Manzon Allah: Haske mai kore duhu (23)

Darasi na Talatin: Hijirar Iyalan Gidan Annabi (SAW) da masu rauni Kamar yadda muka ji a baya da yawa daga cikin sahabbai sun riga sun yi hijira. Shi kuma Aliyu (RA) ya zauna tsawon kwana uku a Makka bayan hijirar Annabi (SAW), ya mayar wa mutanen Makka da kayan ajiya da na amana wadanda suke […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (23)

Darasi na Talatin:

Hijirar Iyalan Gidan Annabi (SAW) da masu rauni

Kamar yadda muka ji a baya da yawa daga cikin sahabbai sun riga sun yi hijira. Shi kuma Aliyu (RA) ya zauna tsawon kwana uku a Makka bayan hijirar Annabi (SAW), ya mayar wa mutanen Makka da kayan ajiya da na amana wadanda suke a hannun Annabi (SAW), sannan ya tafi a kasa har ya tarar da Manzon Allah (SAW) a Kuba, ya sauka a wurin Kulsum dan Hadam.

A lokacin da Manzon Allah (SAW) ya tabbata a Madina ya aika Zaid dan Harisa da Abu Rafi’i zuwa Makka sai suka taho da Fatima da Ummu Kulsum da Uwar Muminai Sauda da Ummu Ayman da Usama dan Zaid. Abdullahi dan Abubakar shi ma ya fito tare da iyalin Abubakar, su ne: Ummu Ruman, Asma’u da A’isha Uwar Muminai (Allah Ya kara musu yarda baki daya) suka taho Madina. Wannan hijira tasu ta kasance bayan hijirar Annabi (SAW) da wata shida ne.

Shi kuma Suhaib da ya tashi yin hijira mushirikai suka hana shi sai ya danka musu dukiyarsa gaba daya mai yawan gaske sai suka kyale shi, lokacin da ya isa Madina sai yake labarta wa Annabi (SAW) yadda suka yi da mushirikai sai Annabi (SAW) ya ce kasuwancin Baban Yahaya ya yi riba! (wato Suhaib Allah Ya kara masa yarda).

Mushirikai sun daure Musulmi masu rauni suka hana su yin hijira suka ci gaba da azabtar da su don su bar addinin Musulunci, daga cikinsu akwai: Walid dan Walid da Iyash dan Abi Rabi’a da Hisham dan Al’as. Manzon Allah (SAW) ya rika yin addu’a a sallolinsa biyar ga kafiran da suke tsare da wadannan mutane, wannan addu’a ita ce asalin Alkunut, bayan wani lokaci kafirai suka fitar da dukkan Musulmi daga gidajensu suka amshe dukiyarsu daga nan suka yi hijira zuwa Madina.

Bayan saukar Musulmi Madina wata matsala ta same su domin sun baro kasarsu wadda suka saba da ita, kuma sabanin jinyace-jinyace da suka addabe su sai Annabi (SAW) ya yi musu addu’a wadda a cikinta ya ce: “Ya Allah! Ka soyar da Madina gare mu kamar yadda muke son Makka ko sama da haka. Sannan Ka inganta ta, sannan Ka sa mana albarka cikin sa’inmu da mudunmu. Kuma Ka dauke annobanta Ka sanya shi a Juhfa.”  Allah kuwa Ya amshi wannan addu’a, sai Muhajirai suka samu waraka daga dukkan cututtuka, suka samu sakewa da walwala suka rika jin son Madina a zukatansu.

 

Darasi na Talatin da Daya:

Ayyukan da  Annabi (SAW) ya fara yi a Madina

Annabi (SAW) ya sanya ginshikan rayuwa na Musulunci na farko a Madina. Wannan ya sa Musulmi suka zamo wata daula mai cin gashin kanta wadannan ayyuka su ne:

  1. Gina masallaci inda taguwarsa ta durkusa, ya sayi wannan fili ne don na wadansu marayu ne guda biyu. Girman tsawo da fadin filin zira’i 100 ne.

An gina shi da tubali da duwatsu, rufinsa na ganyen dabino ne, yana da kofofi uku, alkibilarsa ta kasance daga Arewa inda Baitul Makadis yake.

Annabi (SAW) ya sanya hannunsa mai albarka aka yi aikin tare da shi. Har yakan dauki duwatsu da tubali tare da Muhajirai da Ansar wanda haka ya kara sanya musu nishadi a cikin aikin, a gefen masallacin kuma an gina dakuna biyu na Sauda da A’isha (Allah Ya kara musu yarda), a lokacin su kadai ne kawai, ya tare da A’isha a cikin Shawwal na wannan shekara ta farko da yin hijira.

Bayan an gina wannan masallaci ne sai Musulmi suka fara zuwa suna halartar jam’in salloli biyar a cikinsa, sai wadansu su jinkirta wadansu kuma su zo da wuri. Sai Annabi (SAW) ya nemi shawarar Musulmi kan yadda za a fadakar da mutane lokacin Sallah sai wadansu suka ba da shawarar a rika daga wuta, wadansu kuma suka ce a yi busa wadansu suka ce a rika buga ganga. Sai Umar (Allah Ya kara masa yarda), ya ce ko dai a aiki wani mutum ya rika kiran Sallah sai Annabi (SAW) ya karbi shawarar Umar, ashe dama Abdullahi dan Zaid dan Abdu Rabbihi mutumin Ansar ya yi mafarki da kiran Sallah sai ya zo yaba Annabi (SAW) labari da haka. Sai ya ce masa mafarkinka gaskiya ne, sai ya yi izini ga Bilal (Allah Ya kara masa yarda) da ya kira Sallah don yana da madaukakiyar murya. Bayan ya idar sai Umar (RA) ya rike mayafinsa ya ce wallahi hakika na ga misalin haka. Sai aka karfafa wannan, daga wannan ranar kiran Sallah ya zama daya daga ayyukan Musulunci.

  1. Ya kawo karshen gabar da take a tsakanin kabilun Awsu da Khazraj.
  2. Ya kulla ’yan uwantaka a tsakanin kowane Muhajiri da Ansar (mutanen Madina). ’Yan uwantaka wani dauri ne na zumunci mai karfi a tsakanin Muhajiri da Ansar wadda Annabi (SAW) ya kulla ta dalilin irin so da kauna da Ansarawa mutanen Madina suka nuna ga masu hijira; ya kai har suna jayayya kowa na so Muhajiri ya sauka gidansa don ya dauki nauyin bakuncinsa, suna raba komai da suka mallaka su dauki rabi suba dan uwansu Muhajiri rabi. Suna raba gidansu da dukiyarsu da gonakinsu har matansu ma sukan bai wa Muhajiri zabi. Misalin idan matan hudu ne idan ya zabi biyu sai su sake su, suna dai fifita Muhajirai a kan kansu. Haka nan suna gadon juna kafin a saukar da ayar wadanda suka fi cancanta da gado, wato aka shafe hukuncin, a kan wannan ne suka samu yabo na musamman daga Allah

An yi wannan kulli ne a gidan Anas dan Malik (Allah Ya yarda da su baki daya).

Abdurrahman dan Awfu ne bai karbi tayin ba da dan uwansa ya nemi ya zabi wacce ya fi so, sai dai ya ce Allah Ya yi albarka a iyalinka da dukiyarka amma a nuna mini kasuwa, aka nuna masa ya shiga neman na kansa inda a karshe Allah (SWT) Ya yi albarka a kasuwancin har ya zama gawurtaccen mai arziki kuma ya auri ’yar mutanen Madina.

  1. Ya Sanya tausayin yara a zukatan manya.
  2. Ya ilimantar da su ilimin addini da rayuwa.
  3. Ya kula da marayu da marasa gata.
  4. Ya dauki alkawarinsu a kan rashin daukar fansa a tsakaninsu.
  5. Ya yi daidaito wurin ba da haoki tsakanin Musulmi da Yahudawa.
  6. Ya kulla yarjejeniya daYahudawan Madina.
  7. Wanda ba Musulmi ba daga Yahudawa zai samu taimako da daidaito.

Larabawa kafin wannan ba su kasance suna da wani abu mai kama da hukuma ba ko wani tsari na game ba, babu abin da suka sani sai jayayya da yamutsi.

Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhamma Sa’idu Gamawa ta tarho: