Manyan Gobe barka da warhaka 06

Barkanmu da sake saduwa a wannan filin namu na Manyan gobe. A yau na kawo muku labarin ‘beran daji da beran birni’. Labarin ya kunshi yadda ya kamata Manyan gobe su zama masu tafiyar da rayuwarsu cikin sauki ba tare da takura ba. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin beran daji da beran birni […]

Manyan Gobe barka da warhaka 06

Barkanmu da sake saduwa a wannan filin namu na Manyan gobe. A yau na kawo muku labarin ‘beran daji da beran birni’. Labarin ya kunshi yadda ya kamata Manyan gobe su zama masu tafiyar da rayuwarsu cikin sauki ba tare da takura ba.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin beran daji da beran birni

A wani lokaci da ya shude ne beran birni ya kai ziyara wajen abokinsa beran daji. Don farin cikin karbar abokinsa, sai beran daji ya shirya wa beran birni mota cike da kayan abincin da ke daji.
beran birni na ganin haka, sai ransa ya baci. Ya ce da beran daji “Haka kuke zama a nan? Ai wannan abincin ya yi kadan, biyo ni birni ka ga yadda muke bushasha da abincin zamani.”
Sai beran daji ya bi na birni zuwa birni. Bayan sun isa birni ne sai beran daji rika ganin abubuwan mamaki. Da suka isa masaukin beran birni, sai suka ga abinci iri-iri. Sun yukuro ke nan za su ci abincin, sai ga wata katuwar kyanwa ta zo ta kore su, a takaice da kyar suka sha suka buya a wani rami, inda suka kwana da yunwa.
Gari na wayewa, sai beran daji ya ce shi ya hakura gara ya ci gaba da zama a daji, domin hakan ya fi masa kwanciyar hankali.
Da fatan Manyan gobe za su koyi darasi daga wannan labarin.