Manyan ’yan ta’adda sun kashe juna a Katsina

Moɗi-moɗi ne ya kashe jarumin ɗan sandan nan na garin Dutsinma wanda ya hana su yin rawar gaban hantsi a kwanakin baya.

Manyan ’yan ta’adda sun kashe juna a Katsina

Da misalin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na ranar Laraba ne aka yi artabu a tsakanin gungun ’yan bindigar daji da suka addabi yankunan ƙananan hukumomin Safana da Danmusa da Batsari.

Usman Moɗi-moɗi da Jan Kare tare da wasu da dama daga cikinsu sun kwanta dama ta hannun wani ɗan bindigar mai suna Kabiru Mai Ɗan Hannu.

Kamar yadda labarin ya iske mu daga wata majiya mai ƙarfi wadda ke da kusanci da garin da abin ya faru, ta ce, su dai su Moɗi-moɗi sun je sun sato dabbobin su Kabirun ne yayin da suka biyo sawunsu kuma aka yi masu kwanton ɓauna.

A nan aka fafata har su Kabiru suka yi nasara a kan su Moɗi-moɗi.

In za a iya tunawa, Moɗi-moɗi ne ya kashe jarumin ɗan sandan nan na garin Dutsinma wanda ya hana su yin rawar gaban hantsi a kwanakin baya.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka