Manyan matsaloli 10 da Buhari zai fuskanta a bana

Bayan ya aza harsashin gudanar da mulki ta hanyar nada manyan jami’ai daministoci, babban kalubalen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fuskanta zai faru ne a bana. Shugaban kasar ya nuna ya shirya wa fuskantar kalubalen a bana, ta hanyar gabatar da kudirin kasafin kudin bana ga Majalisar Dokoki ta kasa a makon shekaranjiya. Wannan […]

Manyan matsaloli 10 da Buhari zai fuskanta a bana
Manyan matsaloli 10 da Buhari zai fuskanta a bana

Bayan ya aza harsashin gudanar da mulki ta hanyar nada manyan jami’ai daministoci, babban kalubalen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fuskanta zai faru ne a bana. Shugaban kasar ya nuna ya shirya wa fuskantar kalubalen a bana, ta hanyar gabatar da kudirin kasafin kudin bana ga Majalisar Dokoki ta kasa a makon shekaranjiya. Wannan ne ya sa jaridar Aminiya ta yi kokarin gano wasu manyan matsaloli da za su iya zama kalubale ga Shugaba Buhari a daidai lokacin da yake kokarin cimma kudirorinsa:

Tallafin mai: A daidai lokacin da muka shiga sabuwar shekara a yau, ’yan Najeriya za su fara kashe kunne domin jin shawarar Buhari game da batun da aka fi cece-ku-ce kansa na janye tallafin man fetur. Ana ta yi masa kiraye-kirayen ya kawo karshen wannan tsari, wanda kwararru da ’yan Najeriya da dama suke dora wa alhakin jawo wahalar mai a sassan kasar nan. Yarda da janye tallafin ko kin yarda za ta zamo shawara mai wahala da fadar Shugaban kasa za ta dauka a bana. Kuma ’yan Najeriya za su zuba ido su ga ko Buhari zai iya yanke shawarar kawo karshen haka, ta yadda za a kawo karshen karancin mai da kuma mummunar almundahanar da ake tafkawa wajen shigo da man fetur daga waje.

Boko Haram: Bayan rantsar da shi, Shugaban kasa Buhari ya ba wa kwamandojin soja cewa zuwa karshen Disamban da ya gabata, su kawo karshen hare-haren Boko Haram da suka addabi yankin Arewa maso Gabas. Kuma a farkon makon jiya an ruwaito shi yana cewa ‘an karya lagon Boko Haram.’ Wannan ra’ayi ne Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ya rika maimatawa, kuma ya ce, Boko Haram ta koma matsayin da ba za ta rike wani yanki na Najeriya ba.
Wannan ya nuna an samu gagarumar ci gaba idan aka kwatanta da baya, lokacin da mayakan Boko Haram suke rike tare da sanya tutocinsu a kananan hukumomi da daman a Jihar Borno da Yobe da Adamawa. Sai dai duk da nasarorin da aka samu, maharan Boko Haram sun ci gaba da kai hare-hare nan da can, ciki har da hare-haren bama-bamai musamman a kan fararen hula. Sannan dubban ’yan Najeriya har yanzu suna zaune ne a sansanonin ’yan gudun hijira a sassa da dam na kasar nan, saboda ba a bayyana cewa suna iya komawa garuruwansu don komai ya yi lafiya. daya daga cikin kalubalen da Shugaba Buhari zai fuskanta a bana shi ne samar da wani kayyadajjen lokaci n araba Arewa maso Gabas da sauran birbishin Boko Haram, domin mutanen da aka raba su da muhallinsu su koma garuruwansu. Wani kalubalen kuma shi ne na yadda za a kawo karshen matsalar satar mutane ana garkuwa da su da kuma satar shanu da suke dada karuwa a sassan kasar nan.
 Biyan albashi: Biyan albashi yana daga cikin manyan matsalolin da wasu gwamnonin jihohi suka fuskanta a lokacin da suka karbi ragamar mulki a watan Mayun bara. Wannan ya jawo da dama daga cikinsu suka nemi tallafin Gwamnatin Tarayya, inda Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a yi haka ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN). Babban Bankin ya ba su Naira biliyan 338 a matsayin tallafi na musamman ga jihohin musamman don su biya bashin albashin da ake bin su. Matsalar biyan albashi tana ci gaba da zama alakakai ga gwamnatocin jihohi da dama. Yadda za a a warware wannan matsala a daidai lokacin da kudin shigar da ake samu daga man fetur ke dada yin kasa na daga cikin manyan matsalolin da gwamnatin Buhari za ta fuskanta.
Abin da zai yi da Jonathan: Yayin da zabensa ya ta’allaka da yaki da cin hanci da rashawa, Shugab Buhari ya fara fuskantar batun da yi wa tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki wanda na hannun dama tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne shari’a, bisa zargin karkatar da kudin sayen makamai. Wasu daga cikin al’amuran da suka shafi karkatar da kudin makaman da izinin Shugaba Jonathan. Sai dai har yanzu fadar Shugaban kasa ba ta nuna wata sha’awa ta yi wa Jonathan tambayoyi kan batun sayo makaman ba, duk da cewa an gurfanar da wasu daga cikin mukarrabansa a gaban kotuna kan lamarin.
Batun sayo makaman daya ne daga cikin bangarori da dama da Buhari ya fara bincika, kuma ta yiwu a binciki sassa da dama a bana, lamarin da ke kawo tambayoyi kan yadda Buhari zai yi da magabacinsa. Kwanakin baya Kakakinsa, Femi Adesina, ya ce babu wani abu da ya zame matsala ga Shugaban kasar game da batun Jonathan, in da ya bayyana cewa yiwuwar bincikar tsohon Shugaban kasar a matsayin wata gada ce da za su iya tsallake ta a lokacin da suka isa kanta. Ko wannan gwamnati za ta isa gadar ko a’a a bana, ’yan Najeriya suna ji suna gani suna kuma saurare.
Ina za a fuskanta da yaki da cin hanci?: Yadda aka faro da almubazzarantar da kudin sayo makamai da ake zargin gwamnatin da ta gabata, mene ne ke kunshe a rumbunan sauran sassa da daidaikun mutane? Sananne ne cewa akwai sauran sassan tattalin arzikin kasa da za a iya bincika. Wato kamar bangaren man fetur da ma’aikatar kudi ta tarayya. Tabbas wannan babban aiki ne da ke gaban fadar Shugaban kasa a bana.
A baya, hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suna gudanar da bincike kan cin hanci da rashawa ne su gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotuna, inda ake gaza cin nasara ko a dakile ci gaba da shari’a ko ma a yi watsi da ita. Babbar jarrabawar da yaki da cin hanci da rashawa na Buhari zai fuskanta shi ne yawan barnar da za a bankado a yi bincike a kai a gabatar gaban kotu tare da yanke hukunci da kuma kwato kudaden.
Faduwar darajar Naira: Darajar Naira ta ci gaba da faduwa a ’yan watannin nan, har zuwa matsayin da take kai na Dala daya Naira 260. daya daga cikin manyan kalubalen da Buhari zai fuskanta a bana, shi ne yadda zai dakatar da faduwar darajar Naira, wadda take jawo mummunar karayar tattalin arzikin kasa da kawo cikas ga tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnati.
Samar da wutar lantarki: Shekara da shekaru samar da ingantacciya kuma wadatacciyar wutar lantarki na cikin manyan kalubalen da kasar nan ke fuskanta. Wasu hukumomin bincike a baya sun gano an kashe makudan kudi a bangaren ba tare da samun wani ci gaban kirki ba. Kuma duk da haka ana sa ran Shugaba Buhari ya kara hobbasa a bangaren wutar lantarki a bana, kuma ya farfado da aikin samar da wutar lantarki na Mambila wanda wasu kamfanonin kasar China suke da sha’awa a kai.
Tabbatar da kasancewar APC a dunkule: Sakamakon lashe zabe da kuma yadda za a raba ganimar nasarar da aka samu, manyan wadanda suka jagoranci yakin zaben za su bukaci a tuna da su yayin rabon ganimar. Tabbas a bana, akwai bukatar Shugaban kasa ya yi taka-tsantsan don kauce wa fuskantar matsala da wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC, manya daga cikinsu su ne, tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Cif Bola Tinubu da Dokta Rabi’u Kwankwaso da Alhaji Aliyu  Wamakko da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai kuma Gwamnan Jihar Sakkawato, Alhaji Waziri Tambuwal. Wadannan muhimman mutane ne da suka taimaka wajen samun nasarar jam’iyyar a matakin kasa. Akwai bukatar Shugaba Buhari ya nemo hanyoyin sauraren bukatunsu na kashin kai da bukatunsu na siyasa ta yadda ba za su ji cewa an yi waje da su wajen rabon ganimar nasarar da aka samu ba.
Shin ministocinsa za su fidda shi kunya?: Shugaba Buhari ya dauki dogon lokaci yana kokaribn zakulo mutanen da suka dace ya nada a matsayin ministocinsa. Kuma kamar yadda aka sanya rai, wasu fitattun mutane an ba su “muhimman” ma’aikatu a abin da gwamnati take gani daya daga cikin shirye-shiryenta na tabbatar da dorewar ci gaban kasa ne. Daga cikin wadanda aka ba muhimman ayyuka da ’yan Najeriya suke fatar su fitar da gwamnatin Buhari daga kunya akwai: Audu Ogbeh, Aikin gona da Rotimi Amaechi, Sufuri da Chris Ngige, kwadago da Samar da Aiki da Kayode Fayemi, Albarkatun kasa da Babatunde Fashola, Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje da Ibe Kachikwu, Minista a Ma’aikatar Man Fetur da Isaac Folorunsho, Lafiya. Shugaban kasar ya sanya samar da aikin yi da farfado da aikin gona da inganta samar da kayan jin dadin rayuwa da hako albarkatun kasa a matsayin manyan ayyukan da gwamnatunsa za ta fi mayar da hankali a kai. Don haka za a sanya ido kan rawar da minsitocin da aka ba wadannan ma’aikatu za su taka wajen gudanar da ayyukansu.
Babu shakka Shugaba Buhari ne shugaban da bai ci sa’a ba, idan aka lura yadda ya zo gadon mulki a daidai lokacin da ’yan Najeriya suke gaggauce su ga an samu ci gaba a kasar nan fiye da kowane lokaci, don haka wajibi ne ministocinsa su tashe tsaye wajen yin abin da ya dace – domin ganin Buhari bai gaza a bana ba.