Manyan hafsoshin soja 19 ne kwamitin binciken sayo makamai zai binciki zamaninsu

Kwamitin bincikar yadda aka sayo makamai ga sojojin Najeriya daga shekarar 2007 zuwa yanzu zai binciki kwangilolin da aka bayar a zamanin manyan hafoshin soja 19 da suka yi aiki daga shekarar 2007 zuwa 2015. A ranar Litinin ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Mashawarcinsa kan Harkokin Tsaro ya kafa kwamitin, inda mashawarcin ya […]

Manyan hafsoshin soja 19 ne kwamitin binciken sayo makamai zai binciki zamaninsu
Manyan hafsoshin soja 19 ne kwamitin binciken sayo makamai zai binciki zamaninsu

Kwamitin bincikar yadda aka sayo makamai ga sojojin Najeriya daga shekarar 2007 zuwa yanzu zai binciki kwangilolin da aka bayar a zamanin manyan hafoshin soja 19 da suka yi aiki daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A ranar Litinin ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Mashawarcinsa kan Harkokin Tsaro ya kafa kwamitin, inda mashawarcin ya kafa kwamitin mutum 13 don binciken.
Wata majiya ta ce cikin manyan hafsoshin sojan 19, akwai manyan hafsoshin tsaro biyar da manyan hafsoshin sojan kasar nan 14 da mashawartan Shugaban kasa kan Tsaro hudu sai kuma a gefe guda akwai minisocin tsaro hudu.
Manyan Hafsoshin Tsaron da suka yi aiki daga shekarar 2007 zuwa 2015 sun hada da marigayi Laftana Janar Owoye Andrew Azazi (2007-2008) da Iya Cif Mashal Paul Dike (2008-2010) da  Iya Cif Mashal Oluseyi Petinrin (2010-2012) da Admiral Ola Ibrahim (2012-2014) da kuma Iya Cif Mashal Aled Badeh (2014-2015).
Manyan Hafsoshin Sojin kasa da za a binciki zamaninsu sun hada da Laftana Janar Luka Yusuf (2007-2008) da Laftana Janar Abdurrahman Dambazzau (2008-2010) da Laftana Janar Azubuike Ihejirika (2010-2014) da kuma Laftana Janar Kenneth Minimah (Janairun 2014-Yulli 2015).
Manyan Hafsoshin Sojin Ruwa da za a binciki zamaninsun sun hada da Bayis Admiral G.T. Adekeye (2005-2008) da Bayis Admiral Iko.I. Ibrahim (2008-2010) da Bayis Admiral O.S. Ibrahim (2010-2012) da Bayis Admiral D.J. Ezeoba (2012-2013) da kuma Bayis Admiral U.O. Jibrin (2013-2015).
Hafsoshin Mayakan Sama da binciken zai shafa sun hada da Iya Mashal Paul Dike (2006-2008) da Iya Mashal Oluseyi Petirin (2008-2010) da Iya Mashal Mohammed Dikko Umar (2010-2012)  da Iya Mashal Aled Badeh (2012-2014) da kuma Iya Mashal Adesola Amosu (2014-2015). Mashawartan Shugaban kasa kan Tsaro da binciken ya shafa sun hada da Janar Aliyu Gusau da Janar Owoye Azazi da Janar Sarki Mukhtar da kuma Kanar Sambo Dasuki.
Sai kuma ministocin tsaro da za a binciki zamaninsu da suka hada da: Yayale Ahmed (2007-2008) da  Shettima Mustapha (2098-2009) da Godwin Abbe (2009-2010) da Adetokunbo Kayode (2010-2011) da Bello Haliru Mohammed (2011-2012) da  Erelu Olusola Obada (2012-2013) da Janar Aliyu Gusau (2013-2015) da kuma Musiliu Obanikoro (2012-2014).

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50