Manyan ‘yan siyasar da suka canja sheka zuwa PDP siyasarsu ta zo karshe – Yahaya Kega
Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma Shugaban kungiyar Dillalan Mota ta Najeriya reshen Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya ce yawancin manyan ’yan siyasar da suka fice daga Jam’iyyar APC suka koma Jam’iyyar PDP siyasarsu ta zo karshe a Najeriya. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya […]

Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma Shugaban kungiyar Dillalan Mota ta Najeriya reshen Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya ce yawancin manyan ’yan siyasar da suka fice daga Jam’iyyar APC suka koma Jam’iyyar PDP siyasarsu ta zo karshe a Najeriya.
Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, fadar Jihar Filato.
Ya ce wadanda suka canja sheka daga APC suka koma PDP, dama haka rayuwar siyasarsu take. Kuma mutane ne da ba su da alkibla, wadanda damuwarsu ce take gabansu, ba damuwar ’yan Najeriya ba. Su dai bukatarsu kullum ya kasance ana yi da su.
Alhaji Yahaya Kega ya ce dama wadannan mutane a PDP suke, kafinsu canja sheka su dawo APC su ci zabe. Ya ce bayan da suka ci zaben sai suka ci amana. Da yanzu aka gano su, ba za su sake samun damar tsayawa zabe a APC ba, shi ne suka canja sheka zuwa PDP. Wato suka koma inda suka fito.
Ya ce babu shakka zuwan gwamnatin Shugaba Buhari ta bude wa ’yan Najeriya ido, saboda adalcin da gwamnatin ta zo da shi, su kuma irin wadancan mutane ba sa son wannan adalci da gwamnatin Buhari ta zo da shi.
Alhaji Yahaya Kega ya yi kira ga talakawan Najeriya su yi amfani da wannan dama da suka samu, su zabi mutanen kirki wadanda za su taimaka wa gwamnatin Buhari a zaben badi.
Da ya juya ga tsarin zaben tsayar da ’yan takara da Jam’iyyar APC ta fitar kuwa, ya ce a ra’ayinsa ayi zaben ’yar tike a dukan kujerun da za a yi takara, kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a yi a zaben tsayar da dan takarar Shugaban kasa.
“Domin wannan zabe shi ne zaben adalci, wato jama’a ’ya’yan Jam’iyyar APC su fito tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi su zabi ’yan takarar da suke so. Irin wannan zabe shi ne zai fitar da ainihin ’yan takara nagari,” inji shi.