Manyan ’yan adawa sun cika Sakkwato don bude Jami’ar Jihar
A ranar Talatar da ta gabata ce aka bude sabuwar Jami’ar Jihar Sakkwato da aka gina ta kan Naira biliyan 17 cikin shekara biyu, inda jiga-jigan ’yan adawan kasar nan suka halarci bikin bude ta.Jami’ar wadda za ta fara karatu da dalibai 800 wurin bude ta an fito da sabon salon siyasa, inda Gwamnoni Bakwai […]
?????????????????????????????????????????????????????????

A ranar Talatar da ta gabata ce aka bude sabuwar Jami’ar Jihar Sakkwato da aka gina ta kan Naira biliyan 17 cikin shekara biyu, inda jiga-jigan ’yan adawan kasar nan suka halarci bikin bude ta.
Jami’ar wadda za ta fara karatu da dalibai 800 wurin bude ta an fito da sabon salon siyasa, inda Gwamnoni Bakwai na Jam’iyyar PDP da ke fada da shugabannin jam’iyyarsu kuma ake rade-radin za su koma Jam’iyyar APC suka hallara.
A wurin bikin tsohon Shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato kan yunkurin tallafa wa yara masu tasowa, domin idan ba ilimi babu kasa. Ya yi kira ga al’ummar kasar nan su zauna lafiya domin sai da zaman lafiya ne ake yin komai da zai iya kawo wa kasa ci gaba.
Shi ma Tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a jawabinsa a wurin taron ya bayyana ilimi a matsayin ginshiki kuma abin dogaro ga kowace al’umma, inda ya ce kan haka wannan gwamnati ta yi kokari. Ya ce baya ga samar da ilimi ya kamata a fito da wata hanya da za ta taimaki yaran ta samar musu da aikin yi ba su gama karatu ba wata makama da za su rike.
Janar Buhari ya kara da cewa “Na je Kano wurin bude Jami’ar Arewa maso Yamma kuma yau gani na zo Sakkwato don bude wannan jami’a mallakar wannan jihar, sai jiya (Litinin) bayan Azhar na san zan zo nan kuma cikin ikon Allah gani saboda muhimmancin ilimi.”
Da farko Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana makasudin gina jami’ar da cewa domin ta kara fito da al’ummar jihar daga cikin jahilci da samun ingantaccen iilmi. Ya ce makarantar ta samu nasarar hade kabilun Najeriya wuri daya suna murna saboda wannan ci gaba.
Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin sun hada da Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Ribas da tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a Jam’iyar APC Sanata Bola Tinubu da Sarkin Musulmi da Shugaban Gudanarwar Jami’ar Alhaji Umaru Shinkafi wanda Alhaji Bello Suleman ya wakilta da sauransu.
Sauran wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnonin jihohin Kano da Jigawa da Adamawa da Ribas da tsohon Gwamnan Borno Alhaji Ali Modu Shariff da dukkan tsofaffin gwamnonin Jihar Sakkwato in ban da Alhaji Attahiru Bafarawa.
Sauran sun hada da Shugaban sabuwar PDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif Bisi Akande da sarakunan Argungu da Yawuri da shugabannin majalisun jihohin Sakkwato da Zamfara da Mataimakin Gwamnan Sakkwato da sauransu.
Akwai rade-radin taron wanin yunkuri ne da Gwamnoni Bakwai ke yi domin barin Jam’iyyar PDP.