Manyan makarantu sun fara yajin aikin gargaɗi a Yobe

Ƙungiyar ta ce sai gwamnatin jihar ta saurari buƙatunsu sannan za a daidaita kan yajin aikin.

Manyan makarantu sun fara yajin aikin gargaɗi a Yobe

Ƙungiyar Manyan Makarantu a Jihar Yobe (JASU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na mako guda daga ranar Litinin.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ta aike zuwa ga dukkanin shugabannin ƙungiyar mai lamba JASU/ADM/03/VOL.4.1.

Shugaban JASU, Dokta Modu Lawan Gana ne, ya sanya hannu, kuma ya bayyana wa manema labarai a Damaturu.

“Wannan shawarar ta zo ne bayan tsawaita wa’adin da aka bayar a ranar 23 ga watan Satumba, 2024.

“Ya ƙare ba tare da ɗaukar mataki ba daga ɓangaren gwamnatin jiha dangane da bukatunmu ba.”

Sanarwar ta ce, an yanke hukuncin ne bayan ƙuduri mai kwanan wata 23 ga Satumba 2024 kan tsawaita wa’adin da mako guda.

“Matuƙar gwamnatin Jiha ba ta yi wani abu ba, ina sanar da ku a ƙungiyance cewa za a kai tsawon mako guda ana yajin aiki.

“Don haka ana kira ga mambobin JASU da su ci gaba da wannan yajin aiki na gargaɗi na mako guda daga ranar Litinin 30 ga Satumba, 2024.

“Da fatan za a tabbatar da cewa an hana duk ayyukan da suka shafi koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba a makarantun ƙaro ilimi da ke jihar nan har sai an cimma matsaya nan ba da daɗewa ba, muna roƙon ku da ku bayar da haɗin kai da bin ƙa’idojin taronmu.”

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro