Manyan kasashen duniya na rububin gayyatar Buhari
Manyan kasashen duniya suna rububin gayyatar Shugaban kasa Muhammdu Buhari don kai musu ziyara a bana a wani abu da ke nuna dawowar martabar Najeriya a idon duniya. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ta lura a baya-bayan nan bayan rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari jaridun kasashen duniya sun sauya akalar alkalumansu wajen bayar da […]
Manyan kasashen duniya suna rububin gayyatar Shugaban kasa Muhammdu Buhari don kai musu ziyara a bana a wani abu da ke nuna dawowar martabar Najeriya a idon duniya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ta lura a baya-bayan nan bayan rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari jaridun kasashen duniya sun sauya akalar alkalumansu wajen bayar da labarai masu dadi game da Najeriya.
Kuma ana jin wannan ne ya sanya kasashen Ingila da Amurka da Indiya suka gayyaci Shugaba Buhari domin ya gana da manyan jami’ansu. Baya ga haka ana jira Shugaban na Najeriya da ayarinsa a wajen bikin cika shekara 70 na Majalisar dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York a watan Satumba mai zuwa.
Akwai yakinin taron na Majalisar dinkin Duniya zai bayar da wata dama ta musamman ga Najeriya wadda take farfadowa tare da samun tagomashi a idon duniya, a gefe guda kuma ta inganta alakarta da sauran kasashen duniya da shugabanninta a matsayinta na jagorar Afirka.
Bayanai sun ce, ziyarartar Amurka za ta haifar da alheri da dama ta musamman ta farfado da kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu bayan da ta yi tsami sakamakon sace ’yan matan Chibok lokacin da Amurka ta so shiga aikin soji na hadin gwiwa don ceto ’yan matan.
Nasarar Buhari da Osinbajo a zaben Shugaban kasa da ya gabata, ana sa ran ya kawo karshen takaddamar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Nahiyar Afirka Misis Linda Thomas-Greenfield, tuni ta fara tattaunawa da wakilan Najeriya kan tsare-tsaren ganawar da za ta gudana a tsakanin shugabannin kasashen biyu a fadar White House da ke Amurka.
Sai dai kuma ba a ayyana ranar da Shugaba Buhari zai ziyarci kasashen da aka ambata ba, amma wata majiya a fadar Shugaban kasa da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa za a sanar da ranakun kwanan nan, kuma akwai yiwuwar Amurka zai fara zuwa.
Bayan rantsar da Shugaban kasa Buhari ya kai ziyara kasashen Nijar da Chadi da Jamus da Afirka ta Kudu, inda a dukkanin tafiye-tafiyen suka tattauna matsalar tsaro da ke barazana ga kasar nan.