Manzon Allah: Haske mai kore duhu (10)
DARASI NA SHA BIYAR HIJIRA ZUWA HABASHA Sannu a hankali Musulunci na kara samun ci gaba duk da munanan matakai da jagororin Makka suka dauka na dakile wannan tafiya. Mushrikan Makka sun kara matsa kaimi wajen musgunawa Musulmi, sun hada kan daukacin kabilun Makka ban da na Banu Hashim da na Banu Abdul Muddalib don […]
DARASI NA SHA BIYAR HIJIRA ZUWA HABASHA
Sannu a hankali Musulunci na kara samun ci gaba duk da munanan matakai da jagororin Makka suka dauka na dakile wannan tafiya. Mushrikan Makka sun kara matsa kaimi wajen musgunawa Musulmi, sun hada kan daukacin kabilun Makka ban da na Banu Hashim da na Banu Abdul Muddalib don katse hanzarin Annabi (SAW). Sun yi taro a bakin dakin Ka’aba ana (kiran wajen Darun Nadwah) don hada kai su kashe Annabi (SAW).
Wani babban al’amari ko mataki da suka dauka kuma shi ne na yanke hukuncin cewa dukkan kabilun Makka su janye kariyar kabilunsu ga dukkan wanda ya shiga Musulunci. A sanadiyar haka sai Musulmi suka zama ba su da wata kariya daga jama’arsu, babu wani wanda zai tsaya musu ko taimaka musu daga cikin kabilunsu idan har wani ya nemi cutar da su saboda addininsu. Wadannan abubuwa sun taru sun addabi Musulmi matuka.
Don haka ne a shekara ta biyar bayan fara kiran Annabi (SAW), Musulmi suka fara tunanin irin matakan da za su dauka don samun sauki na al’amuran rayuwarsu. Daya daga cikin matakan da wasunsu suka dauka shi ne su nemi kariya daga wasu wurare a maimakon abin da aka saba na kowace kabila ta ba da kariya ga al’ummarta. An ruwaito cewa Abubakar (RA) sai da ya nemi kariya daga Ibn al-Diginnah, wanda ba Bakuraishe ba ne. Hakika Abubakar ya fita da niyyar hijira zuwa Habasha har ya kama hanya ya kai Bark sai Malik dan Diginnah shi ma shugaba ne na kabilarsa sai ya hadu da shi yake tambayar sa ina zuwa da ya labarta masa an fitine shi da tsananta cutar da shi, shi ne zai tafi Habasha a nan ya ce masa haba irin ka baya barin garinsa kana sada zumunci, kana tufatar da wanda ba shi da shi da taimakon gaskiya, kana tabbatar da bako, kana daukar kowa naka don haka na dauki makwabtakarka a haka ya dawo da shi ya shelanta haka ga Kuraishawa kuma ba wanda ya musa masa, amma sun ce ya umurci Abubakar kada ya fito fili yin sallah ya bauta wa ubangijinsa a gida don muna tsoron ya fitini ’ya’yanmu da matanmu da masu rauninmu, a kan haka sai ya gina masallaci a harabar cikin gidansa sai dai shi mutum ne wanda idan yana karanta Alkur’ani ba ya boyewa kuma ba ya mallakar idonsa ma’ana sai ya yi ta kuka, ya kansance duk lokacin da yake sallah yana jawo hankalin mata da yara suna ta’ajjubi kan irin wannan kuka da karatu nasa har su taru suna kallon sa bai ma san suna yi ba. Da Malik ya tunatar da shi ya daina bayyana karatunsa sai ya ce: “Na mayar maka da makwabtakar na yarda da makwabtakar Allah.”
Ganin halin da Musulmi ke ciki, ga kuma ayoyin Alkur’ani da suke nuna kasar Allah mai fadi ce, sai Annabi (SAW) ya fara tunanin shawartar wasu daga cikin Musulmi da su yi hijira su bar Makka zuwa kasar Habasha. Kuma an zabi Habasha ne saboda a lokacin suna karkashin sarki mai adalci kuma sun riki addini saukakke daga sama wato addinin Nasara, ba bautar gumaka ko bautar wuta ko kuma maguzanci suke kai ba.
Bayan Annabi (SAW) da jama’arsa sun yanke hukuncin tura wasu Musulmi hijira zuwa Habasha, sai mutane kimanin goma sha shida suka fita zuwa hijira ta farko a cikin watan Rajab, a shekara ta biyar bayan fara kira daga Manzon Allah (SAW). Daga cikin wadanda suka fita zuwa Habasha a karo na farko akwai Usman ibn Affan da matarsa Rukayyah ’yar Annabi (SAW), akwai Zubayr binil Awwam da Mus’ab ibn Umayr da Abdur Rahman bin Awf. Sannan akwai Abu Salamah da matarsa Umm Salamah, akwai kuma Abdullahi dan Mas’ud da dai sauransu.
A lokacin da mutanen Makka suka ji labarin fitar wadannan masu gudun hijira sai suka bi su a guje don su kama su su dawo da su garin Makka, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba. Masu hijirar suka ci nasarar tserewa, kuma suka samu isa Habasha, a inda suka yi zango a kusa da fadar Sarki Najjashi. ’Yan aiken mutanen Makka sun bukaci Sarkin da ya ba su masu hijirar su koma da su Makka. Sai ya ce wa ’yan aiken, “Ku tafi wallahi ba zan sallama muku su ba”. Sai suka fita amma duk da haka suka sake dawowa washegari da wata makidar suka ce: Wai Musulmi suna fadar wata magana mai girma game da Isah (AS). Sai Najjashi ya kira su ya tambaye su game da haka sai Ja’afar (RA) ya ce: Abin da Annabi (SAW) ya zo da shi muke fadi cewa: “Shi bawan Allah ne kuma Manzonsa kuma ruhinsa wanda ya jefa a cikin Maryam wadda ba ta taba saduwa da kowa ba.”
Sai Najjashi ya ce ba ku ketare ba kuma ku zauna a kasata cikin aminci kuma ya yi umurni a mai da kyautar da ’yan aiken Kuraishawa suka kawo su koma da abin su.
Sun zauna a wannan kasa har tsawon watanni cikin aminci da kwanciyar hankali. Ana cikin haka ne sai jita-jita ta fara bazuwa cewar mutanen Makka yanzu sun sassauta irin tsangwamar da suke yi wa Musulmi, don haka yanzu an samu sararawa daga kunci da takurawar da ake yi wa Musulmi. Saboda wannan jita-jita sai ’yan hijirar suka yanke shawarar komawa gida Makka don zama cikin iyalansu da jama’arsu.
Amma dawowarsu ke da wuya sai suka tarar musgunawar har tafi ta baya muni. Babu wani abin da ya canza, sai ma kara ta’azzara ya yi. Saboda kazancewar da lamarin ya yi bayan dawowar masu hijira garin Makka, sai Musulmi suka sake yanke shawarar kara komawa Habasha don ci gaba da hijirarsu. Kuma kamar yadda a wata ruwayar kimanin mazaje 80 ne da mata 18 suka fita a wannan karo na biyu don hijira. An yi wannan tafiya ce a karkashin Ja’afar bin Abi Dalib.
Kasancewar a wannan karo babu wata kabila ko wani babban gida a Makka wadda ba a samu wakiltar ’yan gudun hijira ba, ya tayar da hankalin mutanen Makka kwarai da gaske. Saboda haka suka shirya taro don shawarar irin matakin da ya kamata su dauka, kuma sakamakon haka suka yanke hukuncin tura wata tawaga ta bin sawu zuwa Sarkin Habasha. Wannan tawaga ta kunshi Abdullahi ibn Abi Rabi’ah da Amr binil As, kuma sun je ne da niyyar dawo da ’yan gudun hijira zuwa garin Makka.
Da suka shiga sun kebe da wasu na kusa da sarki suka ba su kyauta sannan suka shigar da manufarsu, su kuma suka yi mawafaka da su har suka taimaka musu a kan hujjar da za su ba da su cimma nufinsu, daga nan aka gabatar da su wurin sarki kuma suka mika kyautar da suka kawo masa sannan suka ce: “Ya kai wannan sarki hakika wasu ’ya’yan wawaye sun zo garinka kuma sun rabu da addininsu kuma ba su shiga addininka ba, sun zo da wani addini wanda suka kirkira wanda ba mu san shi ba balle kai, hakika madaukakan mutanensu kakanninsu da ’yan’uwan iyayensu da danginsu suka aiko mu gareka don ka maido musu da su. Su suka fi su hangen nesa da sanin abin da suke zargin su da shi.”
Sai makusantan sarkin suka karfafi maganarsu amma adili Najjashi wanda aka shaidi ba ya yarda azalunci kowa a garinsa ya nemi jin su ma ta bakin Musulmin har gaskiya ta bayyana sai ya ce: “Wane abu ne wannan wanda ya raba ku da addininku kuma ba ku shiga addini na ba ko addinin da yake kan wannan hanyar ba?”
Wadannan wakilai sun isa gaban Sarki Najjashi tare da mika bukatunsu gare shi. Nan take kuma Sarki Najjashi ya tura aka nemo wakilan ’yan gudun hijirar don a ji bahasinsu. Kuma bayan wakilan mutanen Makka sun yi jawabinsu sai Sarki ya bukaci Musulmi da su mai da martani, wato su ba da hanzarinsu don kare kansu. A nan ne jagoransu Ja’afar ibn Abi Talib ya yi jawabi mai sosa rai wanda ya taba zuciyar Najjashi, wanda a wani kaulin aka ce sai da ya zub da hawaye. Kadan daga cikin abin da Ja’afar ya fada a gaban Sarki Najjashi shi ne, “Mun kasance mu al’umma ce da ke rayuwa cikin jahiliyya, masu bautar gumaka, masu cin mushe, muna aukawa zuwa munanan ayyuka na alfasha, muna yanke zumunta tsakaninmu, muna cutar da makwabtanmu, masu karfi daga cikinmu suna danne masu rauni. Mun kasance cikin wannan kangi har Allah Ya aiko da Manzonsa zuwa gare mu, wanda mun san nasabarsa, mun san gaskiyarsa, da amanarsa da kamewarsa. Wannan Manzo ya kira mu zuwa ga Allah, don mu kadaita Shi wajen bauta, mu tsarkake Shi tare da kaurace wa abin da mu da iyayenmu ke bauta wa na daga duwatsu da gumaka. Ya umurce mu da gaskiya wajen magana, da rikon amana, sada zumunci, kyautata wa makwabta, kamewa daga ketare haddi da zubar da jini a tsakaninmu. Ya hana mu aukawa cikin ayyukan alfasha, da fadin abin da ba mu da tabbas a kai, da cin dukiyar maraya, da yin kazafi ga salihan mata…”.
Bayan kammala bayaninsa sai Sarki Najjashi ya neme shi da ya karanta wani abu daga cikin littafinsu, inda aka ruwaito ya karanta masa wasu ayoyi daga suratu Maryam. Kuma bayani ya tabbata cewa Sarki Najjashi ya karbi addinin Musulunci, kodayake ya yi addininsa ne a boye. Kuma bayan ya mutu mala’ika Jibril ya kawo labarin rasuwarsa ga Manzon Allah (SAW), wanda kuma ya umurci sahabbai da fita don yi masa sallar jana’iza a garin Madina. Wannan shi ne dalilin tabbatar da hukuncin Salatul Ga’ib wato yin sallar jana’iza ga wanda yake nesa.
Abin da ya faru a fadar Sarki shi ya sanya aka bar masu hijira su yi zamansu a Habasha cikin aminci da walwala. Kuma zamansu a wannan kasa ya taimakawa yaduwar addinin Musulunci a wajen Makka da duniya baki daya.
Karin bayani:
1 Siratu Ibn Hisham (1/372)
2 Dalilin da ya sa masu hijira zuwa Habasha suka dawo Makka, abin da ya tabbata daga cikin littattafan tarihi da sira shi ne, watsuwar jita-jita cewa mutanen Makka sun musulunta.
Za mu ci gaba insha Allah.