Manzon Allah: Abin koyi mai kyau ga muminai (2)

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete, Okene  Fassarar Salihu Makera ’Yan uwa maza da mata! Ba za a yi musu cewa hakan saboda kasancewarsa mai karbar wahayi ya dada daukaka matsayinsa zuwa ga mataki na kololuwa ba, ta yadda hakan ya jagorance shi zuwa ga isarwa da bayanin sakon Allah. Sai dai kuma idan muka […]

Manzon Allah: Abin koyi mai kyau ga muminai (2)

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete, Okene 

Fassarar Salihu Makera

’Yan uwa maza da mata! Ba za a yi musu cewa hakan saboda kasancewarsa mai karbar wahayi ya dada daukaka matsayinsa zuwa ga mataki na kololuwa ba, ta yadda hakan ya jagorance shi zuwa ga isarwa da bayanin sakon Allah. Sai dai kuma idan muka amince cewa wani wanda ba ya da halayen yabo kyawawa zai iya samunsu saboda sakon da ake saukar masa, to za mu daure kawunanmu ga jiran zuwan wahayi kafin mu zama masu kyawawan halaye. A zahiri saboda kasancewar ba a iya daidaita halayen daidakun mutane ta wajen karsashi da karfin halin da ikon zabin da ya dace da da ikon auna abubuwa da yanke hukunci a tsakanin mutumin da yake abin misali da mutumin da yake kwaikwaya, babu wan da yake da hujjar da wani zai zamo malalaci a bangaren yin kokarin gyara halayensa.  

Mun gani cewa a karnoni da dama wadansu Musulmi sun kasa iya bambance tsakanin daukar wani mutum suna takalidi da shi da kuma wanda ake yi masa biyayya mudalaki. Dalilin hakan kuwa shi ne, karancin iliminsu da zabinsu ga hanya mai sauki.

A wajen nuna wa Annabi (SAW) soyayya, akwai bukatar a sani kuma a fahimci rayuwarsa da shaksiyyarsa da kuma hakikanin sahihan abubuwan da ya koyar ko ya ce ba a dogara da labaran da suka ginu a kan karairayi da camfe-camfe da bidi’o’i da tawili ba. Domin nuna soyayya ta gaskiya tana bukatar amana. Hanya ta gaskiya da za a bi ga misali za ta bi ta soyayya ce da fahimta ba ta kuka ba.

Zan so in bayar da wasu misalai kan wasu kyawawan dabi’u na mutumtaka da ya bar mana; wadannan sun dace da hakikanin tarihi kuma Alkur’ani ya tabbatar da su, sun zamo abubuwan da Annabi (SAW) ya yi fice a kansu.

Babban abin da ya fifita Annabi Muhammad a kan kowa shi ne gaskiyarsa. Domin ta hanyar gaskiya ne mutum zai zama mai aikata ayyukan da’a har ya zama tsakakakke, sannan ya zama mumini, domin “mumini ba ya karya,” don haka babu makawa ya zama mai gaskiya. Ko mushirikan kuraishawa da suka ki karbar sakon annabtarsa ba su da ja a kan gaskiyar Annabi Muhammad (SAW). Wata rana a hanyar zuwa Badar, Ahnis bin Sharik ya ce da Abu Jahil: “Ya Abul Hakam, babu wanda zai ji mu a nan. Ka gaya min ra’ayinka a kan Muhammad. Shin shi mai gaskiya ne ko makaryaci?” Sai Abu Jahil ya amsa masa da cewa: “Na rantse hakika Muhammad mutum ne mai gaskiya,; bai taba yi mana karya ba.”

Nana Khadija (RA) ta ki amincewar da bukatar aurenta daga manyan sarakuna da shugabannin Larabawa, amma da kanta ta nemi Annabi Muhammad (SAW) ya aure ta, kuma ta amince ta aure shi ne saboda ta yi matukar gamsuwa da kyawawan halaye da dabi’unsa. Kalamanta a lokacin da wahayi na farko ya zo ga Annabi Muhammad (SAW) a fili sun tabbatar da cewa yana da gaskiya da amana da suka kamata a samu a wurin cikakken mutum. Ta ce: “Ya  Muhammad! Babu bukatar ka ji wani tsoro; kada ka damu! Allah ba zai kunyata bawanSa irinka ba. Na san kana fadin gaskiya, kana cika alkawari da tsare amana, kana kula da dangi kana taimakon fakirai, kana bude kofarka ga nakasassu kana taimakon mutanen da annoba ko bala’i  ya shafe su. Na rantse da Allah, ina fata za ka kasance Annabin wannan al’umma.”

Annabi Muhammad (SAW), mutum ne mai tsananin tawali’u da saukin kai fiye da yadda muke tunani. Duk da cewa shi “rahama ne ga dukan duniya,” bai dauki kansa yana ganin ya fi kowa ba. Tun ma kafin wadanda suka so shi su fara nuna masa soyayya ta hanyar furta cewa: “Mahafiyata da mahaifina fansa ne a gare ka ya Manzon Allah!,” bai taba watsi tawali’unsa ba. Ya sha jan kunnen masu wuce iyaka wajen yabonsa cewa: “Kada ku wuce iyaka wajen yabona kamar yadda Kiristoci suka yi, suka ce Isa ‘dan Allah.’ Ni bawan Allah ne kawai. Don haka ku rika kirana da bawan Allah kuma ManzonSa.” 

Kuma duk da cewa shi Annabi ne da aka aiko ga dukan duniya “aljanu da mutane,” bai dora wa wadansu mutane nauyin su rika gudanar da ayyukansa na kashin kansa ba. Kamar yadda A’isha (RA) ta ce, lokacin da aka tambaye ta: “Me (SAW) yake yi a gida?” Sai ta ce: “Yana yin duk abin da kowane mutum yake yi. Yakan dinke suturarsa, ya gyara takalmansa, ya tatsi nonon awaki ko tumakinsa, kuma ya kula da ayyukansa.”   

Kuma bai nuna bambanci a tsakanin mutane, kuma ya gaya wa masu yin haka cewa kuskure ne. Ya ce: “Ku sani Balarabe bai fi wanda ba Balarabe ba; haka wanda ba Balarabe ba, bai fi Balarabe ba; fari bai fi baki ba, haka baki bai fi fari ba. Mafifici a tsakaninsu shi ne wanda ya fi takawa.”

Kuma ya nuna cewa hadin kai yana kawo saukin al’amura, kuma yana da muhimmanci mutane su kasance masu yawan afuwa. Annabi (SAW) ya nuna haka ta hanyar rayuwarsa da kuma furucinsa, kuma ayoyi da dama a cikin Alkur’ani Mai girma sun bukaci haka. Manufarsa ya kyautata tare da bayar da jagorantar rayuwarsa da ta sauran jama’a a bisa hasken umarnin Allah da umarce-umarcenSa. 

Annabi Muhammad (SAW) a koyaushe yana hulda da bayi da mata da ribatattun yaki da yara da dabbobi cikin tausayawa a duk matakan rayuwarsa.

Sai kuma hakuri! Lallai ne hakuri wajibi ne domin yana yin ado ga mai shi kuma ya kawata kowane aiki mai kyau. Wannan kyakkyawan mutum (SAW), mutum ne mai cikakken hakuri – kan abin da ya zo daga Allah da abin da ya bijiro masa daga bayinSa. Sai dai a lokacin da idanunsa ya zubar da hawaye kan bakin cikin rasuwarsa dansa Ibrahim, ya yi haka ne saboda haka kowane mahaifi zai yi. Wannan ba ma kawai yana nuna mana zafin rabuwa da da ba ne a matsayin abin da ba za a iya dakile shu’urin da ke samun dan Adam ba irin wannan lokaci da maza ke yin kuka ba, har ma yana nuni kan yadda ake mika wuya ga kaddara tare da kauce wa wuce iyaka wadda ba ta dace da mai imani ba. Ya nuna kuskuren da wadansu ke yi saboda rasuwar makusanci da sauran kura-kuran da ke nuna tamkar tawaye ne ga hukuncin Allah ta hanyar daukar dogon lokaci ana koke-koke da iface-iface da sunan an yi rashi.

Wani Bature masani mai suna M. Watt ya ce: “Wadanda suka rayu tare da (Annabi) Muhammad, sun gaza gano inda ya gaza a fagen kyawawan halaye.” Kuma a bayansa ma an gaza gano gazawarsa kuma ba za a gano ba har abada. Domin Alkur’ani ne halaye da dabi’unsa (SAW) kuma Alkur’ani ya yi yabo a gare shi. Saboda haka kasancewar Annabi (SAW) mutum, ya sa yana da sauki mu fahimce shi, kuma fahimtar cewa ya fi kowa kyawawan halaye zai sa mu yi saurin nuna kauna da son sa.

Baya ga haka, wajen nuna soyayya ga Annabi Muhammad da yin koyi da shi, yana da kyau mu lura cewa a karkashin wadanne ka’idoji ne shi kuma zai so mu, sannan mu waiwayi kawunanmu don ganin yadda muke koyi da kyawawan halayensa a ayyukanmu. Akwai bukatar mu rika tunani kan yana tare da mu, to yaya mu muna tare da shi? A wani lokaci za mu ga shi uba ne mai tausayi, malami ne mai gaskiya, jagora ne zuwa ga shiriya, shugaban ne mai cikakken iko, kuma miji ne mai adalci da daidaitawa. To mu yaya muke? A wannan zamani da muke ciki nesa da lokaci da wurin da ya zauna, shin muna kokarin yin abin da ya dace domin zama kamar ’yarsa Fatima (RA) da maulansa Zaid (RA) da abokinsa Abubakar (RA) da sahibarsa Khadija (RA)? Ko kuwa idan shi ne a inda muke a wannan hali da muke ciki, yaya zai yi ya rayu kamar yadda koyarwar Alkur’ani da Sunnah suka tanada? Idan muka hada lokacinmu da nasa, wadanne mutane ne da suke tare da shi za su kasance kamarsa? 

Ta hanyar irin wannan tambayoyi ga kawunanmu da suka kamata su rika maimaituwa a zukatan Musulmi za mu iya daukar matakan da suka dace wajen mika wuya da sake jaddada fahimtarmu gare shi da kuma dacewa da Sunnarsa (SAW).  

Ina rokon Allah Ya taimake mu mu rayu a bisa koyarwar Alkur’ani da Sunnah. Allah Ya nuna mana gaskiya, kuma Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya Ya ba mu ikon guje mata. Ya Allah! Ka shirye mu kuma Ka tsare mu daga jahilci da ayyuka masu halakarwa. Ka kare mu daga munanan ayyukanmu. Ka sa karshen ayyukanmu su kasance mafiya kyau da dacewa. Kuma Ka gafarta mana baki daya.

Ya ku ’yan uwana masu girma! Duk abin da na fadi mai kyau a Hudubata ta yau daga Allah ne Madaukaki, kuma duk  wani kuskure daga gare ni. Kuma muna neman tsarin Allah daga bayar da muguwar shawara da dukan nau’o’in halaka da fitina. Ina rokon Allah Ya gafarta min idan na wuce iyaka a duk abin da na fada ko na aikata. 

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga ManzonSa Annabi Muhmmad (SAW) da alayensa da sahabbansa. Allah Madaukaki Ya gafarta mana dukan zunubanmu, lallai Shi Mai gafara ne Mai jin kai.

Imam Murtada Muhammad Gusau ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’a 12 ga Rabi’ul Awwal, shekara ta 1439 Bayan Hijira, 1 ga Disamba, 2017. Kuma za a iya samunsa ta waya mai lamba: +2348038289761.