Manyan ‘yan bindigar da aka halaka a Arewa maso Yamma

Matsalar tsaro a jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya ta fara kamari ne tun kimanin shekara 14 da suka gabata, inda a cikin shekarar 2011 fadan makiyaya da manoma ya fara rikidewa yana komawa ayyukan ta’addanci

Manyan ‘yan bindigar da aka halaka a Arewa maso Yamma

Matsalar tsaro a jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya ta fara kamari ne tun kimanin shekara 14 da suka gabata, inda a cikin shekarar 2011 fadan makiyaya da manoma ya fara rikidewa yana komawa ayyukan ta’addanci da fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Lamarin ya fara kamari ne a wasu sassa na Jihar Zamfara kafin daga bisani ya watsu jihohin Katsina da Sakkwato da Kebbi da Kaduna da ma Jihar Neja.

Alkalumma sun nuna cewa, tun lokacin da lamarin tsaro ya kazanta a wannan yankin, mutane fiye da dubu 13 hare haren ’yan bindigar ya halaka. Yayin da bincike ya nuna cewa, ’yan bindigar sun raba kimanin mutum 800,000 da muhallansu.

Haka kuma matsalar tsaron ta kara tura miliyoyin mutanen yankin cikin kuncin tattalin arziki sakamakon kasa zuwa gonakinsu don yin noma da kuma sakamakon miliyoyin kudi da suka biyan ’yan bindiga don fanso ’yan’uwansu da aka kama da kuma biyan harajin da wasu ’yan bindigar ke dora wa wasu kauyuka.

Duk da kashe wasu manyan ‘yan bindiga da jami’an tsaro da ’yan sa kai suka yi, da kuma yadda matsalar cikin gida tsakanin ’yan bindigar ta yi ajalin da dama daga cikinsu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da addabar yankin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kastina da sauran wasu sassa na jihohin Kaduna da Kano da Neja.

Aminiya ta yi sharhi kan wasu daga cikin manyan ’yan bindigar da suka mutu sakamakon hare haren jami’an tsaro da na sa kai da ma fadan cikin gida a tsakanin su kansu ’yan bindigar a jihohin Arewa maso Yamma. Da dama daga cikin wadanda mutu, a da suna daga cikin ’yan ta’adda da suka addabi jama’a da satar dabbobi da ta mutane da kuma kashe-kashe na ba gaira ba dalili.

Sai dai har yanzu jama’a na ci gaba da muhawa kan cewa, shin ko kisan wadannan ’yan bindiga a yankin Arewaci maso Yammacin Nijeriya, ya kawo wani ci gaba a fannin samar da tsaro da ci gaban al’umma da kuma sake dawowa da dauwamammen zama lafiya.

Wasu da dama na ganin matsalar tsaro na ci gaba da wanzuwa duk da irin wannan kokari da gwamnatin tarayya da na jihohi ke yi, yayin da ake ganin ’yan bindiga na sheke ayarsu tare da ci gaba da ayyukkansu na ta’addanci ta hanyar kashe mutane da garkuwa da su da karbar kudin fansa da satar dabbobi.

Yadda matsalar ta fara

Bincike ya nuna cewa, matsalar ta yi kamari tare da daukar sabon salo a tun a shekarar 2011 da wani rikicin Fulani da manoma ya faru a Jihar Zamfara, inda aka yi fadan da ba a taba yi ba a yankin.

Daga nan ‘yan bindigar Fulani suka bulla a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina, inda daga bisani suka yi kaka-gida a jihohin Sakkwato da Neja da Kebbi.

Kashe manyan ’yan bindigar bai samar da wani gagarumin sauyi ba-Bashar Altine

Bashar Altine Guyawa mai sharhi ne kan matsalar tsaro a Sakkwato ya ce, saboda kashe shugaban ‘yan bindiga ba a samu raguwar kai hari ga mutane.

“Kashe shugaba bay a haifar da raguwar kai hari, domin wasu na jiran bayan ba shi, su hau karaga, a ci gaba da kai hari. Wannan al’amari da kake gani ba in da aka samu raguwarsa, fada da ‘yan bindiga ba da gaskiya ake yi ba, zai yiwu akwai wata manufa boyayyiya da sai a gaba za ta fita.

Duk wani dan bindiga, wanda na sani a yankinmu da babu shi a yanzu ba wata daba tasa da ba ta ci gaba da aikinta ba, tun daga dajin Sububu da aka kashe Halilu. Dabarsa ta ci gaba gudanar da lamarinta. Akwai su Choma da Haru Dole na nan duk Kachalloli ne suna nan zaune a kusa da dajin Sububu da yaransu ba.

Yalo ma da aka ce an kashe da ke dajin Gandu, a dajin akwai dabobi sun fi 100 shi kawai ya fi karfi da fice ne’’.

Ya kara da cewa, “hukumomi dai su tashi tsaye, a yi maganin matsalar, amma kudaden da ake kashewa da kayan aiki, ana bai wa jami’an tsaro aikin banza ne. Ai ya kamata in za a ba da kayan aiki, a je daji bakin daga, ba a bayar ba kuma a mayar ba, wanda ya san tsarin da za a bi don amfani da abin. Duk ba a yi tsarin hana ‘yan bindiga, su kawo hari ga mutanen gari ba, ba da gaske ake ba, amma a jira sai sun zalunci mutane, a bi su daga baya’’.

Hare-haren baya-bayan nan

A makonnin da suka gabata akalla sojoji uku aka kasha, sannan wasu da dama suka jikkata bayan da wani bam ya fashe a Jihar Sakkwato.

Bam din ya tashi ne da wata motar soja da ke dauke da dakarun sojoji zuwa garin Bargaja da ke karamar Hukumar Isa.

Rahotonni sun nuna cewa, dakarun sojojin suna kan hanyarsu ne ta kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai garin a ranar Asabar da ta gabata.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindiga sun fada kauyen tsakanin karfe 12:30 zuwa karfe 3:00 na dare, inda suka bude wuta ba kaukautawa, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin neman daukin sojoji a lokacin ne suka yi kwanton-bauna.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya yi zargin cewa, maharan sun dasa bam din ne a kan hanyar Isa zuwa Bargaja kafin isowar dakarun sojojin.

Mazaunin yankin ya ce, lamarin ya faru ne a wani bangare na hanyar da ta haɗa Isa da Bargaja, sannan ya nuna damuwa kan abin da ya siffanta da karuwar amfani da bama-bamai da ‘yan bindiga ke yi, wanda hakan abin fargaba ne ga mutanen yankin.

An yi wa sojojin sutura da yin sallah, an binne su a gaban iyalai da masoya da ‘yan uwansu a birnin Sakkwato. Mataimakin Gwamna Idris Muhammad Gobir ne ya wakilci gwamna a wurin sallar da aka yi wa mamatan a barikin Giginya da ke birnin jihar.

Awanni bayan kashe sojojin Bello Turji ya dauki alhakin kashe sojojin, a wani bidiyo a kafar Fesbuk. Bashar Altine Guyawa da yake magana kan harkokin tsaro a Sakkwato ya ce, dan bindigar ya nuna wasu makamai ne da ya mallaka, inda ya kamata a dauki matakin dakile kai hare-harensa ga jama’a.

Haka kuma ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Sakkwato a ranar Lahadi da ta gabata a karamar Hukumar Tureta.

Majiyar ta ce, maharan sun shigo da rana a lokacin sallar Azhar da yawan mutane suna masallaci, don yin sallah, a nan  jami’an ‘yan sanda da na Cibil Difens suka kare mutane, inda ‘yan bindigar suka gudu.

Sai dai sun yi nasarar kashe ‘yan sanda biyu a lokacin da suka bi sawunsu, suka yi masu kofar rago, wanda a nan take dan sanda daya ya rasu, dayan sai bayan an tafi da shi Sakkwato, don ya samu rauni da yawa a harbinsa da aka yi masa.

Wani babban jam’in ‘yan sanda da ke wurin ya tabbatar da faruwar lamarin tare da rasa ‘yan sanda biyu.

Guyawa Isa ya ce, “a nan yankin mashigar Dama a Sabon Birni jami’an tsaron da ke wurin shekara biyar da suka wuce, Bello Turji ya kewaye su duk ya kashe su gaba daya su 13, bayan motoci guda-guda da yake konewa a hanyar Gundumi da Unguwar Lalle. Haka ya nuna babu ingancin kayan aiki ga jami’an tsaro, wanda ya kamata a yi abin da ya dace.”

Tsohon Mistan Tsaro Muhammad Badaru a wani bayani nasa ya ce, sojoji sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga 9,300, an yi nasarar kama 7,000 a shekara daya.

Sojoji sun yi nasarar kashe jagororin ‘yan bindiga sama da 10 a yankin, inda sauran ke ci gaba da cin karensu ba babbaka. Wasu daga cikin manyan ‘yan bindigar da jami’an tsaron Nijeriya suka aika barzahu sun hada da:

Kacalla Halilu Sububu

Kacalla Halilu Sububu sojojin Nijeriya ne suka kashe shi a wani hari da suka kai, domin yakar ‘yan bidigar da ke addabar Arewa maso Yamma. dan bindigar a lokacin ya mamaye wani wurin hakar ma’adinai a dan-Kamfani da ke karamar Hukumar Anka, inda ya mallaki dubban shanu a dajin Sububu, yana cikin wanda sojoji ke nema ruwa a jallo, saboda ya yi ta aikata aikin ta’adaci sai ga shi sun yi nasarar kashe shi.

Bahari Alhaji Halidu

Bahari Alhaji Halidu wanda aka fi sani da Buharin Daji, hatsabibin dan bindiga ne da ya addabi mutanen  Kidandan ko Karewa a yankin karamar Hukumar Giwa da sabon Birnin Karawa a karamar Hukumar Igabi da wani bangare na Neja da Zamfara.

Kacalla dan Chaki da Dogon Gudali

Haka ma Kacalla dan Chaki da Dogon Gudali duk an yi nasarar kashe su, bayan addabar mutanen yankin da suka yi.

Dogo Rabe

Dogo Rabe sojojin sama ne suka kashe shi a wani hari da suka kai, domin tarwatsa ‘yan ta’adda a tsakanin kauyukkan Zurmi da Birnin Magaji a Jihar Zamfara.

Alhaji Auta da Kacalla Ruga

Alhaji Auta da Kacalla Ruga su ma an kashe su a wani hari da aka kai a yankin Birnin Magaji.

Rufa’i mai kaji

Haka shi ma Rufa’i Mai Kaji shugaba ne da yake da daruruwan ‘yan bindiga a karkashinsa, inda shi ma aka kashe shi a Zamfara.

Kacalla Yellow

Kacalla Yellow shi ne na baya-baya nan da aka ruwaito sojoji sun kashe a yankin Anka a Jihar Zamfara.

A Jihar Sakkwato

Jihar Sakkwato da take makotaka da Jihar Zamfara da Jihar Kebbi da kuma wani yanki na Jihar Neja tana fama da hare haren ’yan bindiga da ke kashe mutane tare da yin garkuwa da mutane da kuma sace musu dabbobi. Sai dai kamar sauran jihohin Arewa maso Yamma jami’an tsaron gwamnati da na ’yan sa kai da aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da cewa, sun kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kacalla Na-Allah

A Sakkwato sojoji sun kashe Kacalla Na-Allah a karamar Hukumar Isa, wanda dan bindigar ya fito a tsakanin  kauyukkan Girnashe da Kuka Tara a mazabar Tsabre. Haka kuma Kacalla Na-Allah dan uwa ne ga dan bindiga Ibrahim Chimmo da ke ta’asa a dajin Sububu. Wasu daga cikin manyan ’yan bindigar da aka kashe a Jihar Sakkwato sun hada da:

Kacalla Kallamu

Hakazalika, sojoji samu nasara kan wani shugaban ‘yan bindiga da ake kira Kacalla Kallamu a karamar Hukumar Sabon Birni.

A Jihar Katsina

Kamar yadda ’yan bindiga suka rika kai hare hare tare da kashe al’umma bayan tsare wasu don neman kudin fansa, haka su ma ake kashe su. Kisan da ake yi wa ‘yan ta’addan kamar yadda wakilinmu a Jihar Katsina ya yi wani bincike, mafi yawan a tsakanin ’yan bindigar yake faruwa, musamman sakamakon rashin jituwa da kuma takun-saka da yake wanzuwa a tsakanin manyan hatsibiban cikinsu.

Sola

A yankin Batsari, inda aka fara yin wannan sasanci da ke aiki a yanzu. Kafin sasanci, jami’an JTF sun kashe wani hatsabibin dan bingidar mai suna Sola. Kamar yadda Aminiya ta samu labarin yadda aka kashe shi, an ce bayan ya kawo hari a Batsarin abin da bai yi nasara ba, inda jami’an na JTF suka bi sawunsu, wanda an ce har da shi Sarkin Ruma (marigayi) ya bi sahun jama’a, domin kaiwa ga shi Sola. An taras da shi, an kuma kasha shi, sannan aka ciro kansa, aka shigo cikin gari domin jama’a su shaida.

Namurjiya kanen Dangwate

Namurjiya kanan Dangwate shi ma an kashe shi ne sakamakon fada da ya kaure a tsakanin ’yan bindiga.

Ashiru bannar iska

Ashiru bannar iska, wanda shi ma ya rasa ransa a hannun danginsa ‘yan ta’adda.

Ori

Ori wanda yake kani ne ga Turji, jami’an tsaro a  yankin Jibiya sun gama da shi, bayan ya kai masu hari a wani shingen bincike a Maganar Jibiya da ke daidai hanyar shiga Hirji ta kasar Nijer. Ori ya zo da nufin kwace bindigogin da ke hannun jami’an ‘yan sandar da ke wajen.

Bayan bude masu wuta a wani hari na ba-zata, ashe wani daga cikin ’yan sandan yana kwance karkashin motar yana barci. Jin harbin bindigar ya farkar da shi. Nan take ya gane kafar mai harin inda shi ma ya harbe shi a kafa, ya fadi, suka damke shi, kafin zuwa asibiti ya mutu.

Dangawo

Duk dai a wannan yanki na Jibiya, jami’an tsaron sun kashe dangawo, wanda yana cikin manyan ‘yan bindiga masu hadari.

Bala Wuta

Shi kuwa Bala Wuta wanda bayan yin sasancin da Lankai ya jagoranta, ya nuna babu ruwansa har ma ta kai saboda wata satar da yayo Lankai ya same sh har gida a Mazanya.

Bayan ya kwato dabbobin, ga kuma shan na jaki da shi Balan ya yi daga hannun Lankai din, kuma ya sanya masa harajin Naira milyan uku kuma sai da ya biya.

Sai dai wannan bai sa ya saduda ba, inda ya ci gaba da aikin ta’addancin da ya zamo sanadin barin sa duniya daga hannun wasu ‘yan bindigar.

Dangwate da Dan karami

Har ila yau, Dangwate ya rasa ransa ne ta hannun Dan karami. Kamar yadda Aminiya ta samu labari, sanadiyar satar tunkiya ce da kanin Dan karami ya ya yi daga wajen yayansa. Har Dangwate ya sayar da ita, mai ita ya gano, ya karbi abarsa da kuma kudin da suka sayar.

Ya kuma nemi karbe bindigogin da ke hannunsu, wanda hakan ya kara tayar da kura. To ashe batun bai wuce ba, Dan karami ya san da cewa, Dangwate zai biyo ba’asi, sai aka yi masa kwanton-bauna, inda Dan karamin ya harbe shi, ya mutu. Shi ma ba da jimawa wasu barayin dajin suka gama da shi.

Usman Modimodi

A yankin Safana kuwa, akwai Usman Modimodi, wanda shi ma ‘yan bindigar suka kashe shi. Modimodi shi ne wanda ya kori Dagaci daga gidansa na sarauta shi kuma ya mamaye gurbinsa. Kafin korar Dagacin, sai da ya yi masa cin zarafin da za a ce ba a taba samun wanda aka yi wa haka ba ko a cikin mutanen da ke hannun barayin.

Modimodi ne ya sa Dagacin ya fita daga gidansa tsirara babu komai a jikinsa. Shi ne a lokacin rayuwarsa ya addabi yankunan Zakka da wani sashe na Safana da Dutsinma har ya shigo yankin Kurfi.

An kashe wadannan shahararrun ‘yan bindigar dajin a lokacin da suke kan ganiyarsu ta ta’addanci a shekarar 2025.