Manyan Gobe barka da warhaka 05
Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A makon jiya mun kawo muku labarin Dila da Zomo, har muka bukaci ku turo amsar tambayar da muka yi muku a karshen labarin, da yawa daga cikin Manyan Gobe sun amsa tambayar daidai. A wannan makon za mu kawo muku amsar tambayar ne, muna fata za […]
Yaya karatu? Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A makon jiya mun kawo muku labarin Dila da Zomo, har muka bukaci ku turo amsar tambayar da muka yi muku a karshen labarin, da yawa daga cikin Manyan Gobe sun amsa tambayar daidai. A wannan makon za mu kawo muku amsar tambayar ne, muna fata za ku bi bayanin bi-da-bi. A sha karatu lafiya.
Amsar labarin zomo da dila
Tambayar da Malamin ya yi wa Dila da Zomo ita ce: “Akwai wani gida mai dauke da mutane (maza) da kuma dawakai. Wadannan dawakan da mutane suna dauke da kawuna 22 da kuma kafafu 72. Shin mutane da dawakai nawa ne a gidan?”
Amsar Tambayar
Da farko mu dauka d ita ce doki, y kuma mutane. kowa ya sani doki da mutum duka kai daya suke da shi, don haka idan aka hada d+y= za a samu kai 22. Amma mutum yana da kafa 2 ne, doki kuma 4, don haka idan aka hada 4d+2y= za a samu kafa 72.
Don haka tun da akwai kawuna 22, za a samu mutane 8 ne da kafafunsa biyu, 8 sau 2 za a samu 16, haka za a samu dawakai 14, suna da kafafu 4, 14 sau 4 za a samu kafafu 56. Idan aka tara 56+16 za a samu kafa 72. Wato 2(8)+4(14)= 16+56=72, d+y=22 wato 8+14=22