Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa

Yajin aikin ya shafi manyan makarantu daban-daban ciki har da kwalejojin ilimi da fasaha da na lafiya da ke faɗin Jihar Adamawa.

Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri

Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris.

Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin.

Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu.

Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani.

Aminiya ta ruwaito cewa, yajin aikin ya shafi manyan makarantu daban-daban ciki har da kwalejojin ilimi da fasaha da na lafiya da ke faɗin Jihar Adamawa.

Ƙungiyoyin dai na neman gwamnatin ta mayar da mambobinsu kan tsarin albashin manyan makarantu da kuma tsarin sabon albashi mafi ƙanƙanta da kuma janye tsarin zaftare albashinsu da ake yi da sunan haraji.

Natasha ta yi ƙarar Akpabio a Majalisar Dinkin Duniya

’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan

DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?

Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa