Manyan Taraba ke haddasa fitina a jihar

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Taraba Injiniya Ahmad Zakari Ngoroje ya ce abin kunya ne yadda jihar ta zama koma-baya tare da kasancewa a sahun gaba wajen haddasa fitina da kashe jama’a.Injiniya Ngoroe ya shaida wa wakilin Aminiya haka ne a lokacin da suke tattaunawa a Abuja, inda ya dora alhakin aukuwar fitinu […]

Manyan Taraba ke haddasa fitina a jihar
Manyan Taraba ke haddasa fitina a jihar

Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Taraba Injiniya Ahmad Zakari Ngoroje ya ce abin kunya ne yadda jihar ta zama koma-baya tare da kasancewa a sahun gaba wajen haddasa fitina da kashe jama’a.
Injiniya Ngoroe ya shaida wa wakilin Aminiya haka ne a lokacin da suke tattaunawa a Abuja, inda ya dora alhakin aukuwar fitinu da kashe-kashen jama’a kan son zuciyar wasu manyan jihar, musamman ’yan siyasa wadanda ba sa kyautata wa jihar da matasanta.
Injiniya Ngoroji wanda ya zargi wadannan ’yan siyasa da yin amfani da matasa don cimma burinsu na kashin kai, ya bukaci matasan jihar su sanicewa kowace jam’iyya mutum yake, bai kai matsayin Jihar Taraba ba domin mutanen na bukatar zaman lafiya da ci gaba. “Ya kamata addinin mutum, ko jam’iyarsa ko kabilarsa su zamo sila na ci gaba ne ba jawo fadace-fadace ba. Duk dan Taraba ya san cewa jiharmu na daya daga cikin jihohin da suke baya a kasar nan, to lallai ne a samu zaman lafiya domin a samu ci gaba a fita daga matsala,” inji shi.
Ya ce ya kamata matasan sun sani cewa ’ya’yan wadannan manya ba su shiga cikin harkokin tayar da zaune-tsaye, ya ce ’ya’yan manyan ya kamata su shiga gaba in dai aiki ne mai kyau domin su ci riba su kai wa iyayensu. “Amma da yake an san aikin laifi ne sai dai su sayi makamai da kayan maye su ba ’ya’yan talakawa su tura su. Ba yadda za a yi Najeriya da Taraba su ci gaba in ba zaman lafiya da hadin kai,” inji shi.
Ya shawarci matasa su tashi su nemi ilimi da sana’a kuma su yi hakuri a lokacin karatu ko sana’a domin hakuri na da amfani tare da kawo nasara. Ya ce matasan Najeriya suna da daraja matuka don haka ya kamata su zamo masu bin doka sun fito su zabi wadanda za su kare musu martaba, maimakon bata rawarsu da tsalle wajen aikata laifuffuka da karya doka da sauran miyagun ayyuka.