Manzon Allah: Haske mai kore duhu (14)
Su fa kafirai sun yarda akwai Allah kuma sun tabbatar masa da tauhidin halitta, wato sun amince shi Yake halitta da ruwan sama da fitar da tsirrai da matarwa da rayarwa. Tauhidin Uluhiyya ne ba su yarda da shi ba wato kadaita Allah a wajen bauta kamar su dogara da Allah da mayar da al’amarinsu […]
Su fa kafirai sun yarda akwai Allah kuma sun tabbatar masa da tauhidin halitta, wato sun amince shi Yake halitta da ruwan sama da fitar da tsirrai da matarwa da rayarwa. Tauhidin Uluhiyya ne ba su yarda da shi ba wato kadaita Allah a wajen bauta kamar su dogara da Allah da mayar da al’amarinsu a gare Shi da neman agaji yayin musiba ko roko na biyan bukatu. Suna ganin sanya wani a tsakanin Allah da su shi zai sa su samu biyan bukatunsu. Kamar sanya wani salihi, wanda ta haka ne suka suranta wadansu bayin Allah suka mayar da su abin bauta, ta haka har sun mallaki gumaka masu yawan gaske, a cikin Ka’aba kawai akwai gumaka 360, suna da su a gidajensu, wasu har a aljihu ake yawo da su don ba su kariya. Haka manyan halittun Allah sun mayar da su abin bautar kamar su rana da wata da taurari da duwatsu da shanu da sauransu Ciwon Abu Dalib ya tsananta har lokacin wafatinsa ya halarto, sai Manzon Allah (SAW) ya shiga wurinsa ya tarar da su Abu Jahil da Abdullahi dan Abu Umayya, sai ya ce masa ya Baffa! Ka ce ‘La’ilaha illallahu’ kalmar da zan tsaya maka da ita a matsayin hujja a wurin Allah. Sai su kuma suka ce masa ashe ba ka kwadayin turbar Abdulmudallib? Ba su gushe ba sunata kwadaitar da shi har a karshe ya ce: ‘A kan turbar Abdulmudallib.’
Sai Annabi (SAW) ya ce lallai zan roka maka gafara, sai Allah Ya saukar da wadannan ayoyi:
“Ba ya kasancewa ga Annabi da wadanda suka yi imani su nema wa mushirikai gafara koda sun kasance ma’abota kusanci bayan ya bayyana a gare su lallai su ma’abota (wutar) jahim ne.” Da fadar Allah (SWT): “Lallai kai ba ka (iya) shiryar da wanda kake so, sai dai Allah Shi Yake shiryar da wanda Ya so.”
Abu Dalib har ya rasu bai yi imani ba duk da gwagwarmayar da ya sha a kan ci gaban Musulunci amma saboda irin kariya da taimako da son da yake yi wa Manzon Allah (SAW) ya sa a Lahira shi ne mafi karancin wanda za a yi wa azaba kamar yadda ya tabbata a ingantaccen Hadisi da Abbas ya tambayi Annabi (SAW) cewa dame za ka wadartar da Baffanka? Don yana kaffa-kaffa da kai kuma yana fushi a kanka? Sai ya ce yana gwargwadon dan ruwan da ya kawo idon sawun kafa a wuta, (saboda karanci) ba don ni ba, da yana cikin can kasar wuta.
Lallai Abu Dalib ya ba da gagarumin taimako wajen yaduwar Musulunci domin sadaukantakar da ya nuna da jajircewa da fuskantar wahalhalu saboda ya kare dan dan uwansa wanda ya fi kauna a kan ’ya’yansa. Rasuwarsa ta kasance ne a watan Ramadan shekara ta goma 10 da aiko Manzon Allah (SAW).
Bai murmure daga wannan rashin ba kuma sai ga rasuwar matarsa Khadija a cikin wannan shekarar bayan wata biyu da rasuwar Abu Dalib, a wata ruwayar kuma aka ce bayan kwana uku. Khadijah (RA) babbar mataimakiya ce ga Annabi (SAW) wurin isar da wannan sako, ta taimake shi da kanta da dukiyarta. Manzon Allah (SAW) yana cewa game da ita: “Ta yi imani da ni a lokacin da mutane suka kafirce mini, ta gaskata ni lokacin da mutane suka karyata ni, ta yi musharaka da ni a cikin dukiyarta lokacin da mutane suka haramta mini. Allah Ya azurta ni da ’ya’yanta a lokacin da ya hana ni na watarta.”
Sayyidatu Khadija (RA) mace ce abar koyi ga dukan matan Musulmi na kwarai, daga falalarta wata rana ta dauko wani abinci ko abin sha za ta kai wa Annabi (SAW) Allah Ya yi masa wahayi cewa ya karanta mata gaisuwa (sallama) daga Ubangijinta da busharar wani gida a Aljanna.
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yawan tunata da ambatonta wanda har wannan ya sa wata rana A’isha (RA) ta nuna kishinta a kan haka.
Tabbas rasuwar Abu Dalib da Khadija (RA) ya sa Annabi (SAW) ya yi bakin ciki mai tsanani da shiga damuwa sosai. Rasuwar wadannan mutum biyu wadanda suke kamar katanga ce ga Annabi (SAW) ya sa kofa ta bude aka koma ruwa wurin cutar da shi saboda rashinsu. Har ya kasance mushirikai suna zuba masa kasa da bola a bayansa idan yana Sallah. A wannan hali ne Manzo (SAW) ya rika rokon Allah yana cewa “Ya Ubangiji! Ka gafarta wa mutanena domin ba su sani ba ne.”
Darasi na Ashirin
Tafiyar Manzon Allah (SAW) zuwa Da’ifa Tsangwamar da ake yi wa Annnabi (SAW) ta tsananta har wata rana aka zuba masa kasa a kansa, sai daya daga cikin ’ya’yansa tana kuka tana wanke masa yake cewa: “Kuraishawa ba su sa ni jin na tsani wani abu har sai da Abu Dalib ya rasu.”
Bayan rasuwar Khadija da wata daya cikin Shawwal, sai Manzon Allah (SAW) ya auri Sauda ’yar Zam’ah, ta kasance a karkashin Assakran dan Amru, sun yi imani tun farkon Musulunci, kuma suna cikin wadanda suka yi hijira zuwa Habasha, bayan rasuwar mijinta sai ta ji tsoron komawa ga dangita, kada su azabtar da ita su mayar da ita kafircinsu. Da aka shaida wa Annabi (SAW), a kan haka sai ya nemi aurenta don ya ba ta kariya kuma ya karrama ta, kuma haka zai rage masa kadaici. Sauda (RA) mace ce mai yawan shekaru tana da shekara 55, aurenta ya ba mutane da yawa mamaki, ashe akwai hikima a kan haka kuma ya zama abin koyi ga mutane. Bayan shekara daya kuma ya auri A’isha (RA) a Shawwal sai dai bai tare da ita ba sai a Madina, tana da shekara tara. A’isha Uwar Muminai ita ce mafi soyuwar matan Manzo (SAW), a kan wannan ne ma ya sa Sauda (RA) ta sarayar da kwananta ga A’isha (RA) saboda ta manyanta, bayan Annabi (SAW) ya kara auro wadansu matan a Madina.
A’isha (RA) ta kwashi ilimi sosai a wurin Annabi (SAW) kasancewa tana da kuruciya ta auri Manzon rahama (SAW), ta ruwaito hadisai 2,210 daga Annabi (SAW), har ya kasance sahabbai suna amsar fatawa a wurinta bayan rasuwar Annabi (SAW).
Al’amarin Kuraishawa kuma sai ya koma tsantsar wulakanci, wannan mawuyacin hali ya sa Annabi (SAW) ya bar garin Makka ya nufi Da’ifa ko za su amshi kiransa. A haka ya fita a kasa tare da bawansa Zaid dan Harisa wanda Khadija ce ta ba shi kyautarsa, shi kuma ya ’yanta shi ya rike shi kamar dansa. Duk wanda ya hadu da shi a hanya sai ya kira shi zuwa ga Musulunci. Da ya isa ya sauka a gidan wadansu ’yan uwansa uku amma da ya kira su sai suka fada masa mummunar magana, daga nan ya rika bi gida-gida na shugabannin kabilar garin yana kiransu, sai dai babu ko mutum daya da ya amshi tayin nasa. Da ya yi kwana goma a garin sai suka ce ya fita daga garin suka hada shi da wawayensu da yara da bayi suka bi shi da zagi da muzantawa suna jifarsa da duwatsu, suka rotsa masa kai har takalminsa ya jike da jini saboda raunuka duk da Zaidu (RA) yana ta kare shi yana kuma ture su.
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]