Manzon Allah: Haske mai kore duhu (20)
Mun dauki mako 19 fitowa 20 muna gabatar da wani abu kan tarihin Manzon Allah (SAW) a wannan fili. Hakika rayuwar Manzon Allah rayuwa ce da ke cike da haske, rayuwa ce ta gwagwarmaya, rayuwa ce ta ilimi, rayuwa ce ta iya shugabanci (siyasa), rayuwa ce da dan Adam bai taba ganin irinta ba a […]
Mun dauki mako 19 fitowa 20 muna gabatar da wani abu kan tarihin Manzon Allah (SAW) a wannan fili. Hakika rayuwar Manzon Allah rayuwa ce da ke cike da haske, rayuwa ce ta gwagwarmaya, rayuwa ce ta ilimi, rayuwa ce ta iya shugabanci (siyasa), rayuwa ce da dan Adam bai taba ganin irinta ba a tarihinsa. A yau muke kawo karshen littafi na daya na wannan tarihi na mafificin halitta, wanda duk yadda mutum ya kai da kokarin gano hakikaninsa (SAW) sai dai ya tsinci kadan domin Mahaliccci ya riga Ya ce da shi: “Lallai kai kana da halaye mafiya girma.” Kuma za mu dan dakata sai wani lokaci mu dora daga littafi na biyu, domin mu ba mutane dama su je su yi nazari kan abin da muka gabatar. Allah Ya sa mu yi kokarin dabbaka dimbin darussan da ke cikin rayuwar Manzon Allah (SAW) da muka gani a cikin wannan littafi :
Manzon Allah: Haske mai kore duhu (20)
Daga Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa
Sai Barra’u bn Ma’arur ya damke hannun Manzon Allah (SAW) ya ce “Na rantse da Wanda Ya aiko ka da gaskiya, za mu kare ka tamkar yadda za mu kare iyalanmu da ’ya’yanmu. Lallai ne mu mayaka ne da suka gaji yaki iyaye da kakanni. Daga nan sai tattaunawa ta ci gaba har aka samu cikakkiyar fahimtar juna tsakanin Annabi (SAW) da wakilan mutanen Madina. Bayan an amince da bayanan Manzon Allah (SAW) sai mutanen Madina da ke wurin taron duka suka yi masa mubaya’a, tare da alwashin cewa:
- Za su tsarkake Allah Shi kadai wajen bauta
- Za su bayar da mafaka kuma su taimaki Manzon Allah (SAW) da sahabbansa.
- Za su ba da kariya da tsaro ga Manzon Allah (SAW) daga duk abin da zai cutar da shi.
- Za su dauki nauyin bukatar da za ta taso ta dukiya sakamakon kulla wannan yarjejeniya, komai nauyin abin.
- Za su yi biyayya ga Manzon Allah (SAW) a lokacin sauki da tsanani.
- Ba za su yi jayayya ko juya baya ga dokokin da za a kallafa a kansu ba.
- Za su rungumi duk abin da yake na halal da kaurace wa haram.
- A kowane yanayi ko lokaci za su tsaya tare da kare gaskiya a tafarkin Allah ba tare da tsoro ko ja da baya ba.
Wannan shi ne cikakken alkawarin da aka kulla a tsakanin mutanen Madina da Annabi (SAW) wanda ya share fagen hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina a shekara ta 13 da aiko shi zuwa ga al’ummar duniya.
Darasi Na Ashirin Da Shida
Hijirar Musulmi Zuwa Madina
Da gama bai’a sai hijira ta gaba daya ta fara kankama daga Makka zuwa Madina, wadansu sahabbai da suka yi hijira zuwa Habasha, su ma sai suka rika tafiya Madina. Manzon Allah (SAW) ya yi mafarki da wannan hijirar har ya ba Musulmi labarinta ya ce: “Na ga hakika ina hijira daga Makka zuwa wata kasa da take da dabinai, sai zatona ya ba ni (kasar) Yaman ce ko Hijir, sai ga shi ashe Madina ce.”
Farkon wanda ya fara yin hijira shi ne Abu Salma Al-Makhzumi mijin Ummu Salma wadda bayan rasuwarsa ta auri Annabi (SAW).
Mutanenta sun hana ta tafiya sai dangin Abu Salma suka kwace mata danta sai Abu Salma ya tafi shi kadai, sai dai ita ma bayan shekara sun bar ta ta riske shi a can Madina. Wannan ya faru ne tun kafin a yi bai’a da shekara daya.
Daga nan sai Amir dan Rabi’a da matarsa Laila ’yar Hasima da Abdullahi dan Ummu Maktum (Allah Ya kara musu yarda). Musulmi sun ci gaba da yin hijira amma suna sulalewa ne su tafi a boye don tsoron Kuraishawa kada su hana su, har sai da Umar dan Khattabi (Allah Ya kara masa yarda) ya yi tasa a bayyane bayan ya je Ka’aba ya yi Dawafi ya tunkari manyan mushrikai rataye da bakarsa da takobi rike a hannunsa, ya je inda suke zaune ya ce zai yi hijira wanda yake so uwarsa ta haifi wani, ’ya’yansa su yi maraici, matarsa ta zama bazawara, to ya biyo shi bayan gari, ai kuwa babu wanda ya iya cewa ko uffan balle ya tari gabansa, daga nan wadanda suke da rauni suka fito suka bi shi zuwa Madina su ashirin.
Musulmi dukansu sun yi hijira sai fa Annabi (SAW) da Abubakar da Aliyu da Suhaib da Zaid dan Harisa da wadansu kadan wadanda suke da rauni kwarai ba za su iya jure wahalhalun tafiya mai nisa ba su kawai suka rage. Abubakar (RA) ya shirya zai tafi Annabi (SAW) ya dakatar da shi ya ce ni ma ina jira a yi mini izini ne, sai Abubakar (RA) ya ce mahaifina fansa gare ka ya Manzon Allah! Kai ma kana burin haka? Sai ya ce: Na’am, sai Abubakar (RA) ya zauna don ya sahibce shi kuma ya tanadar musu abin hawa biyu da za su hau.
Darasi na Ashirin da Bakwai
Haduwar Kuraishawa a Gidan Nadwa da yunkurin kashe Annabi (SAW)
Kuraishawa sun gigita da ganin Musulmi sun samu mafaka inda za a kiyaye su, a ganinsu wannan babban hadari ne da barazana ga addininsu da kasuwancinsu.
A kan haka sai suka taru a Gidan Nadwa a ranar 26 ga Safar shekara ta 14 da aiko Manzon Allah (SAW), suna so su dauki mataki na karshe tun Annabi (SAW) bai fice daga garin ba. Manyan shugabannin Kuraishawa sun halarci wannan taro, ba shugabanninsu kadai ba har Iblis sai da ya halarci wannan majlisi don ya taya su kulla makirci, ya yi shigar siffar tsoho, bayan ya nemi izininsu ya ce daga Najad yake.
Abul Aswad shi ya fara magana ya ce: “Mu kore shi daga kasarmu, mu gyara al’amuranmu kada mu damu da inda ya tafi.”
Sai tsohon Najad ya ce: “Kun ga ya iya zance da zakin magana da rinjayar da zukatan maza, idan ya fita to zai samu mutane suna kewaye da shi, zai yi amfani da su ya aikata muku abin da ya ga dama.”
Sai Abul-Bukhtari ya ce “Ku daure shi ku kulle masa kofa har abin da ya riski mawaka ya riske shi na mutuwa”.
Sai tsohon Najad ya ce: “Wallahi idan kuka daure shi sai an fitar da al’amarinsa zuwa ga sahabbansa tunda suna fifita shi a kan iyayensu da ’ya’yansu, za su fi karfinku su rinjayeku ku dai duba wani ra’ayin ba wannan ba.”
Sai Abu Jahil ya ce: “Mu samu matashi daga cikin kowace kabila majiyi karfi su je su yi masa bugun mutum daya su kashe shi, sai jininsa ya watsu a kan kowace kabila, kun ga idan haka ta faru Banu Abdul-Manaf ba za su iya yakar dukan kabilar Kuraishawa ba, sai su yarda da diyya mu biya su.”
Sai tsohon Najad ya ce wannan ita ce magana ta wannan mutumin, wannan shi ne ra’ayin da ba wani da ya fi shi. Kuma kowa ya tabbatar da wannan ra’ayin sai suka ci gaba da shirin yadda za su zartar da kudirinsu.
Sai dai abin da ba su sani ba Allah Ya aiko Mala’ika Jibril (AS) ya labarta wa Annabi (SAW) dukan makircin da mushirikai suka kulla za su yi masa daga nan aka yi masa izini da yin hijira da iyakance masa lokacin da zai fita kuma aka ce kada ya kwanta a gadon da yake barci a wannan dare.
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]