Manyan jami’an tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma 200 za su kalli fim din Juyin Sarauta a Abuja

Manyan jami’an hukumomin kula da tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma su 200 a karkashin jagorancin Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Hadiza Bala Usman, za su kalli fim din Juyin Sarauta a taron da za su gudanar a Abuja. Nuna fim din ya biyo bayan bukatar da ta bijiro wa Kamfanin Ramat […]

Manyan jami’an tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma 200 za su kalli fim din Juyin Sarauta a Abuja
Manyan jami’an tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma 200 za su kalli fim din Juyin Sarauta a Abuja

Manyan jami’an hukumomin kula da tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma su 200 a karkashin jagorancin Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA), Hadiza Bala Usman, za su kalli fim din Juyin Sarauta a taron da za su gudanar a Abuja.

Nuna fim din ya biyo bayan bukatar da ta bijiro wa Kamfanin Ramat Production, wanda ya shirya Juyin Sarauta daidai lokacin da aka gayyace ta kaddamar da fim din, sai shugabar ta fifita bukatar ganin dimbin al’umma daga Afirka ta Yamma sun amfana da fim mai nuni da tarihi da al’adar yadda ake gudanar da harkokin sarauta a rayuwar Bahaushe.

Fim din Juyin Sarauta ya kasance irinsa na Hausa na farko da ya zama zakaran gwajin dafi kuma ya taba shiga gasar Fina-finai ta Duniya ta Lake International Pan African Film Festibal da ake yi duk shekara a kasar Kenya, inda aka fitar da shi a jerin zakarun da za su fafata gasar a ranar 7 zuwa 10 ga Nuwamba, 2018. Sannan ya kasance a jerin fina-finan da za su fafata a gasar nagartattun fina-finai a nan gida Najeriya, wato Kaduna Film Festibal, wadda za a gudanar a Kaduna ranar 25-27 ga watan nan.

A shekarar 2017 fim din Juyin Sarauta ya lashe gasar Zuma Film Festibal, Abuja a matsayin fim din da ya fi kowane da aka yi da harshen  Najeriya (Best Nigerian Language Film), sannan a bana ya lashe kyautuka 6 a gasar AMMA.

Masana sun ce fim din Juyin Sarauta ya fito da hakikanin tarihi da al’adar Bahaushe kan yadda ake jan ragamar al’umma tsawon zamani a kasar Hausa, tare da matsalolin da ake fuskanta a harkokin sarauta. “Sarkin Jadarwa ya nuna yadda ya kamata a tarbiyyantar da wadanda ke gadon sarauta, domin tafiyar da harkokin rayuwar al’umma a kasar Hausa,” inji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON jarumin da ya fito a matsayin Sarki.

Shugabar Kamfanin Ramat Production, da ya dauki nauyin shiryawa da dawainiyarsa, Balaraba Ramat Yakub, ta yi fatan ganin da zarar fitowar Juyin sarauta kasuwa ya samu karbuwa don amfanin al’umma, musamman masu nazarin adabin Hausa a jami’o’i da manyan makarantun kasar nan.