Manzon Allah: Abin koyi mai kyau ga muminai (1)

Daga Hudubar Imam Murtadha Gusau  Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete, Okene  Mukaddima: Bayan haka ya bayin Allah! A wannan ayar Alkur’ani: “Lallai, abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah.” An ambaci “abin koyi mai kyau” wato mutumin da ya kamata mutane su yi koyi da shi kuma su bi shi. […]

Manzon Allah: Abin koyi mai kyau ga muminai (1)

Daga Hudubar Imam Murtadha Gusau 

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete, Okene 

Mukaddima:

Bayan haka ya bayin Allah! A wannan ayar Alkur’ani: “Lallai, abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah.” An ambaci “abin koyi mai kyau” wato mutumin da ya kamata mutane su yi koyi da shi kuma su bi shi.

Wannan ayar Alkur’ani wata babbar jigo ce ga wajibcin bi da koyi da Manzon Allah (SAW), ta wajen furucinsa da aikisa. Kuma ayar ba ta iyakance matakan wannan koyi da biyayya ba, ba ta ayyana abin da yake wajibi ne mu yi koyi da shi ba da kuma abin da yake ganin dama ko abin so ba. Sai dai littattafan fikihu sun yi bayani dalla-dalla kan hakan.  

’Yan uwa maza da mata! Yin koyi tare da bin gwadaben Annabi (SAW) bai takaita ga tushen addini (akida) kadai ba, har ma ya shafi rassansa (furu’a). Misali haramun ne mutum ya yi tsarki da hannun dama bayan ya yi bayi kamar yadda wadansu malamai (Allah Ya yi musu rahama) suka ce, saboda Annabi (SAW) ya hana mu yin haka, kuma wannan yana cikin rassan addini.

Wanke al’aurarmu bayan mun yi bawali ko bayi, wajibi ne, kuma hakan yana cikin rassan addini. Cin abinci da hannun dama da makamantan haka, su ma suna cikin al’amuran da ake koyi da Annabi (SAW). Sai dai ya kamata mu sani akwai bambanci a tsakanin Sunnan (jam’in Sunnah) da ake nufi da ayyukan ibada da muke koyi da Annabi (SAW), ya alla na wajibci ne ko na mustahabbanci da kuma Sunnan da ake nufin wasu ayyuka da Annabi (SAW) yake aikatawa kamar taje gashin kansa (ta yadda zai) mayar da shi baya da kuma yin wanka a kwarya ko masaki ko wani mazubi da yadda yake tafiya da sauransu.

Ba a wajabta wa Musulmi cewa dole sai ya yi koyi da shi a irin wadannan abubuwa na baya ba, kuma duk da cewa bin misalinsa a cikin irin wadannan abubuwa yana nufin cikar kamala wajen koyi da shi, amma in mutum bai yi koyi da shi a cikinsu ba bai yi zunubi ba, sai dai ana sa ran wanda ya yi koyin da shi ya samu lada a kan haka.

Ina fata da wannan mun bayyana wasu muhimman abubuwa kan a wane abu ne koyi da Annabi (SAW) yake zama wajibi ko mustahabbi, ya alla a kinshikai ko rassa, kuma akwai bambanci a tsakanin Sunnah kan aikata ayyukan ibada da kuma Sunnah ta halayyar rayuwa.

A ka’ida dai wajibi ne a yi koyi tare da kwafar ayyukan Annabi (SAW). Imam  Bukhari ya rubuta wani babi a cikin littafinsa mai suna: “Babin Koyi da Ayyukan Annabi (SAW).”

Imam Al-Hafiz Ibn Hajar, (Allah Ya yi masa rahama) lokacin da yake sharhi a kan wannan babi a cikin littafinsa Fathul  Bari ya kafa hujja kan haka da ayoyi masu zuwa:

“Lallai, abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatar samun rahamar Allah da Ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa.” (k:33:21).

Wadansu ma’abuta ilimi suna cewa wajibi ne a yi koyi da Annabi (SAW) kamar yadda yake kunshe a wani umarni da Allah Ya bayar inda Ya ce: “Kuma abin da Manzo ya ba ku, to ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to ku bar shi. Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Mai tsananin ukuba ne.” (k:59:7).

Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Ka ce: “Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne Mai jin kai.” (k:3:31).

Kuma Madaukaki Ya sake cewa:  “…ku bi shi (Annabi Muhammad), tsammaninku, kuna shiryuwa.” (k:7:158).

Don haka akwai bukatar mu rika yin koyi da aikinsa da ayyukansa da maganganunsa, sai inda aka samu hujjar da ta ce wani aiki na Annabi (SAW), na ganin dama da zabi ne ko ta kebanta gare shi ne kawai.

Ya kamata ku sani yin koyi da shi (SAW) a maganganunsa da ayyukansa ba su takaita ga ayoyin da suka gabata kawai ba, domin asali yana yin ayyukansa ne domin a yi koyi da shi, sai inda aka samu kebance shi da aikin (khususiyya).

 Wannan kuma ya kunshi hatta gudanar da harkokin Musulmi a lokacin zaman lafiya ko yaki, kuma wannan ne abin da ake kira ‘siyasa.’

Sahabbai (Allah Ya yarda da su) sun fahimci wannan ka’ida ta yin koyi da Annabi (SAW) a cikin ayyuka da maganganunsa. Imam Bukhari  (Allah Ya yi masa rahama) ya fadi a babinsa da muka ambata, cewa Ibn Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Annabi (SAW) ya taba sanya zoben zinare, sai dukan mutane suka sanya zobban zinare. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ina sanya wani zoben zinare, sai ya jefar da shi ya ce: “Ba zan sake sanya shi ba.” Sai mutane suka watsar da zobban zinaren su ma.”

Game da ayyukan da suka kebanta da Annabi (SAW), ba za a tabbatar da haka ba, sai tare da wata hujja. Kuma abubuwan da suka kebanta da Annabi (SAW) sanannu ne, malamai sun rubuta littattafai da dama a kan haka. Ba mu samu wani malami da ya ce, gudanar da al’amuran mutane (siyasa) wani abu ne da ya kebanta da shi ba, ko ya ce daidai yake da auren mata fiye da hudu ba da sauransu.

Don haka yana da muhimmanci kowane Musulmi ya san ma’anar siyasa a addini.  A nan mun kawo wata muhawara da Imam Ibn kayyim ya kawo a littafinsa Bada’i Al Fawa’id, a tsakanin Ibn Akil Al-Hambali da wani malamin mazahabar Shafi’iyya. Ya fadi a cikin littafinsa cewa:  “Babu siyasa face wadda ta dace da shari’a.” Ibn Akil ya ce: “Siyasa ita ce duk wani aiki da mutane suke yi, wanda yake da kusanci da ayyuka na kwarai kuma yake nesa da munanan ayyuka da yaudara koda wannan aiki bai tabbata daga Annabi (SAW) ba, kuma ko ba a yi wahayi a kansa ba.”

Imam Ibn kayyim yana ganin abin da Ibn Akil ya ce shi ne daidai, inda ya ce: “Idan alamomin adalci suka bayyana kuma manufofinsa suka fito balo-balo ta kowace hanya, to wannan ita ce shari’a kuma addinin Allah.”

Babu tufka da warwara a cikin wannan da abin da muka ambata a baya game da koyi da Annabi (SAW), domin abin da ake nufi idan za a cimma wani abu mai amfani ba tare da saba wa nassin addini ba, to wannan abin ya dace da abin da aka aiko Annabi (SAW) kuma bai yi hannun riga da shi ba. 

Wadanda suke ci gaba da maimata irin wadancan abubuwa suna so ne su takaita addini a matsayin ayyukan ibada na tsakanin mutum da Mahaliccinsa, suna so su cire addini daga harkokin rayuwar ta yadda tsarin ballagazanci zai gudanar da rayuwar Musulmi. Sukan yi duk abin da za su iya, su kawo duk wani dalili domin su rudar da Musulmi a kan wannan al’amari.

Ya bayin Allah! Rayuwa da dabi’un Annabi Muhammad (SAW) suna da muhimmanci wajen karba da yada addinin da ya kawo. Kuma ba za a ga wani sabani game da kyawawan halayen da yake da su kafin ya zama Annabi da wadanda ya rika nunawa bayan ya zama Manzo ba (SAW). Wannan ya nuna cewa kyawawan dabi’unsa sun dace da kyawawan dabi’un da Alkur’ani ya ambata. Misali saboda ya yi fice wajen gaskiya da rikon amana da tausayi tun kafin ya zama Annabi, ya sa ake kiransa da Muhammadul Amin, (Muhammadu Amintacce).”

A lokacin da muke dada fahimtar abubuwa bisa shudewar kwanaki kan muhimmancin kasancewa ‘dan Adam’ ya kamata a san cewa da farko Annabi Muhammad (SAW) shi ma dan Adam ne sannan Annabi. Kuma idan ba mu son takaita Musulunci da Musuluncin Annabi ga wani takaitaccen zamani ko wayewa, akwai bukatar mu fahimci wani abu na koyarwarsa ga duniya cewa ya shallake wancan lokaci.  Kuma domin zamowa dan Adam nagari, akwai bukatar ka zama abin koyi mai kyau.

Ya bayin Allah! Sanya Annabi Muhammad (SAW) a matsayin abin koyi yana nuna dabi’unsa su kasance dabi’u ne da suka dace da dukan duniya. An auna halayensa ta fuskoki da dama sun shafi sassan rayuwa ba kawai wasu al’adun gargajiyar wasu kawai ba.

Duk mutumin da za a yi koyi da shi ya kasance yana halaye da kyawawan dabi’un da suka dace da tunani da fahimta da yanayin mabambantan jama’a, kuma ba za su canja ba, saboda yanayin lokaci ko wurin zama. Wannan ne ya sa tilas da farko ya zamo ‘dan Adam’ domin amfanin dukan talikai irinsa a matsayinsu na bayin Allah ba tare da lura da addini ko akidar da suke riko da shi ba. To idan aka lura da halayyar bunkasar dan Adam da horarwarsa, za a iya ganin kyawawan halayen Annabawa masu girma a koyaushe suna da fiffikon kyan halaye a kan sauran mutanen da suke tare da su.

 Idan za a iya tunawa kafin Annabi (SAW) ya fara samun wahayi, ya kasance zaune na tsawon lokacin a cikin mutanensa inda ya yi fice wajen kyawawan dabi’u da halaye. Yana da dabi’un da suka kunshi, “halaye masu girma da ya ginu a kai,” halayen da suke mutum sa ya zama jagora a cikin jama’a. Annabi Muhammad (SAW) yana da halayen girma da mutunci tun kafin annabta. Littattafan tarihi da dama suna cike da misalan kyawawan halayensa. Tun kafin a yi masa wahayi, ya kasance mutum mai gaskiya, mai amana, mai sakin fuska, mai tausayi, mai kyauta. Yana da kaifin basira da kuma tausaya wa mata da jin kan kananan yara tun kafin Allah Ya umarce shi da haka. Wadannan kyawawan dabi’u da duniya ke nema suna daga cikin dalilan da Alkur’ani ya bayyana shi da abin koyi mai kyau ga dukan talikai.

Imam Murtadha Gusau, shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da Masallacin marigayi Alhaji Abdurrahman Okene da ke Okene, Jihar Kogi. Kuma za a iya samunsa ta waya mai lamba: +2348038289761.