Manyan Gobe barka da warhaka 26

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon kawunku Nura Sahabi Suleja ya kawo muku labarin ‘Wani Yaro mai hikima’. Labarin na kunshe da darasin yadda za ku fadakar da na gaba da ku cikin hikima.A sha karatu lafiya Labarin Yaro mai hikima Wani yaro ne mai hikima, sai […]

Manyan Gobe barka da warhaka 26
Manyan Gobe barka da warhaka 26

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon kawunku Nura Sahabi Suleja ya kawo muku labarin ‘Wani Yaro mai hikima’. Labarin na kunshe da darasin yadda za ku fadakar da na gaba da ku cikin hikima.
A sha karatu lafiya

Labarin Yaro mai hikima

Wani yaro ne mai hikima, sai mahaifinsa ya ce ya zo ya raka shi wani wuri, suna cikin tafiya har suka kai gonar mangwaro, sai mahaifinsa ya ce masa ya tsaya a nan, shi zai hau, amma idan ya ga wani yana zuwa ko yana kallonsu, to sai ya fada masa, don ya sauko, ya amasa wa mahaifinsa, daga nan ya nannade kafar wandonsa, sannan ya hau daya daga cikin bishiyar mangwaron. Hawansa bishiyar ke da wuya har ya kai hannu zai tsinko wani mangwaro nunanne ke nan, sai yaron ya ce masa: “Baba ana kallonmu.” Hakan ya sanya ya sauko da sauri.
Bayan ya duba bai ga kowa ba sai ya tambayi dansa, “wane ne yake kallonmu?”
Sai yaron ya ce masa: “Baba malaminmu na islamiyya ne ya ce mana, duk abin da muke yi idan wani ba ya ganin mu, to Allah Yana ganin mu, shi ya sa na ce maka ana ganin mu.”
Mahaifinsa ya yi shiru, a lokaci guda ya rika kallonsa yana mamakin hikima irin tasa. Daga nan ya yi wa Allah godiya da Ya ba shi yaro mai hankali da tunani, hakan ya sanya ya fasa tsinkowa mangwaron.
 Daga Nura Sahabi suleja jihar neja. 08034145643; 08078983237