Manyan sababbun da ke kawo mutuwar aure (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban mukalar da muke kawo muku.(11) Auren Jari-Hujja: Wasu iyayen na dogara ne da abin da ’ya’yansu ke samu a gidan miji, inda za a ga tana diban kayan abinci ba da izinin miji ba, ko ta rika yanke kudin cefane, idan mijin ya […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban mukalar da muke kawo muku.
(11) Auren Jari-Hujja: Wasu iyayen na dogara ne da abin da ’ya’yansu ke samu a gidan miji, inda za a ga tana diban kayan abinci ba da izinin miji ba, ko ta rika yanke kudin cefane, idan mijin ya gane sai ka ga auren ya mutu. Wani lokaci kuma mazan ne ke yi auren don su amfana da nasaba ko dukiyar gidan surukansa, a karshe idan gaskiya ta yi halinta auren ya mutu.
(12) Auren kisan wuta: Wasu matan na yaudarar mazan da suka zo neman aurensu, don su cimma burinsu na koma wa gidan tsohon mijinsu. Inda mazajen ba su yi bincike ba sai ka ga sai bayan an yi auren sai mijin ya rasa ina matsalar take bayan sun yi auren soyayya kuma kiyayya ta biyo baya. Ku sani Manzon Allah (SAW) ya tsine wa wanda ya yi aure don ya halatta wa wani ita matar kuma ko da sun koma auren bai halatta ba.
(13) Mace ta dauka ‘ya’yanta ne kawai ‘ya’ya: Wannan ba karamar matsala ba ce da ke tasiri a cikin al’ummarmu, sai ka ga mace ko don ba su yi zaman dadi da kishiyarta ba ko kuma wata ma ba ta zauna da uwar ba, sai su dau karan tsana su saka wa yaran wanda har zai iya kawo lalacewar tarbiyyar yara. Irin wadannan na sanya bayan mahaifin yaran ya gane ya dauki matakin da zai haifar da saki.
(14) Rashin daukar namiji shugaba: Hakan na sanya namiji ya hasala, inda a karshe ka ga auren ya mutu.
(15) daukar mace bai wa maimakon abokiya: Allah Ya kira mace da abokiya a cikin kur’ani, don haka mace ba baiwa ba ce kamar yadda wasu ke daukarsu. Yadda ake daukar matan ne idan an yi aure yakan sa wadansu su kasa jurewa a karshe auren ya mutu.
(16) daukar muguwar shawarar kawaye: daukar irin wannan shawara na sanya aure ya mutu. Bai kamata a ce mace tana yada sirrin mijinta ga kawayenta ba, kai ko mahaifanta ba komai za ta fada musu ba.
(17) Tsananin kishi: Wani daga cikin magabata ya yi wa ’yarsa huduba yayin da zai kai ta gidan miji da cewar ‘kashedinki da kishi domin kishi mabudin saki ne’. Idan har maigidanki ya yi niyyar karo aure ke kuma kika ce ba zai yiwu ba a karshe sai ka ga auren ya mutu.
(18) Mace ta ki karbar gyara ko kuskure: Sau tari mata ba su so in sun yi laifi a ce don me ki ka yi kaza, karshe su rufe idanu su ce me suka yi? Wannan yakan sanya mazaje su ga matansu ba su dauke su a bakin komai ba. A karshe auren ya mutu.
(19) Kafirce wa miji: Manzon Allah (SAW) ya ce ya leka cikin wuta sai ya ga mafiya yawan wadanda ke ciki mata ne’. Haka annabi (SAW) ya ce ‘yaku taron mata ku yawaita sadaka da istigfari domin mafiya yawanku ‘yan wuta ne, sai wata ta ce saboda me? Sai ya ce kuna kafirce wa mazajenku (rashin godiya).” Sai ka ga hakan ya haifar da mutuwar aure.
(20) Rashin adalci: Namiji zai karkata a kan mace guda ta zama mowa ko kuma ya dauki karan-tsana ya saka wa ‘ya’yan wata, to wannan bai dace ba kuma Manzon Allah (SAW) ya ce duk mai irin wannan halin Allah zai tayar da shi da barin jikinsa a shanye.
Za nu ci gaba.