura muna neamm gafararSa kuma muna tuba gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah […]
Daga Hudubar Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan
Masallacin NASFAT na kasa da ke Abuja
Fassarar Salihu Makera
Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa muna neman shiriyarSa muna yi maSa shukura muna neamm gafararSa kuma muna tuba gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, kuma Wanda Ya batar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, ba Ya da kama balle misali balle kini. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu, masoyinmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda yake cewa: “An aiko ni ne tsakanin ad Sa’a kamar wadannan biyu, sai ya nuna manuniyarsa da yatsar tsakiya” yana mai nuni da kusantowar Sa’a. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa masu tsarki ababen tsarkakewa.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin Allah da takawa, domin Alkiyama ta kusanto, Allah Mai girman Daraja Ya ce: “Sa’a ta kusanto. Wata ya tsage.” Takawa tana amfani a Lahira.
Ku sani ya bayin Allah! Lallai Sa’a ba za ta tsayu ba, har sai wasu abubuwa daga alamomin kusantowar Sa’a sun bayyana, wadanda a kansu ne hudubarmu ta yau take magana wato Manyan Alamomin Sa’a.
Wato kamar yadda suka zo a cikin Hadisin alamomi goma da ake kira Manyan Alamomin Sa’a, su ne:
Fitowar Dujal da saukar Annabi Isa dan Maryam (AS) da fitowar Yaju wa Majuju da fitowar daga mafadarta da fitowar wata dabbar kasa da hayaki da girgizar kasa guda uku da wata wuta da za ta fito daga Aden a kasar Yemen. (Sai dai Dujal suna da yawa, kamar yadda Fir’auna suke da yawa).
Ya bayin Allah! Amma shi Dujal, mutum ne daga cikin ’ya’yan Adam, kuma a zahiri shi daga Bani Isra’ila ne. Zai zagaye duniya zuwa dukan sassanta a cikin misalin shekara daya da rabi cikin ikon Allah, sai dai ba zai iya shiga Makka da Madina ba, domin mala’iku za su hana shi daga shiga cikinsu.
Kuma zai kasance lokacin fitowar Dujal lokaci ne na fari da yunwa, inda zai rika da’awar shi ne Allah. Wadanda suka yi imani da shi, sai su samu wadata da koshi, domin Allah Madaukaki zai fitini wani sashi na halitta da shi. Amma muminan da suka karyata shi ba su bi shi (Dujal) ba, sai su hadu da yunwa, amma sai Allah Ya rika kosar da su ta tasbihi da tsarkake Shi da suke yi, wato wannan tasbihi sai ya tsaya a matsayin abinci, yunwar ba za ta cutar da su ba.
Hakika Annabi (SAW) ya gargadi al’ummarsa game da Dujal da fitinarsa kuma ya siffanta musu shi domin su san shi, zai kasance idonsa daya a fili, dayar kuma shafaffiya, don haka ne ake kiransa Dujal mai ido daya.
Annabi (SAW) ya bayar da labari cewa, Allah zai bayyanar da wasu abubuwa da suka saba wa al’ada (abubuwan ban mamaki kamar mu’ujizoji da karamomi) domin ya jarrabi bayi da shi. Domin ya nuna musu wanda zai shiryu da wanda zai bace.
Daga cikin abubuwan ban mamakinsa zai iya tsaga mutum daga cikin muminan da suke karyata shi gida biyu tun daga fuskarsa, sannan ya hada shi da izinin Allah, amma sai wannan mumini ya ce, babu abin da wannan zai kara min face karyata ka.
Daga cikin abubuwan ban al’ajabinsa akwai cewa Dujal zai kasance yana da koguna biyu, wani kogi na ruwa da zai rika riya aljannarsa ce da kogi na wuta da zai rika riya wutarsa ce. Hakika Annabinmu (SAW) ya ba mu labari cewa wannan kogin wuta shi ne sanyi a wurin muminai, kuma kogin ruwan shi ne wuta a kansu.
Akwai dujal-dujal da dama a cikin al’umma wadansu ana samu a cikin malamai da masu da’awar ilimi, inda za ka ga mutum yana yin wasu abubuwa na ban al’ajabi. Ire-irensu ne ake samun wadanda suke cewa sun kai wani mataki da Annabi (SAW) bai kai ba, karya suke tunda Allah Ya halicci sammai da kasa tun daga Annabi Adam (AS) har zuwa tashin kiyama ba a yi ba, kuma ba za a yi kamar Annabi Muhammad (SAW) ba.
Sannan ga bokaye da miyagun malaman da suke siddabaru ga mutane, su bayyana wa mutum cewa kaza ya faru da shi jiya, kuma kaza zai faru da shi gobe, da haka sais u rika nuna abubuwan al’ajabi. Duk wadannan ayyuka ne irin na dujal kuma duk Musulmi nagari ya wajaba ya guje musu.
A karshen kwanakin Dujal ne Annabi Isa dan Maryam (AS) zai sauka daga sama, a Gabashin Damaskus kamar yadda Hadisi ya bayyana, sai Dujal ya tabe shi a Falasdinu, a wata alkarya da ake kira Babu Ludda, wata alkarya ce daga cikin alkaryun Falasdinu, sai Annabi Isa (AS) ya kashe shi. Sannan Annabi Isa (AS) ya yi hukunci da shari’ar Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW). Sannan a zamanin Almasihu bayan gushewar Yajuju wa Majuju, sai a samu yalwa mai yawa da aminci, kasa ta fitar da abubuwan da suke cikinta na daga zinare har sai an rasa mutumin da zai karbi sadaka saboda wadatar dukiya.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, godiyar da take dacewa da ni’imarsa ta cika karinsa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Wanda Yake cewa: (Suna tambayarka game da Sa’a, yaushe ne matabbatarta. Ka ce, abin sani iliminta yana wurin Ubangijina, babu mai sanin lokacinta face Shi.” Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin Allah da takawa. “Ku bi Allah da takawa, kuma ku sani cewa lallai ne zuwa gare Shi ake mayar da ku.”
Ya bayin Allah! Sa’a ba za ta tsaya ba, face alamomin nan goma sun kammala. Kuma daga cikin abin da zai faru a bayan wadancan akwai, fitowar rana daga mafadarta d fitowar wata dabbar kasa tana yi wa mutane magana, to a lokacin duk wanda ya yi imani zai tabbata mai imani, wanda ya kafirta zai tabbata kafiri, ba za a karbi tubar wanda bai kasance ya yi imani gabanin haka ba, kuma ba za a karbi tubar wani ba a bayan haka. Wadannan alamomi biyu za su faru ne a wuni daya a tsakanin asuba da walaha. Sannan sai hayaki ya sauka ya cika kasa, sai kafirai su rika jin kamar za su mutu saboda tsananin wannan hayaki, amma mumini sai ya kasance musu kamar girgije.
Za a yi girgizar kasa sai uku, girgizar za ta riki wanda yake kanta a gabashi da girgizar wanda yake yamma da girgizar da ke cikin Jaziratul Arab.
Kuma daga cikin wadannan alamomi ya ku ’yan uwa a cikin imani! Wata wuta za ta fito daga Aden ta kasar Yemen, sai ta kora mutane zuwa yamma ba za ta rika ci balbal ba, a’a za ta rika kora su korawa.
Kuma Sa’a za ta tsaya ne a kan ashararan mutane domin lallai dukan Musulmi daga mutanen da suke bayan kasa za su mutu kafin tsayuwar Sa’a da shekara dari, sannan kafirai su yi ta yin yawa har Sa’a ta tsaya a kansu.
Mun kawo wadannan alamomi ne domin tunatarwa gare ku, amma ku sani duk wanda ya mutu ya fara haduwa da tasa Sa’ar, domin daga lokacin da aka kwantar da shi a kabarinsa, kabarin zai kasance imma rauda daga raudar Aljanna ko tururi daga turirin wuta.
Allah Ya tabbatar da ni da ku a kan addinin Musulunci, Ya shiryar da mu ga ayyukan da’a da tuba gabanin mutuwa, amin.
“Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da kuma zalunci. Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”
Wannan aya tana kunshe da umarni kan abubuwa uku da hani kan abubuwa uku da suka kamata Musulmi su rika kiyayewa.
Allah Ya yi mana albarka ni da ku.
Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallaicn NASFAT na kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa
ta tarho mai lamba: 080347108620