Manzon Allah: Haske mai kore duhu (15)

Bayan Annabi (SAW) ya farfado tare da dawowa da karfin jikinsa, sai ya daga hannu ya yi wata addu’a mai sosa rai. A cikin addu’ar tasa, kamar yadda Ibn Hisham da Dabarani da wadansu malaman tarihi suka ruwaito, yana cewa “Ya Ubangijina! Ina mika kukana a gare Ka game da gazawar karfina da yawan raunina […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (15)
Manzon Allah: Haske mai kore duhu (15)

Bayan Annabi (SAW) ya farfado tare da dawowa da karfin jikinsa, sai ya daga hannu ya yi wata addu’a mai sosa rai. A cikin addu’ar tasa, kamar yadda Ibn Hisham da Dabarani da wadansu malaman tarihi suka ruwaito, yana cewa “Ya Ubangijina! Ina mika kukana a gare Ka game da gazawar karfina da yawan raunina dangane da al’amuran mutanena. Ya Mafi rahamar masu rahama, Kai ne Ubangijin masu rauni kuma Kai ne Ubangijina. Ga wane ne Ka mika al’amarina? Ga wadanda suke nesa da ni amma suka tsananta wajen musguna mini, ko kuwa ga makiyana (makusanta) wadanda Ka jibantar da al’amarina a hannunsu? Idan ba Ka yi fushi da ni ba, to ba abin da zai dame ni. Amma zan yi farin ciki idan Ka yarda da ni. Ina neman tsari da fuskarKa da take haskaka kowane duhu, wadda kuma daga gare ta dukkan al’amuran duniya da Lahira suke daidaita. Kuma daga fushinKa, kada ya auka mini ko kin yardarKa kada ta riske ni. Na mika wuyana zuwa ga bukatarKa har sai Ka yarda da ni. Babu tsimi babu dabara sai a gare Ka.”

Mutanen Da’ifa sun ci gaba da bin Annabi (SAW) da abokin rakiyarsa har kimanin mil uku a wajen garin Da’ifa, har sai da Manzon Allah (SAW) ya kasa tafiya saboda jigatar da ya yi. A nan ne Zaid bn Harisa ya tallafe shi a kafadarsa zuwa wani lambu da ke kusa don samun mafaka. Wannan lambu kuma na mutanen Makka ne, mallakar Utbah da Shaybah ’ya’yan Rabi’ah. Masu lambun wadanda a lokacin suke cikin lambun, sun tausaya wa halin da Manzon Allah (SAW) yake ciki, duk kuwa da cewa suna daga cikin masu adawa da shi a garinsu na Makka. Don ganin halin da Annabi (SAW) yake ciki har suka aiko masa da lemo don ya tsotsa.

A haka da kyar suka isa ganuwar Utba da Shayba dan Rabi’ah mil uku daga Da’ifa ya shiga ciki sannan suka juya, sai Annabi (SAW) da Zaid suka shiga suka zauna karkashin itaciyar Inabi ya jingina da bangon wurin a nan ya yi addu’ar da ke sama.

’Ya’yan Rabi’ah sun gan su a wannan halin suka tausaya musu kuma suka kawo musu inabi tare da wani bawansu da suka ji Annabi (SAW) ya yi Bismillah sai bawan wanda Banasare ne wanda yake daga zuriyar Annabi Yunus sunansa Addas, ya ce ka fadi maganar da mutanen garin su Yunus Ibn Matta suke fadi.

Sai ya nemi labarin Annabi Yunus (AS) a wajen Annabi (SAW), kuma ya ba shi kissar, nan take ya musulunta.

Bayan Manzon Allah (SAW) ya dan huta, sai ya kama hanyarsa ta komawa garin Makka. Yana cikin tafiya ne, daidai wani wuri da ake kira Karnul Sa’alib (ko Karnul-Manazil), sai Annabi (SAW) ya lura da wani girgije yana yi masa rumfa a samansa. Yana daga kai sai ya ga Mala’ika Jibrilu (AS) a cikin wannan girgije. Sai Mala’ika Jibrilu (AS) ya ce masa Allah (SWT) Ya ga abin da wadannan mutane suka yi maka, kuma Ya aiko ni da Mala’ikan Duwatsu kan cewa ka fadi abin da kake so a yi da wadannan mutane. A nan sai Mala’ikan da ke kula da duwatsu ya bijiro, ya yi sallama ta gaisuwa ga Annabi (SAW), sannan ya ce masa ‘Allah Ya aiko ni don in aiwatar da duk umarnin da ka ba ni game da wadannan mutane, idan ka ce in binne su a karkashin duwatsun Abu Kubays da Kuwaiku’an (da ke garin Makka), yanzun nan sai in aiwatar.’ Amma sai Annabi (SAW) ya ki yarda a halaka su, yana cewa yana fata wata rana wadansu za su fito daga cikin tsatson wadannan mutane, wadanda za su kadaita Allah wajen bauta. (Imam Bukhari da Imam Muslim sun ruwaito wannan magana). Kuma an ruwaito cewa jin wannan magana daga bakin Manzon Allah (SAW), sai Mala’ika Jibril ya ce lallai Allah Ya yi gaskiya da Ya ambace ka mai tausayi mai gaskiya. Lallai Manzon Allah (SAW) mai tausayin al’ummarsa ne, domin kuwa duk da tozarta shi da kuma neman jikkata shi ko hallaka shi da mutanen nan suka yi, amma Manzon rahama bai kai kararsu zuwa ga Allah ba, kuma da Allah (SWT) Ya ba shi zabin ko ya hallaka su, sai ya zabi barinsu ba tare da wani bata lokaci ba. Har ma a wata ruwayar aka ce Manzon Allah (SAW) ya ce “Ya Ubangijina! Ka shiryar da mutanena domin ba su sani ba ne.”

Daga nan ne kuma, Annabi (SAW) ya ci gaba da tafiya a hanyarsa ta komawa Makka, inda ya sake zango a gonar wadansu mutane, har ya hadu da wani bawansu da ya zo daga garin Nainawa (garin su Annabi Yunusa Ibn Matta) kuma ya musulunta a hannun Manzon Allah (SAW). Bayan ya ci gaba da tafiya kuma sai ya sake yin zango a garin da ake kira Nakhilah. A wannan gari ne ya tashi cikin dare yana karanta ayoyin Alkur’ani a cikin Sallah, a gindin wata itaciya ta dabino, inda jama’ar aljannu suka zo suna sauraronsa. Shi ne fadar Allah a Suratul Ahkaf cewa: “Kuma ka tuna lokacin da Muka turo maka wata jama’a daga aljannu suna sauraren Alkur’ani….”

A sanadiyar haka kuma suka karbi addinin Musulunci sannan suka tafi suna ba da labarin abin al’ajabi da suka ji ga sauran jama’ar aljannu.

Bayan ya ci gaba da tafiya sai Annabi (SAW) ya isa Kogon Hira, inda ya fara shawarar yadda zai yi ya shiga garin Makka. Wannan shawara tana da muhimmanci domin kasancewar yanzu babu Abu Dalib, kuma kabilarsa ta Banu Hashim ta janye kariyarta gare shi tunda Abu Lahab ya karbi jagorancinta.

Annabi (SAW) ya shiga Makka cike da fatan Allah Ya kawo masa mafita, amma kafin ya isa Makka ya tsaya a Hara’i ya aika wa Al’aknas yana neman makwabtakarsa, Al’akhnas ya ba da uzuri cewa yana da rantsuwar wani a kansa wanda ko yake da ita ba ya ba da kariya, ya sake turawa wurin Suhail dan Amru nan ma bai samu ba, ya ba da uzuri, daga Bani Amir dan Lu’ayyu yake su kuma ba su ba da makwabtaka ga Bani Ka’ab. Sai ya aika wa Mud’imu dan Addiyyu daga Bani Naufal dan AbdulManaf dan uwan Hashim dan Abdul-Manaf kakan Annabi (SAW), to a nan ya karba masa. Sannan ya shigo Makka ya zarce masallaci ya yi Dawafi da Sallah raka’a biyu sannan ya wuce gidansa. Daga nan Mud’imu da ’ya’yansa suna dauke da makamai kewaye da shi, to da ma Mud’imu ya shelanta ya ba Annabi (SAW) makwabtaka, kuma sun yarda, ke nan duk wanda ya taba shi fitina ce.

To haka ya sa suka canja salo na neman ya zo musu da Mu’ujiza, su wai yaya za a yi a rasa wanda za a aiko sai mutum dan uwansu, a ganinsu sai fai ko Mala’ika.

Sun zauna sun kitsa kulle-kullensu sai suka aika masa ya zo madaukakan mutanensa na son magana da shi.

Hakika Annabi (SAW) yana kwadayin shiryiwarsu don haka ya fita da saurinsa gare su shi ne fadar Allah: “Hakika ka yi kusan wahalar da kanka a kansu idan ba su yi imani da wannan labari ba kana mai bakin ciki.” (Kahafi:6)

Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141, email:[email protected]