Manyan hafsoshi sun tare a Maiduguri
Manyan hafsoshin sojin kasar nan sun tare a Maiduguri fadar Jihar Borno don cika umarnin da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osubanjo ya ba su, domin karfafa yaki da Boko Haram wadda a baya-bayan na ta hallaka mutane da dama. A makon jiya mayakan kungiyar sun kai harin kwanton bauna ga ayarin motocin malaman Jami’ar […]

Manyan hafsoshin sojin kasar nan sun tare a Maiduguri fadar Jihar Borno don cika umarnin da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osubanjo ya ba su, domin karfafa yaki da Boko Haram wadda a baya-bayan na ta hallaka mutane da dama.
A makon jiya mayakan kungiyar sun kai harin kwanton bauna ga ayarin motocin malaman Jami’ar Maiduguri da ma’aikatan Kamfanin Mai na kasa (NNPC) da suke samun rakiyar sojoji da ’yan Sibiliyan JTF, don ci gaba da gudanar da binciken man fetur a Tafkin Chadi, inda suka hallaka sama da mutum 30.
Manyan hafsoshin sojin a karkashin jagorancin Hafsan Tsaro Laftana Janar Gebriel Olanisakin, sun isa Maiduguri ne a ranar Talata.
A tattaunawar wakilinmu da Kakakin Rundunar Sojin kasa, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka game da zuwan manyan hafsoshin ya ce, “Ka san akwai umarnin da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Oshinbajo, ya bayar cewa manyan hafsoshin su dawo Maiduguri domin a ga yadda za a karfafa yaki da ta’addancin a Arewa maso Gabas, kuma bisa wannan
umarni ga shi a yau dukansu sun hallara a nan Maiduguri, kuma sun kwashe sama da sa’o’i 4 suna tattauna yadda za a shawo kan al’amarin tare da daukar sababbin matakai. Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sojin Najerya suna kokarin magance ayyukan ’yan ta’adda, don haka muna rokon jama’a su ba mu cikakken hadin kai da goyon baya da bayanan da za su taimaka a gane maboyar ’yan ta’addan.”
Ya kara da cewa, sananne ne cewa akwai ’yan Boko Haram na zaune masu taimaka wa mayakan Boko Haram alhali suna cikin mutane a boye, suna taimaka wa Boko Haram na daji. “To muna so mutane su gane cewa wannan yaki ba na soja kadai ba ne, na jama’ane baki daya. Muna so mutane su sanya ido, su kuma kai rahoton abin da bai gamshe su ba ga jami’an tsaro don daukar matakan da suka dace,,” inji shi.
Da ya juya kan harin kunar bakin wake a wasu wuraren da sace mata 14 a hanyar Damboa da kuma harin kwanton baunar da maharan suka ka yi wa ayarin masu aikin gano man fetur a yankin Magumeri, Birgediya Kuka-Sheka ya ce duk da cewa an karya lagon ’yan ta’addan Boko Haram, za a rika samu wadansu za su rika sari-ka-noke a nan da can don haka akwai bukatar a rika hakuri ta tare da addu’o’i da bayar da goyon baya ga jami’an tsaro ta hanyar tona asirin munafukan da suke tallafa wa ’yan ta’addan ga hukumomin tsaro.
Ya ce sojojin suna nan sun tashi tsaye don cimma burin umarnin da Hafsan Hafsoshin Sojin kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ba su na su kamo Abubakar Shekau a raye ko a mace cikin kwana 40.