Manyan Gobe barka da warhaka

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Musa da wani tsuntsu’. Labarin na kunshe da yadda taurin kai ke kai mutum ga halaka.  A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin Musa mai taurin kai Malam Hassan ba shi da wata sana’a illa farauta, duk a kauyensu babu wanda ya kai […]

Manyan Gobe barka da warhaka
Manyan Gobe barka da warhaka

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Musa da wani tsuntsu’. Labarin na kunshe da yadda taurin kai ke kai mutum ga halaka. 

A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Musa mai taurin kai

Malam Hassan ba shi da wata sana’a illa farauta, duk a kauyensu babu wanda ya kai shi sanin daji.
Rannan a hanyarsa ta zuwa farauta sai ya hadu da Musa. Ya tambaye shi inda zai je, sai ya ce masa zai je neman tsuntsu ne domin kwadayin nama yake. Malam Hassan ya hana shi cin kowane tsuntsun da ke dajin amma ya ki ji.
Jim kadan sai Musa ya hango wani tsuntsu, wuf! Ya kama. Kunkuru ya ce masa an hana cin tsuntsayen dajin nan amma ya ki ji. Ya ce yana masa bakin ciki ne don ya ga zai ci nama mai tsoka.
A hanyarsa ta koma wa gida ya hadu da biri, shi ma ya hana shi cin tsuntsun da ya kama amma ya ki ji.
Bayan ya isa gida, ya yanka tsuntsu ya gasa ya cinye. Kawai sai ya fara ihu yana birgima a kasa rike da cikinsa yana kuka. Mahaifiyarsa ta same shi ya ce ya ci tsuntsu ne. kafin a kai shi asibiti ya cika.
Don haka kada Manyan Gobe su zama masu taurin kai, domin taurin kai na janyo da-na-sani.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi