Manyan sabubban da ke kawo mutuwar aure

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban mukalar da muke kawo muku.1.  Zargi: Hakika idan ma’aurata suka rika zargin juna a nan ma aurensu ba zai ko’ina ba.2.  Rashin bin ka’idojin saki: Kafin a kai ga saki akwai matakai da Allah (SWT) Ya kawo a al-kur’ani kama daga yi wa […]

Manyan sabubban da ke kawo mutuwar aure
Manyan sabubban da ke kawo mutuwar aure

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban mukalar da muke kawo muku.
1.  Zargi: Hakika idan ma’aurata suka rika zargin juna a nan ma aurensu ba zai ko’ina ba.
2.  Rashin bin ka’idojin saki: Kafin a kai ga saki akwai matakai da Allah (SWT) Ya kawo a al-kur’ani kama daga yi wa mace wa’azi, kauracewa a shimfida kana duka wanda ba mai cutarwa ba. Idan abin ya ci tura kuma a zauna tsakanin wakilan bangarorin har Allah Ya ce in an yi da niyyar gyara kuma za a cim ma maslaha. Idan abin ya ci tura ga matakan saki kamar yadda ya zo cikin suratul dalak. “Kar ka saki mace sai tana cikin tsarkin da ba ka tara da ita ba. Ka samu shaidu adalai biyu. Kana mace ta yi idda a dakinta sai har in ta zo da wata alfasha.” Rashin bin wadannan ne ka’idojin ne yake haifar yawan rabuwar aure.
3.  kazanta: Akwai matar da tana iya kwashe wata ba ta daga kujera ta share ba. Kana iya tashi da safe kuma ka iske kayan abincin a wurin da aka ci abincin. Uwa uba akwai matan da in ka rabe su za ka ji su suna wari ko tsami. Haka akwai mazajen da idan sun dawo aiki haka suke kwantawa ba tare da sun yi wanka ba, inda za ka ji suna wari. kazanta daga kowane bangare na sanya aure ya mutu.
4.  Namiji mai dukan mace: Ka ga a nan babu wanda zai aurar da ’yarsa ga wani katon da zai rika dukan matarsa. Bayan an yi aure za ka samu wadansu mazaje suna dukan matansu, hakan sai ya haifar rabuwa.
5.  karin aure alhali babu ikon: Akwai masu auren gasa ai wane biyu gare shi don haka ni ma biyu zan yi, ba su duba dalilai da hikimomin da Allah (SWT) ya ce a yi sama da daya ba. Wani sai ka samu bayan ya yi auren ya kasa biyan bukatar matansa ta saduwa, wani kuma ya kasa daukar nauyin gidansa saboda nauyi ya yi yawa. Hakan sai ya sa aka hakuri, karshe auren ya mutu.
6.  Yawan kai kara: Bai dace ma’aurata su dinga kai karar junansu ba. Don kuwa suna iya sasanta kawunansu, amma iyayen na can na ganin bakin wani, hakan sai ka ga aure ya mutu.
7.  Sanya karya farkon aure wurin ciyar da gida, daga ranar da ya canja da yadda ya saba ciyar da gidan sai ka ga ta canja masa sai rikici, a karshe auren ya mutu.
8.  Cin bashi don yin bukatunta da sunan miji.
9.  daukar salon rayuwar Turawa: Akwai mazajen da za su mayar da gidansu kamar hotel suna kawo abokanan su suna zama falo da matarsa, karshe zargi ya shiga, wanda zai yi sanadiyyar mutuwar auren.
10.  karya: Tsakanin ma’aurata na haddasa mutuwar aure.
Kadan ke nan daga cikin sabubba dubbai da a halin yanzu ke kawo tarnaki har a rika jin garuruwa da dama ‘yan mata da zawarawa na zanga-zanga wai sun rasa mazajen aure.
Sai mu zama alkalai don kuwa wadannan laifuffuka ba su karkata a jinsi guda ba, sai dai za a iya cewa wani jinsin ya fi daukar kaso mai tsoka. Da fatan Allah Ya sa mu ji kuma mu gyara don mu samu rabauta duniya da lahira.
Naku: Sanusi Hashim Katsina (Abu-Abdullah) 08065507271