Manyan sababbun da ke kawo mutuwar aure 23
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad SAW.Aure dai kamar yadda muka sani ibada ne kuma sunna ne da kowane manzon da Allah SWT Ya aiko bisa doron kasa sai ‘yan kadan wadanda ba su yi aure ba.A wannan mukalar na rairayo wadansu […]
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad SAW.
Aure dai kamar yadda muka sani ibada ne kuma sunna ne da kowane manzon da Allah SWT Ya aiko bisa doron kasa sai ‘yan kadan wadanda ba su yi aure ba.
A wannan mukalar na rairayo wadansu sabubba a takaice da suke kawo mutuwar aure, ina kuma fata za a kiyaye su don a samu dorewar rayuwar aure.
(1) Rashin daukar aure a matsayin ibadah: Hakika aure sunnah ne na kowane manzo, kuma manzon Allah (SAW) ya ce “aure sunnata ce kuma wanda ya kyamace ta ba ya tare da ni.” Abin takaicin shi ne da yawan mutane sun dauki aure a matsayin wata kafa ta biyan bukatar sha’awa ba wai ibada ba, hakan na kawo mutuwar aure.
(2) Rashin tsarkake zuciya yayin aure: Kamar yadda muka sani kowace irin ibada ba ta inganta idan babu ikhlasi (yi don allah). A wannan zamani ba a cika yin aure don Allah ba, sai ka ga an yi aure tun ba a je ko’ina ba ya mutu.
(3) Rashin zaben da ya dace: na haifar da mutuwar aure. Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘ana auren mace don abubuwa hudu: kyau, dukiya, nasaba da addini, sai ya ce “ina umartarku da ku zabi ma’abociyar addini sai ku rabauta.” Amma a yanzu abin ba haka yake ba, zuciyata ta fi kawatuwa da kyalkyali maimakon na addini, hakan zai sa aure ya mutu. Haka ma ga bangaren mata. Kada a manta rashin zaben mijin da ya dace ma na haifar da mutuwar aure, domin Manzon Allah (SAW) ya ce “idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi’arsa ya zo neman auren ’yarku, to ku aurar masa idan kuka ki kuma fitina za ta yadu a doron kasa da fasadi mai girma.” A yanzu ba a yin haka, an fi tambayar mai kudi ne ko talaka, idan kuwa haka ne duk inda kwadayi ya yi rinjaye to za a fuskanci wulakanci.
(4) Rashin aikin yi: Manzon Allah (SAW) ya ce ‘ya ku taron matasa, wanda yake da iko ya yi aure, wanda ba shi da hali kuma ya yi azumi zai zame masa daddaka. Akwai aure da yawa da suka mutu saboda mijin ba shi da aikin yi da gara ta kare sai a rabu.
(5) karairayi wajen neman aure: Abin takaici wasu za su yi aron mota ko sutura ko wayar hannu, mace kuma za ta nuna wani babban gida tace nasu ne, ko saurayi ya yi alkawarin zuwa yawon shakatawa bayan sun yi aure da sauransu. A karshe a gane karya ce, wanda hakan kuma sai ya haifar da mutuwar aure.
(6) Tsoron haihuwa: Akwai mazan da za su auri mace tana samun ciki sai su dauki karan tsana su dora mata, wata ma sai dai ta haihu a gidansu, kuma wata za su auro sai ka ga sun tara ‘ya’ya iyayensu daban-daban.
(7) Auren sha’awa: Akwai mazajen da in sun ga mace suka bukace ta, to ko ta wane hali sai sun auro ta, kuma da zarar sun tara da ita za su sake ta. Akwai wanda aka fada mini ya auri mata 26.
(8) boye ciwo ko mugun hali: Wajibi ne iyaye su bayyana wata cuta da ke damun ‘ya’yansu, idan an amince shi ke nan, amma a yanzu sai a rika boye cuta ko wani hali, wanda a karshe a gane an yi ha’inci, kuma ya haifar da mutuwar aure.
(9) Asiri: Wani salo ne da mutane suke mallakar masoyansu. Akan yi hakan ne ta hanyar bin muggan malamai da bokaye, wanda a karshe idan ya karye sai ya haifar da mutuwar aure.
(10) Auren dole: Ya tabbata wata ta kawo karar iyayenta wurin Manzo Allah (SAW) akan sun yi mata auren dole, ya ce tana da zabi; ko ta zauna ko a raba auren. Sai yarinyar ta ce za ta zauna da shi, ta yi hakan ne don iyaye su fahimci ba su da hurumin tilasta wa ’ya’yansu auren wadanda ba sa so.
Za mu ci gaba.