Manyan Gobe barka da warhaka 07
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin zomo da mai unguwa. Labarin ya kunshi yadda rashin adalci ke janyo asara. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin Zomo da Mai Unguwa A wani lokaci da ya wuce an yi wani zomo da ya kasance kwararren makeri, baya ga haka ya […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin zomo da mai unguwa. Labarin ya kunshi yadda rashin adalci ke janyo asara.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin Zomo da Mai Unguwa
A wani lokaci da ya wuce an yi wani zomo da ya kasance kwararren makeri, baya ga haka ya fi kowa iya fenti a garinsu. Kowa ya amince kwararre ne a kan aikinsa.
Rannan sai labari ya iso wurin wani mai unguwa, sai ya ce a kira masa zomo domin akwai fentin da zai yi masa a sabon gidansa.
Zomo ya yi farin ciki da wannan gayyata kuma ya yi alkawarin burge mai unguwa, don ya zama mai yi masa aiki a kodayaushe.
Yana isa gidan mai unguwa, sai ya nuna masa irin aikin da zai yi masa.
Ashe mai unguwa yana da kare da mage, inda bayan ya tafi sai suka roki zomo ya dan yi musu fenti a jikinsu domin su kara kyawu.
Bai tanka musu ba, duk da haka suka ci gaba da damun sa. Bayan kwana biyu ne sai ya dan shafa musu fentin.
Mai unguwa na ganin fentin a jikinsu, sai ransa ya baci, cikin hasala ya ce ba zai biya zomo kudin aikinsa ba. Zomo ya ba shi hakuri, amma mai unguwa ya ki. Sai zomo ya je ya yi masa asiri.
Da mai unguwa ya ga sarkin garin sai ya fara cire masa rawani da ja masa kumatu. Abin ya ba sarki haushi. Ya ce sai ya hukunta shi. Daga karshe aka tube mai unguwa.