Manyan labarai a shekara ta 2013

Shekarar 2013, ita ce shekara ta 13 a shekarun karni na 21, kuma ba shekara ba ce wadda Fabrairunta ke da kwanaki 29, sannan ranar farko a cikinta ita ce talata; don haka shekarar 2014 za ta kama a ranar Laraba. ( a tsarin kirgar Romawa (Roman Numerals): MMdIII).                           Ariel Castro, Wanda ya boye ’yan mata […]

Manyan labarai a shekara ta 2013

Shekarar 2013, ita ce shekara ta 13 a shekarun karni na 21, kuma ba shekara ba ce wadda Fabrairunta ke da kwanaki 29, sannan ranar farko a cikinta ita ce talata; don haka shekarar 2014 za ta kama a ranar Laraba. ( a tsarin kirgar Romawa (Roman Numerals): MMdIII).
                           Ariel Castro,
 Wanda ya boye ’yan mata uku har tsawon shekara 10. Kafafen yada labarai sun dade suna yamadidi da shi. Labarin Castro ya bayyana a a ranar 6 ga Mayun 2013. Inda ya kama matan a kan titin Clebeland  a tsakanin shekarun 2002 zuwa 2004; a lokacin shekarunsu sun kama daga 14 da 16 zuwa 20.

 

 

Yarinya rike da hoton Nelson Mandela wajen bikin binne gawarsaMutuwar Mandela
Mutuwar Shugaba Nelson Mandel na Afirka ta Kudu, ranar 5 ga Disambar 2013, ta girgiza al’ummar duniya.
A ranar 13 ga Fabrairun 2013, an kama gwarzon wasan nakasassu na olymfik, Oscar Pistorius  da tuhumar laifin kashe budurwarsa, Reeba Steeenkamp a gidansu da ke birnin Pretoria ta Afirka ta Kudu.

Tsarin Kula da lafiya na Obamacare
A shekarar 2013, Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya gano cewa tsarin kula da lafiya na Obamacare, na cikin labaran da suka karade duniya, musamman ganin yadda ya haifar da takaddamar da ta dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka al’amarin da aka aiwatar a ranar 1 ga Oktoba; kuma ba a taba ganin irin wannan al’amari ba a tsawons hekara 17. An kuma shafe kwana 15, inda ma’aiaktan Gwmanatin Tarayya har miliya guda da dubu 300 suka shiga wani mummunan hali; sannan kasar ta haifar wa masu biyan haraji asarar Dala biliyan biyu.

Murabus din Paparoma Benedict
Murabus din Paparoma Benedict dbI  a Fabrairu, inda aka nada Pope Francis, ya tayar da kura, ba ma a tsakanin mabiya darikar Katolika ba, har da daukacin al’ummomin duniya; don kowa da yadda ya rika fassara al’amarin.

Jaririn gidan Sarautar Ingila
An haifi Yarima George na Cambridge ( wanda aka yi wa lakabin George Aledander Louis, a ranar 22 ga Yulin 2013.

Edward Snowden
Wanda ya yi wa Hukumar tsaron Amurka tonon asiri, ya yi matukar tayar da kura, musamman yadda ya sulale ya gudu zuwa kasar Rasha, inda ya shafe wata guda kafin ya samu mafakar siyasa a kasar. Al’amarin tonon asirin Snowden tun watan Janairu ake ta takaddama a tsakanin Amurka da kasashen duniya, a zuwa karshen shekarar nan , ind aya bayyana ya cimma manufarsa ta rayuwa, a hirar da ya yi jaridar Washington Post.

Guguwar Haiyan a Filifins
A ranar 8 ga Nuwambar 2013 aka yi guguwar Typhoon Haiyan, wadda ta haifar da asarar rayuka dubu shidda a kasar Filifins; ta lalata gidajen mutum miliyan 16, yayinda da daruruwan mutane suka bace.