Manzon Allah: Haske mai kore duhu (11)
Darasi na Goma Sha Shida Abin da ya biyo bayan Shekarar Hijirar Habasha A lokacin da Musulmi masu hijira a Habasha suka samu sararawa kuma wakilan mutanen Makka suka koma gida ba tare da samun nasarar shawo kan Sarkin Habasha ba, yanayin da Annabi (SAW) da jama’arsa suke ciki a garin Makka kuma sai kara […]
Darasi na Goma Sha Shida
Abin da ya biyo bayan Shekarar Hijirar Habasha
A lokacin da Musulmi masu hijira a Habasha suka samu sararawa kuma wakilan mutanen Makka suka koma gida ba tare da samun nasarar shawo kan Sarkin Habasha ba, yanayin da Annabi (SAW) da jama’arsa suke ciki a garin Makka kuma sai kara munana yake yi. Makiya Annabi (SAW) sun sake damara don su katse hanzarinsa. Don haka suka fito da hanyoyi daban-daban da suka hada da kara musguna wa Musulmi da hada baki don kaurace musu da yin batanci ga Annabi (SAW) da shirya kashe shi da hana baki da suka shigo gari saurarensa da janye kariyar kabila ga mutanensa da sauransu.
Daga cikin cutarwar fatar baki da suka yi ga Manzon Allah (SAW) akwai kiransa da mahaukaci ko boka ko mai sihiri ko makaryaci ko mai raba kan jama’a da sauransu. Amma Allah (SWT) Ya wanke shi daga wadannan zarge-zarge, kuma Ya sanya jifar da suke yi masa da wadannan miyagun kalmomi ba su yi tasiri a tsakanin mutane ba.
Darasi na Goma Sha Bakwai
Kokarin Kuraishawa na kashe Annabi (SAW):
Kuraishawa sun ji bakin cikin ganin addinin yana kara samun daukaka Musulunci na ci gaba da yaduwa, kuma ga Abu Dalib ya tsaya tsayin daka wajen taimakonsa da kare shi daga farmakinsu, domin shi sadauki ne na gaske. A karshe suka fara tunanin kamar kokarinsu yana tafiya ba tare da samun wata nasara ba, sai suka yanke shawarar su kashe shi. A kokarin haka Utbah dan Abu Lahab ya nufi Annabi (SAW) bai yi nasara ba, Annabi (SAW) ya yi wata addu’a a kansa ya ce “Ya Allah Ka aiko masa daya daga karnukanKa. Da Utbah ya yi tafiya zuwa Sham cikin fatake suka sauka a wani wuri sai ga zaki yana kewaya su a nan ya gane wannan zakin ne makashinsa har ya furta haka. Da za su kwanta barci sai aka sanya Utbah a tsakiyar mutane, amma da suka yi barci haka zakin ya fizge shi ta kansa ya kashe shi.
Abu Jahil da ya ga kashe Annabi (SAW) ya ci tura kuma ya ki daina aibata abubuwan bautarsu, sai ya ce shi zai je da dutse mai nauyin da zai iya dauka ya kwada masa a kai, idan ya yi sujuda, duk abin da zai faru ya faru, in ya so ku sallama ni ga Banu Abdu-Manaf. Kuraishawa suka ce, “Wallahi ba za mu sallama ka ba, ka je ka zartar da nufinka.” Da asuba ta yi ya dauki katon dutse wanda karfinsa zai iya dauka ya nufi inda Annabi (SAW) yake yana Sallah, su kuma suka labe suna kallo, kawai sai suka ga ya dawo a firgice har launinsa ya canja kamar wanda aka ci da yaki. Sai suka tambaye shi, “Yaya haka ya Abul Hakam?” Ya ce: “Na je in aikata abin da na fada jiya sai aka bijiro mini da wani irin mugun rakumi da ban taba ganin irinsa ba, ya siffanta musu shi, ya nufo ni zai cinye ni.” Haka dai ya kasa aiwatar da mugun nufinsa. An ruwaito daga Annabi (SAW) cewa, “Wannan rakumin Jibrilu (AS) ne kuma da ya kusanto lallai da kama shi zai yi.”
Haka dai harkokin kokarin kashe shi suka yi ta aukuwa ba nasara, koyaushe ya zo ibada a Ka’aba sai su yi ta muzanta shi suna dariya. Wata rana a wajen da suke taruwa a kusa da Ka’aba su Ukbah bn Abu Mu’aiz ya tashi ya fuskanci Annabi (SAW) ya kama mayafinsa ya zargo shi daga wuyansa ya shake shi, shaka mai tsanani. Sarihu ya ruga ya gaya wa Abubakar (RA) ya ce “Ka riski abokinka.” Ya yi maza yana zuwa ya kamo kafadar Ukbah ya tunkude shi ya daki wannan ya bugi wancan yana cewa ashe za ku kashe mutum don ya ce Ubangijina Shi ne Allah?” Sai suka juya dukan a kan Abubakar (RA) har sai da ya fita hayyacinsa, fuskarsa ta kumbura har ba a bambance hancinsa da bakinsa. Suka ja shi da mayafi suka tura shi gidansa, ba sa kokwanto ko mutuwa zai yi, sai dai bai mutu ba sai wurin yamma ya yi magana yana tambayar halin da Annabi (SAW) yake ciki. Da aka ba shi abinci da ruwa ya ki karba har sai da dare ya nutsa sannan aka lallaba aka kai shi ya ga Annabi (SAW) da sauki a Darul Arkam a can karshen dutsen Safa inda Musulmi ke yin taronsu na ganawa da sanin addininsu da karatun Alkur’ani, wuri ne mai nisa daga idon jama’a.
Allahu Akbar! Ana cikin wannan hali na kunci Musulunci ya samu daukaka, mutum biyu daga manyan Kuraishawa suka musulunta, su ne ammin Annabi (SAW) Hamza dan Abdulmudallib jarumi da Umar dan Khaddabi sadauki marar tsoro. Umar shi ne dayan mutum biyu da Annabi (SAW) ya yi addu’a ya roki Allah Ya karfafi Musulunci da shi. Annabi (SAW) ya roki Allah Ya daukaka Musulunci da wanda ya fi so cikin wadannan mutanen kamar yadda Hadisi ya tabbatar wato: Umar dan Khattab ko Abu Jahil dan Hisham, sai Allah Ya zabi Umar (RA) wanda Musulmi suka dandani rashin tausayi da wulakanci daga gare shi kafin ya musulunta.
Dalilin musuluntar Hamza wata rana ya dawo daga farautarsa yana dauke da bakarsa ya tarar da Abu Jahil ya samu Manzo (SAW) kusa da Safa ya buge shi a kansa da dutse har jini na zuba. Sai baiwar Abdullahi dan Jad’an wadda ta ga duk abin da ya faru ta labarta masa, ya harzuka kawai sai ya je kusa da Ka’aba inda Abu Jahil ke zama da tawagarsu ya tsaya ya ce, “Shi ne ka bugi dan dan uwana ba ka san ni ma ina kan addininsa ba ne?” Sannan ya buge shi da bakarsa. Haka harshensa ya furta kamar dai harshen ya riga zuciyarsa ce, a nan take sai Allah Ya yalwata kirjinsa, imani ya shige shi, ya musulunta. Allahu Akbar!
Wasu ruwayoyi da aka ambaci dalilin musuluntar Umar ba su inganta ba, daga cikin ire-iren wadannan ruwayoyi akwai wadda take cewa, Umar ya yi niyyar ya kashe Annabi (SAW) a kan kokarin Kuraishawa na gamawa da shi, sun yanke shawara a tafi kawai a kashe shi, “Wa zai je?” Umar ya ce, “Ni!” Sai suka ce, “Lallai wannan aiki naka ne, kai za ka iya.” Umar ya fito da takobi da rana tsaka ana tsananin zafi ya nufi inda Manzo (SAW) yake tare da wadanda suka rage ba su yi hijira zuwa Habasha ba, wato su Abubakar da Aliyu da Hamza wanda kwanansa uku da musulunta a lokacin. Sai Nu’aim dan Abdullahi Annahhamu ya hadu da shi ya ce ina zuwa? Ya ce wurin wannan karkataccen, shi ne Nu’aim ya gargade shi cewa banu Abdu-Manaf ba za su kyale ka ba idan ka kashe shi, a karshe ma ya ce masa ka fara gamawa da na gidanka! Umar ya ce su wane ne sai ya sanar da shi kanwarsa Fatima da mijinta da dan Amminsa duk sun musulunta. Sai ya juya ya tafi gidan a fusace!
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]