Manyan mutanen da Tinubu ya sallama daga aiki
Tun bayan karbar mulki Gwamnatin Tinubu ke ta daukar tsauraran matakai
Tun Bayan karbar mulki daga tsohon shugaban kasa, Muhamamdu Buhari a ranar 29 ga Mayu, 2023, Gwamnatin Tinubu ke ta daukar wasu matakai masu tsauri daidai da manufofinta da tsare-tsarenta.
Daga ciki kuwa har da sallamar wasu manyan jami’an gwamnatin Buhari; Ga wasu daga cikinsu, albarkacin cikar Bola Ahmed Tinubu kwana 100 da zama Shugaban Kasar Najeiya:
- Abin da ya kamata ’yan mata masu son shiga fim su yi —Amaryar TikTok
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Bambanta Kotun Zaɓen 2023 Da Na Baya
Gwamnan Bankin CBN
Kwana 12 da hawan Tinubu kan mulki ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a ranar 9 ga watan Yuni ya sa a bincike shi, a ci gaba da binciken da ake wa ofishinsa kan sabon tsarin hada-hadar kudi.
Emefiele ya taka muhimmiyar rawa wajen sake fasalin kudi da na takaita amfani da tsabar kudi da aka bullo da shi gabanin zaben da Tinubu ya lashe da nufin takaita sayen kuri’u da ’yan siyasa ke yi.
Shugaban EFCC
A ranar 14 ga Yuli, 2023, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya sanar cewa Tinubu ya dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa sakamakon wasu manyan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa.
Tun lokacin Bawa ke tsare ba a gurfanar da shi ba, amma “gwamnati ta ce hakan zai ba da damar gudanar da bincike mai kyau zargin da aake masa.”.
Manyan Hafsoshin Tsaro
A ranar 19 ga watan Yuni Tinubu ya sallami daukacin manyan hafsoshin tsaro da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada — Janar Lucky Irabor, babban hafsan hafsoshin tsaro; Shugaban hafsan soji, Farouk Yahaya; Shugaban hafsan sojin ruwa, Awwal Gambo; Shugaban hafsan sojin sama, Isiaka Amao — da Sufeto Janar na ’yan sanda, Usman Alkali.
Babagana Monguno
A ranar ya sallami mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya nada Malam Nuhu Ribadu a ranar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen zaman hafsoshin tsaron kasar.
Da farko ya nada Nuhu Ribadu mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kafin daga bisani ya zama mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Shugaban APC
16 ga watan Yuni shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar ajiya aikinsa, wanda aka yi amannar cewa ya yi haka ne don gudun kada gwamnati mai ci ta kunyata shi saboda rawar da ya taka a lokacin babban taron jam’iyyar APC na 2022 wanda ya samar da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasan jam’iyyar.
Jakadun Najeriya
Ranar 3 ga watan Satumba Tinubu ya umarci duk jakadun kasar nan da su dawo gida zuwa 31 ga watan Oktoba, amma bada Jakadan Nigeriya da ke zauren Majalissar Dinkin Duniya.
A watan Janairun 2021 ne Buhari ya amince danada jakadu 95 zuwa kasashe daban-daban bayan amincewar majalissar dattawa.