Manyan Gobe barka da warhaka 01

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon Kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku Labarin Balbela da Zakanya. Labarin na kunshe da darasin idan kana cutar wadansu don ka fi su karfi ko arziki, to wata rana sai ka dawo kana neman taimakonsu. A sha karatu lafiya.Naku Bashir […]

Manyan Gobe barka da warhaka 01
Manyan Gobe barka da warhaka 01

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon Kawunku Naseeru Taneemu Annuree ya kawo muku Labarin Balbela da Zakanya. Labarin na kunshe da darasin idan kana cutar wadansu don ka fi su karfi ko arziki, to wata rana sai ka dawo kana neman taimakonsu.

A sha karatu lafiya.
Naku Bashir Musa Liman

Labarin Balbela da Zakanya

A cikin dokar daji akwai wata zakanya da ta hana namun daji zaman lafiya, takan kashe duk wanda tsautsayi ya hada ta da shi ko da ba yunwa take ji ba. Hatta tsuntsaye na kuka da yadda take damun su da gurnani marar dadin ji. Wannan zuluncin ya sanya namun daji suke zaman dar-dar dare da rana.
Wata rana dan da take ji da shi ya fita wasa bai dawo gida ba. Ta jira har ta gaji amma bai dawo ba, ga shi kuma shi ne da daya tilo gare ta. Cikin tashin hankali ta bazama cikin daji neman sa. Ta rasa wanda za ta tambaya domin duk wanda ya hango ta sai ya tsere. Har yamma ta yi ba ta ga danta ba. Hankalinta ya dugunzuma ainun a yayin da ta zauna karkashin wata bishiyar kuka tana numfashi da kyar.
Ashe a kan bishiyar akwai wata balbela wacce kuma tuni ta lura da abin da ke faruwa. Tausayin zakanyar ya kama ta. Cikin karfin hali ta sauko kasa-kasa tare da yi wa zakanyar alamar ta biyo ta a baya, suka ci gaba da tafiya har suka iso bakin wani kududdufi suka tarar da dan zakanyar kwance yana barci alamar shi ma ya yi yawon neman hanyar koma wa gida har ya gaji bai samu ba. Wannan taimakon da balbela ta yi wa zakanya ya sanya ta sauya halayenta. Tun daga ranar ba ta kara cutar kowa a dajin ba.
Daga Naseeru Taneemu Annuree (NTA)