Manyan abubuwan kunya 10 da suka faru a siyasar Nijeriya daga 1999

Ƙurar da Orubebe ya tayar a wajen da haɗa sakamakon Zaɓen 2015.

Manyan abubuwan kunya 10 da suka faru a siyasar Nijeriya daga 1999

Bayan kwashe tsawon shekaru ana gwagwarmayar da ta hadu da yawan kamawa da tsarewa a kurkuku da kashe masu rajin dawo da mulkin dimokuradiyya a karshe Nijeriya ta koma ga tafarkin mulkin dimokuradiyya ranar 29 ga watan Mayun 1999.

Wannan ne ya sa sojoji suka koma bariki kuma ya bude wani sabon shafin da ake kira da Jamhuriyya ta Hudu.

Zuwa yanzu za a iya cewa shi ne lokaci mafi tsawo da fararen hula suka dauka suna mulki ba tare da sojoji sun katse ba tunda aka karbi mulkin kai a 1960.

Sai dai duk da haka akwai tangarda a tafiyar. Tafiyar ta hadu da rigingimun iri-iri wadanda suka kara bude idon ’yan Nijeriya su kara karfafa dimokuradiyyarsu.

Ga wasu daga cikin tabargazar da suka faru a siyasar kasar nan tun daga 1999.

Salisu Buhari da shaidar karatunsa na Toronto

Kimanin wata biyu da kaddamar da Majalisar Wakilai a 1999, majalisar ta fara samun kanta a cikin abin kunyar da har yanzu ke cikin manyan abubuwan da suka shafi wani babban mai rike da mukami a Nijeriya.

Ibrahim Salisu Buhari shi ne dan majalisa mafi karancin shekaru daga Jihar Kano wanda kuma ya zama Shugaban Majalisar Wakilan amma aka fallasa ya yi karyar shekarun haihuwa da kuma jabun takardun kammala jami’a.

Mujallar The News wadda ta bankado abin kunyar, ta ce Salisu Buhari ya yi da’awar ya samu diploma a Jami’ar Ahmadu Bello a 1988; kuma ya yi digiri a Jami’ar Toronto a kasar Kanada a 1990 inda ya yi hidimar kasa a 1991.

Haka Salisu Buhari ya ce an haife shi ne a ranar 3 ga Janairun 1963.

Sai daga baya ta gano cewa an haifi Ibrahim Salisu Buhari ne a ranar 3 ga Janairun 1970 inda ya cika shekara 29 a wancan lokaci da ya yi takara ya ci zabe a 1999, alhali Tsarin Mulki ya tanadi cewa sai dan shekara 30 ne zai yi takarar.

Kuma an gano cewa ya samu takardar shiga Jami’ar ABU amma aka sallame shi saboda ya yi karya a kan takardun makarantarsa.

Sannan bayanai sun nuna bai taba yin karatu a Jami’ar Toronto da ke Kanada ba kuma bai yi hidimar kasa ba, a cewar Mujallar The News.

Duk da cewa ya musanta zargezargen, amma jin labarin Gwamnatin Tarayya ta kammala shiri don gurfanar da shi a gaban kotu sai ya yi murabus daga kujerarsa ta Shugaban Majalisar Wakilai da kuma kujerarsa ta majalisa da yake wakiltar Karamar Hukumar Nassarawa a ranar 22 ga Yulin 1999, kwana 49 da hawansa.

Tazarcen Obasanjo karo na uku

A kusan karshen mulkin Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo zango na biyu siyasar kasar nan ta shiga cikin rudu lokacin da majalisa ta yi kokarin yi wa Tsarin Mulki gyara don bai wa Shugaban Kasar damar yin takara karo na uku.

Duk da cewa Shugaban Kasa Obasanjo ya musanta cewa yana da burin ci gaba da mulki na wasu shekara hudu, amma yadda abubuwa suke tafiya sun nuna yadda ’yan Nijeriya suka shirya domin kare dimokuradiyya da guminsu.

Shugaban Majalisar Dattawa na lokacin (2006), Sanata Ken Nnamani ya fadi a wajen kaddamar da littafinsa “Standing Strong: Legislative Reforms, Third Term, and Other Issues of the 5th Senate,” cewa wasu sanatoci da suka goyi bayan gyaran Kundin Tsarin Mulki sun canza ra’ayinsu bayan da suka yi magana da mutanen da suke wakilta.

Ya kara da cewa, nuna zaman majalisar kai-tsaye ta talabijin a ranar 16 ga Mayun 2006, lokacin da ake muhawara a kan Tsarin Mulki ya bayar da damar yin zango uku ga Shugaban Kasa, ya tilasta wasu sanatoci watsi da goyon bayan da suke yi wa kudirin.

Zaben Shugaban Kasa na 2007

A lokacin da shirin Shugaban Kasa Obasanjo na ta-zarce karo na uku ya rushe, ana ganin zaben da ya kawo Shugaban Kasa Umar Musa ’Yar’aduwa shi ne mafi muni a tarihin Nijeriya.

Yanayin yadda aka gudanar da zaben ne ya sa masu sa-ido na Kungiyar Tarayyar Turai (EU) suka bayyana zaben da “Mafi muni da suka taba gani a duniya da ke cike da magudin da satar akwatunan zabe da yi wa masu zabe barazana.”

Bayan ga wannan kuma rashin yin shiri daga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ya jefa zaben a rashin tabbas, inda aka fara gudanar da zaben a wasu wuraren da misalin karfe 5:00 na yamma saboda rashin isar kayayyakin zabe a kan lokaci.

Haka Hukumar INEC ba ta sanya sunan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar a cikin takardar zabe ba, lamarin da ya janyo ya kai ta kotu inda mako daya kafin zabe Babbar Kotu ta umarci Hukumar INEC ta yi gyara.

A wancan lokaci Shugaban Kasa Umaru ’Yar’aduwa ya bayyana cewa zaben yana cike da kura-kurai inda ya yi alkawarin samar da dokokin da za su inganta harkokin zabe.

Rigimar matsayin Jonathan lokacin da ’Yar’aduwa ba ya nan

Daya daga cikin manyan matsalolin da siyasar kasar nan ta shiga shi ne lokacin da ’Yar’aduwa ya yi rashin lafiya ya tafi kasar Saudiyya don yin jinya ba tare da ya mika al’amuran kula da kasar ga Mataimakinsa a hukumance ba kamar yadda Tsarin Mulki ya tanada.

Rashin zamansa a kasar nan na mako 10 ya kawo tsaiko an tafiyar da harkokin gwamnati lamarin da ya janyo ’yan majalisa suka yanke hukuncin cewa Mataimakinsa Goodluck Jonathan ya zama Shugaban Kasa na riko, amma ministocin ’Yar’aduwa suka yi wa tutsu.

Wannan mataki ne Shugaban Majalisar Dattawa na lokacin David Mark ya kira ‘dokar lalura saboda rashin madogarar Tsarin Mulki.’

Kafin Majalisar Dokoki ta Kasa ta dauki matakin, siyasar kasar nan ta dauki zafi an rarrabu kan addini da kabilanci, inda mutane da dama daga Kudu inda Jonathan ya fito suka fassara wasan buyar da ake yi da wata dabara ta hana Kudu maso Kudu damar shugabancin kasar nan.

Patricia Etteh

A ranar 6 ga Yuni 2007 Patricia Etteh ta zama mace ta farko Shugabar Majalisar Wakilai.

Sai dai matar wadda mai gyaran gashi ne kafin ta zama lauya kuma ta mulki majalisar na dan lokaci kalilan a matsayin mai mukami na hudu mafi girma a Nijeriya.

Wata biyu bayan hawanta kujerar aka fara zarginta da almundahana.

An sa ta gurfana a gaban wani kwamiti da aka kafa don bincikar yadda aka yi ta bayar da umarnin kashe Naira miliyan 628 wajen gyaran gidanta da na mataimakinta da sayen motoci 12 ga Majalisar Wakilai.

A wani zaman wancan kwamiti a kokarinta na kare kanta an rika kiranta da ‘Barauniya! Barauniya!! cikin harshen Yarabanci, inda daga bisani jami’an tsaro suka fitar da ita daga majalisar.

Bayan makonni ta yi murabus tare da mataimakinta Babangida Ngroje.

Cuwa-cuwar tallafin mai da ya kai Faruk Lawan kurkuku

A shekarar 2011 Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti don binciken tallafin man fetur inda aka gano cewa gwamnati ta biya wasu ’yan kasuwa Naira biliyan 229.7 a tsakanin shekarar 2010-2011.

Shugaban kwamitin dan Jihar Kano, Faruk Lawan da ake kira Malam Mai Amana ‘Mr Intergrity,’ ya mika wa majalisar rahoton kwamitin da ke dauke da sunayen kamfanonin da suka damfari gwamnati.

Bayan wasu kwanaki sai Lawan ya fada a cikin harkallar cin hanci lamarin da daga baya ya kai shi zaman fursuna a kurkukun Kuje. Wani faifan bidiyo ya nuna shi yana karbar wasu dalolin Amurka daga daya daga cikin ’yan kasuwar yana durawa a cikin hularsa.

Bayan kusan shekara 10 Mai shari’a Angela Otaluka ta Babbar Kotun Birnin Tarayyar Abuja ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai a kurkuku saboda karbar Dalar Amurka 500,000 a lokacin yana Shugaban Kwamitin.

Kotun ta samu bayanai cewa Lawan ya nemi a ba shi Dala miliyan uku inda ya fara karbar Dala dubu 500 a matsayin somin-tabi na kudin daga wajen babban dan kasuwar nan mai harkar man fetur, Femi Otedola a 2012.

Alkalin ta yarda cewa ya karbi kudin ne don ya cire Kamfanin Otedola na Zenon Oil and Gas daga jerin kamfanonin da suke damfarar gwamnati.

Sai dai Kotun Koli ta rage shekarun da zai yi daga bakwai zuwa biyar.

Zanga-zangar mamaye Nijeriya

Wannan zanga-zanga ta samo asali ne yayin da gwamnati ta yi nufin cire tallafin man fetur da kara kudin daga Naira 65 zuwa Naira 141 a kan kowace lita.

Zanga-zangar da ta barke a ranar 2 ga Janairu 2012 ta zama wani babban yunkuri na ’yan Nijeriya da ya yi kusan kassara tattalin arziki kasa lura da cewa mutane da dama da suka hada da ma’aikata da ’yan kasuwa da masu kamfanoni masu zaman kansu sun shiga zanga-zangar.

Zanga-zangar ta fara zama ta siyasa ganin ’yan adawa suna amfani da ita wajen sa ’yan Nijeriya su huce fushinsu a kan ci gaba da tsadar rayuwa da karuwar almundahana a kasar.

Ci gaba da zanga-zangar ce ta tilasta gwamnati rage kudin man zuwa Naira 97.

Hargitsi a Majalisar Dokoki

Bayan Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya koma babbar jam’iyyar adawa, jami’an tsaro sun rufe masa hanyar shiga majalisar.

Hakan ya janyo hargitsi a majalisar har ta kai ga an ba hammata iska a tsakanin ’yan majalisa da ’yan sanda inda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen hana ’yan majalisar shiga harabarta.

Ganin an rufe dukkan kofofin shiga majalisar ’yan majalisar suka rika haura katanga inda wasu suka shiga da kafa kafin Tambuwal ya samu shiga cikin majalisar.

Mamaye Majalisa da gidajen Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakinsa

A shekarar 2018 an yi amfani da jami’an tsaro wajen yi wa ’yan majalisa barazana musamman sanatocin wadanda gwamnati ke kallonsu a matsayin manyan masu adawa da ita.

Na farko jami’an DSS sun mamaye gidan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Sarki don kama shi.

Sufeto Janar na ’Yan sanda ne ya bayar da umarnin kama Saraki da sunan cewa wai akwai wasu tambayoyi da ya kamata ya amsa game da sanayyar da ake zargin yana da ita da wadanda aka kama da fashi da makami a wani banki a garin Offa da ke Jihar Kwara inda aka yi asarar rayuka.

A dai wannan rana jami’an Hukumar EFCC suka yi kawanya ga gidan Mataimakinsa Ike Ekweremadu, bisa cewa ana gayyatarsa don amsa wasu tambayoyi a kan wata harkallar kudi.

Yayin da Saraki ya tsere wa kamu, Mataimakinsa Ekweremadu bai samu wannan sa’ar ba.

Ana zargin hakan na da alaka da yunkurin Shugaban da wasu ’yan majalisar na komawa wata jam’iyyar.

Haka a watan Augusta an samu mamaya a cikin majalisar inda jami’an DSS suka hana ’yan majalisar shiga ciki.

Saboda komawar Shugaban Majalisar jam’iyyar adawa. Lamarin ya janyo korar Shugaban Hukumar DSS na Kasa daga kujerarsa

Ƙurar da Orubebe ya tayar a wajen da haɗa sakamakon Zaɓen 2015

Zaɓen shekarar 2015 da ya kawo sanannen dan adawar nan Muhammadu Buhari gadon mulki zai ci gaba da zama mafi ban-mamaki a tarihin Nijeriya, musamman kurar da ta tashi a wajen tattara sakamakon zaben.

Yayin da aka bayyana zaɓen da ɗaya daga cikin wadanda suka fi inganci kuma Shugaban da ke kan gado ya amince da shan kaye tun kafin a bayyana Buhari ya samu nasara, tsohon Ministan Al’amuran Yankin Neja-Delta, Mista Godsday Orubebe kokarin hargitsa karbar sakamakon zaben ya yi, inda ya zargi Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega da aikata wasu laifuffuka, lokacin da ya ga ubangidansa zai sha kasa a zaben.

Kuma yayin da Jega ya danne zuciyarsa a lokacin taƙaddamar, ana kallon manufar Orubebe ita ce ya hana bayyana sakamakon zaɓen na ƙarshe, lamari da ba zai taɓa gogewa daga zukatan ’yan Nijeriya ba.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania