Manyan ayyuka: Hukumomi za su samu biliyan 750 a makon nan-Adeosun
Ministan Kudi, Kemi Adeosun ta ce Gwamnatin tarayya za ta saki kimanin Naira biliyan 750 ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati a makon da muke ciki don aiwatar da manyan ayyukan da suke cikin kasafin kudin shekarar 2017. Da take magana jiya a Abuja yayin da take ganawa da tawagar masu saka hannun jari daga kasar […]

Ministan Kudi, Kemi Adeosun ta ce Gwamnatin tarayya za ta saki kimanin Naira biliyan 750 ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati a makon da muke ciki don aiwatar da manyan ayyukan da suke cikin kasafin kudin shekarar 2017.
Da take magana jiya a Abuja yayin da take ganawa da tawagar masu saka hannun jari daga kasar Faransa wadanda suka hada da kamfanoni 30 da ke son saka jari a Najeriya, Adeosun ta ce tuni gwamnati ta saki kimanin Naira biliyan 450 don aiwatar da manyan ayyuka.