Manyan Gobe barka da warhaka 11
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A yau na kawo muku labarin Kunkuru da kadangare. Labari ne da ya kawo dalilin da ya sa a yanzu kunkuru ba shi da gashi a kansa, ya kunshi yadda kwadayi ke zama mabudin wahala. A sha karatu lafiya.Taku Amina Abdullahi Labarin Kunkuru da […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A yau na kawo muku labarin Kunkuru da kadangare. Labari ne da ya kawo dalilin da ya sa a yanzu kunkuru ba shi da gashi a kansa, ya kunshi yadda kwadayi ke zama mabudin wahala.
A sha karatu lafiya.
Taku Amina Abdullahi
Labarin Kunkuru da kadangare
Akwai wani kunkuru mai matukar kwadayi. Ran nan sai ya ziyarci gidan kadangare. Isowarsa ke da wuya sai ya fara jin kamshin abinci tun kafin ya shiga gidan kadangaren.
Ya dinga yi masa sallama amma ya ji shiru. Bai san cewa ya shiga bandaki wanka ba. Sai ya ga tukunya a kan wuta, ya waiga ya ga babu kowa sai ya bude tukunya ya ga fate a ciki. Sai ya diba ya zuba a kansa, sannan ya rufe da hularsa. Yin hakan ke da wuya sai ga kadangare ya fito. Ya kwashe shi da hira. Ga kuma faten da ke kunar sa. A hakan ya cire hular a gaban kadangaren, inda gashin kansa gaba daya ya kone, wannan dalilin ne ya sa har yau kunkuru ba shi da gashi a kansa.
To Manyan gobe, kun ga abin da kwadayi ke janyowa ko? Da fatan za a daina kwadayi musamman ma idan an je unguwa.