Manyan Gobe barka da warhaka 04

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Ya kamata ku rika mayar da hankali kan karatu, saboda ilimi shi ne gishirin zaman duniya, idan kuna da ilimi zu ka samu sauki wajen gudanar da rayuwarku.A wannan makon na kawo muku labarin zomo da dila. Ina fata za ku karanta labarin hade da amsa mini tambayar da […]

Manyan Gobe barka da warhaka 04
Manyan Gobe barka da warhaka 04

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Ya kamata ku rika mayar da hankali kan karatu, saboda ilimi shi ne gishirin zaman duniya, idan kuna da ilimi zu ka samu sauki wajen gudanar da rayuwarku.
A wannan makon na kawo muku labarin zomo da dila. Ina fata za ku karanta labarin hade da amsa mini tambayar da ke karshen labarin.
A sha karatu lafiya
Naku: Kawu Bashir Musa Liman

Labarin zomo da dila

A wani lokaci da ya wuce zomo da dila abokan juna ne, ba su da aikin yi face takaddama a kan wanda ya fi wayo a tsakaninsu. Tun ana saurarar su har a shiga tsakani har dai aka rabu da su, kasancewar kullum abin kara gaba yake yi kamar wutar daji.
Wata rana suna cikin takaddamar ne sai wani malami ya zo wucewa, nan da nan suka je wurinsa, sannan suka ci gaba da takaddama don malamin ya yi alkalanci ya fadi wanda ya fi wayo da fasaha a tsakaninsu. Ganin abin nasu ba mai karewa ba ne wai shege da hauka, sai ya dakatar da su, bayan sun tsaya ne, sai suka ci gaba da haki kamar sun yi gudun famfalaki.
Daga nan ya ce zai gwada su, duk wanda ya lashe gwajin to shi ne ya fi wayo da fasaha. Ga gwajin: “Akwai wani gida mai dauke da mutane (maza) da kuma dawakai. Jimullar wadannan dawakan da mutane suna dauke da kawuna 22 da kuma kafafu 72. Shin mutane da dawakai nawa ne a gidan?”
Nan da nan suka fara tunani, an dauki lokaci mai tsawo amma sun kasa samo amsar tambayar. Ina so Manyan Gobe su taimaka su amsa musu tambayar ta wannan lambar: 07036925654.