Manzon Allah: Haske mai kore duhu (19)
Sai mutumin Madina Barra’u dan Ma’arur ya yi jawabi ya ce: “Mu muna son cika alkawari da yin gaskiya da baza rayuka,” ya ce ka yi magana ya Manzon Allah! Sai Annabi (SAW) ya ce: “Bayan ya karanta Kur’ani ya yi addu’a ya kwadaitar kan addini kuma ya yi sharudda ga Ubangijinsa: 1- Ku bauta […]
Sai mutumin Madina Barra’u dan Ma’arur ya yi jawabi ya ce: “Mu muna son cika alkawari da yin gaskiya da baza rayuka,” ya ce ka yi magana ya Manzon Allah! Sai Annabi (SAW) ya ce: “Bayan ya karanta Kur’ani ya yi addu’a ya kwadaitar kan addini kuma ya yi sharudda ga Ubangijinsa:
1- Ku bauta wa Allah Shi kadai kuma kada ku hada Shi da komai. Kuma ya sa su sharadi a kansa ga Ubangiji.
Sai suka ce a kan me za mu yi mubaya’a?
Ya ce a kan:
2- Ji da biyayya.
3- Ciyarwa a cikin sauki da tsanani.
4- Horo da kyakkyawan aiki da hani daga mummuna.
5- Tsayuwa saboda Allah ba da tsoron zargin mai zargi ba.
6- Ku taimake ni idan na je gare ku, ku hana a gare ni abin da za ku hana ga kawunanku da matanku da ’ya’yanku, a ba ku Aljanna.
7- A wata ruwayar Ubbada ya ce: “Mun yi masa mubaya’a a kan ba za mu tumbbke wannan lamari ba daga ma’abotanta.
Daga nan sai Barra’u dan Ma’arur ya rike hannunsa ya ce: “Na’am na rantse da Wanda Ya aiko ka da gaskiya za mu hana ka abin da muke hana iyalinmu, mun yi mubaya’a kuma mu ma’abota takwabi ne mun yi gado. A nan sai Haisum ya katse shi ya ce: “Ya Manzon Allah! Tsakaninmu da maza akwai igiyoyi (alkawurra) da kulle-kulle idan muka yanke su shin ba ka ganin idan muka yi haka kai kuma Allah Ya bayyanar da kai (ka daukaka) ka koma wa mutanenka ka bar mu? Sai Annabi (SAW) ya yi murmushi ya ce: “Jini da jini, rusawa da rusawa, ku daga gare ni, ni daga gare ku, zan yaki wanda kuka yaka in amintar da wanda kuka amintar. Bayan Abbas dan Ubbada ya yi nasa jawabin sai suka nemi Manzo (SAW) ya shimfida hannunsa mai albarka suka fadi kalamai na karfafawa ga bin Annabi (SAW) da ba da karfinsu a kansa sai ya shimfida hannunsa As’ad dan Zurara shi ne ya fara yi masa mubaya’a a zance mafi inganci, wadansu sun ce Haisum wadansu kuma suka ce Barra’u ne. Sannan suka ci gaba da yin mubaya’a daya bayan daya. Sai dai mata da baki kawai suka yi tasu bai’ar. Daga nan sai Manzon Allah (SAW) ya umarce su da su fitar da mutum goma wadanda za su kula da mas’alolinsu, sai suka fitar da mutum 7 daga Khazraj, mutum 3 daga Awsu.
Daga Kazraj akwai:
1. Sa’ad dan Ubbada dan Dulaim.
2. As’ad dan Zurara.
3. Sa’ad dan Rabi’a.
4. Abdullahi dan Rawaha.
5. Rafi’u dan Malik dan Ijlan
6. Albarra’u dan Ma’arur.
7. Abdulahi dan Amru dan Hiram.
8. Ubbada dan Samut.
9. Almunzir dan Amru.
Daga Awsu akwai:
1. Asid dan Hadir.
2. Sa’ad dan Haisuma dan Haris.
3. Rifa’a dan Abdulmunzir an ce kuma Abul Haisum ne.
Bayan zaben wadannan sahabbai (Allah Ya kara musu yarda) sai Manzon Allah (SAW) ya ce ku a kan mutanenku kamar masu raino ne ku kasance gare su kamar yadda Hawariyawa suka kasance ga Isah dan Maryam.
Asubahi na yi Kuraishawa suka samu labari suka yi sammako zuwa hemomin mutanen Madina don su gabatar musu da hujja, sai suke ce wa wannan labarin batacce ne wato ba gaskiya ba ne. Sai Musulmin suka yi shiru ba su ce komai ba daga nan suka gane gaskiya ne suka juya kaskantattu. A karshe don su tabbatar da gaskiyar dai suka bi mutanen Madina suka riski Sa’ad dan Ubbada da Almunzir suka yi sa’ar kama Ubbada suka daure, suka yi masa duka suka ja gashinsa har suka shiga Makka da shi, sai dai Mut’imu dan Addiyyu ya cece shi domin yana masa makwabtaka a Madina shi yake kare kayansu na fatauci a can Madina. Har mutanen Madina sun yi nufin shiga Makka sai suka hango shi tafe suka fasa suka tafi Madina cikin aminci.
Darasi na Ashirin da Biyar
Shirye-Shiryen Hijira zuwa Madina
Bayan komawar mutanen Madina gida sai Annabi (SAW) ya aika musu wani sahabi mai suna Mus’ab bn Umayr don ya koya musu addini ya kuma koya musu karatun Alkur’ani. (Mus’ab yana daga cikin wadanda suka dandani wahala saboda Musulunci, shi ne matashin da ya fi kowa gata da jin dadi a garin Makka, mahaifiyarsa na da wadata, sai ta sa aka daure shi lokacin da ta ji labarin ya karbi Musulunci, da ya ji labarin an yi hijira zuwa Habasha ya balle ya gudu can. Bayan sun dawo Makka mahaifiyarsa ta nemi a sake daure shi sai ya ce duk wanda ya zo taba shi sai ya hallaka shi, ta tabbatar zai aikata don haka ta kyale ta yi ban-kwana da shi tana kuka daga nan ta janye duk wani tallafi da take ba shi na kudi da suture masu tsada. A karshe ya dawo miskini kayansa duk sun kode, har wata rana sahabbai sukan zubar da hawaye in suka tuna irin jin dadin da ya bari saboda Allah. Mus’ab ya sauka a gidan Baban Umama As’adu dan Zurara ya ci gaba da yada Musulunci gida-gida har sai da ta kai a garin Madina babu wani gida da ya rage face sun musulunta).
A wani kaulin kuma an ce su mutanen Madina ne da kansu suka nemi Manzon Allah (SAW) ya aika musu mai koyar da su addini, sai Annabi (SAW) ya aika musu Mus’ab. Mus’ab bn Umair ya kama hanya zuwa Madina a matsayin Musulmin farko da ya fita zuwa da’awah. Ya zauna a gidan Abu Umamah As’ad bn Zurarah, wanda suka hada gwiwa tare suka yi aiki tukuru wajen koyar da mutanen Madina addinin Musulunci. Wannan shawara da Annabi (SAW) ya dauka na tura Mus’ab bn Umair zuwa Madina don aikin da’awah da koyar da addini ya yi amfani matuka ta hanyoyi daban-daban. Ya sanya mutanen Madina sun samu koyarwar addinin Musulunci kuma da yawa daga cikinsu sun karbi addinin Musulunci. Sannan zuwan Mus’ab Madina ya fara shirya zukata da tunanin mutanen Madina don yarda su karbi karin jama’ar Musulmi cikinsu har da Annabi (SAW).
Daga wannan karo abin da ake magana a kai shi ne sake ganawa da Annabi (SAW) karo na biyu don samar da cikakkiyar manufa da yarjejeniyar yadda mutanen Madina za su hada kai da Annabi (SAW) don ba shi kariya da mafaka a birnin Madina. Don haka ne a shekara ta 13 da aiko Annabi (SAW) sai mutanen Madina suka aiko da wakilansu don ganawa da Manzon Allah (SAW) a Akabah lokacin aikin Hajji. Wannan tattaunawa da ake yi tsakanin Annabi (SAW) da mutanen Madina har yanzu a cikin sirri ake yi. Mushirikan Makka da mushirikan Madina duk ba su da masaniya kan ganawar da abubuwan da ta kunsa. Don haka da aka shirya zuwa aikin Hajji, ayarin mutanen Madina ya kunshi Musulmi da mushirikai. Akwai akalla Musulmi 73 da suka taho aikin Hajji daga Madina. A lokacin da suka isa filin Mina, sai Musulmin Madina suka wakilta mutum 12 daga cikinsu don ganawa da Manzon Allah (SAW) wadda aka yi cikin tsakiyar dare bisa matakan sirri. A wannan taro Manzon Allah (SAW) ya nemi taimakonsu, ya ce ‘Ina so ku ba ni kariya tamkar yadda kuke kare matanku da ’ya’yanku.’
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]