Manzon Allah: Haske mai kore duhu (24)

Darasi na Talatin da Biyu: Yadda aka assasa zamantakewar al’ummar Musulmi Wannan tsari na ’yan uwantaka ya sa Musulmi sun samu ’yancin kansu, sun san abin da ya wajaba da sanin hakkoki na zamantakewa ta haka suka zama al’umma daya tsintsiya madaurinta daya, suka fita daga tsarin hayaniya da rashin tabbas. A Madina akwai mushirikai […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (24)

Darasi na Talatin da Biyu:

Yadda aka assasa zamantakewar al’ummar Musulmi

Wannan tsari na ’yan uwantaka ya sa Musulmi sun samu ’yancin kansu, sun san abin da ya wajaba da sanin hakkoki na zamantakewa ta haka suka zama al’umma daya tsintsiya madaurinta daya, suka fita daga tsarin hayaniya da rashin tabbas.

A Madina akwai mushirikai da Yahudawa wanda akidarsu ta addini ba daya ba ce, don haka Annabi (SAW) ya tara su kuma ya dauki wasu alkawurra a rubuce daga wajensu wadanda maslaha ce ga kyakkyawar zamantakewa da tabbatar da manufofin shari’a. Ga abin da aka rubuta kan sharuddan zamantakewa tsakanin Musulmi da mushirikai:

1. Muminai da Musulmi na Kuraishawa da na Madina da wadanda suka hadu da su suka yi jihadi tare lallai su al’umma guda daya ce.

2. Bayar da diyya da fansa da take tsakaninsu za ta kasance kamar yadda suke a da.

3. Su rika tsayuwa suna fito-na-fito da duk wani fasadi da wuce iyaka da zalunci koda kan dan daya daga cikinsu ne.

4. Mumini ba zai yaki dan uwansa mumini ba ta hanyar samun taimakon kafiri.

5. Lallai amincin Musulmi daya ne.

6. Wanda ya kashe mumini da nufi to a yi masa kisasi sai dai in mai jibintarsa ya yarda yana wajaba ga Musulmi su tsayu su kalubalanci mai kisan.

7. Ba ya halatta ga Musulmi ya taimaki wanda za a yi wa haddi (wato mai laifin da ya cancanci haddi ) ko ba shi kariya.

8. Lallai idan suka yi sabani a wani abu to a mayar da shi ga Allah da ManzonSa (SAW).

 

Alkawuran da Annabi (SAW) ya rika daga Yahudawa

1. Su al’umma daya ce tare da muminai amma su yi addininsu, Musulmi su yi nasu kuma ciyarwarsu na kansu su ma Musulmi su ciyar da kansu.

2. A tsakaninsu akwai taimako kan duk wanda ya yaki abin da yake cikin wannan takarda ko ya kawo hari Madina kowanensu zai kare ta daga bangarensa.

3. A tsakaninsu nasiha ce da biyayya ban da aikata laifi.

4. Kuma kada mutum ya riki dan uwansa da laifin magajinsa.

5. Lallai a taimaki wanda aka zalunta.

6. Lallai ne su ciyar tare da muminai muddin suna fagen daga.

7. Madina harami ce ga ma’abota wannan takarda.

8. Abin da yake kasancewa na jayayya to a mayar da shi ga Allah da ManzonSa (SAW).

9. Kada a yi kasuwanci da Kuraishawa ko wanda ya taimake su.

10. Kada wanda ya juya wannan rubutun in ba azzalumi ba.

Da wannan alkawura ne Musulmi da mushirikai da Yahudawa mazauna Madina suka samu tsari na bai-daya, wanda ya sa Madina ta wayi gari daula mai zaman kanta da shugabanci. Musulmi su ke da magana abar zartarwa a cikinta, Manzon Allah (SAW), shugabanta.

Manzon Allah (SAW) ya sake a cikinta, Musulmi kuma na biye da shi, ya kasance yana halartar majilisi na Musulmi da wanda ba na Musulmi ba, yana karanta musu ayoyin Allah yana tsarkake wadanda suka yi imani da Allah daga cikinsu, yana sanar da su Littafin Allah da hikima.

 

Darussan da za a dauka a karkashin yarjejeniyar da Annabi (SAW) ya kulla da Yahudawa

1. Manzon Allah (SAW) mutum ne wanda ya iya zamantakewa da kowace irin al’umma.

2. Kwarewar Annabi (SAW) wajen sasanta tsakanin al’umma da rinjayar da abin da zai kawo maslaha. Duk da cewa Allah (SWT) Ya umarci AnnabinSa (SAW) ya dauki makami don kare kansa da kare izzar addinin Musulunci, amma wannan turbar ba ita daya ce Allah Ya sanya ta zama hanyar zamantakewa a tsakanin al’ummomin duniya ba. Asali ma al’amura masu yawa, Manzon Allah (SAW) ya warware su ne ta hanyar maslaha da sasantawa.

Alal hakika Manzon Allah (SAW) kwararren mai sasantawa ne, wanda ya  ba da gudunmawa wajen sasanta Kuraishawa lokacin jayayya a kan gyaran Ka’aba, tun yana kuruciyarsa. Ga shi kuma yanzu, Annabi (SAW) ya kasance zababben Allah kuma dan sakonSa, fiyayyen halitta, jagoran tarbiyya kuma mafificin masu hikima. Don haka lallai ne Annabi (SAW) ya tabbata abin misali kuma makaranta a fagen samar da maslaha da sasantawa a tsakanin al’ummomi.

Yayin da ya zo Madina, Annabi (SAW) ya kulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninsa da mutanen Madina jim kadan bayan yin hijirarsa. Wannan yarjejeniya kuwa ta kunshi sharuddan zaman tare da aka shimfida a tsakanin Larabawan Madina masu masaukin baki ko ‘Ansar -mataimaka’ kamar yadda aka sanya musu, da Yahudawan Madina da kuma  wadanda suka yi kaura daga Makka zuwa Madina wato ‘muhajirai’. Wannan rubutacciyar yarjejeniya, Manzon Allah (SAW) ya tsara ta ce don kyautata zaman tare a tsakanin al’ummomi mabambanta, da Allah Ya kaddara zamansu a kasa daya. A karkashin wannan yarjejeniya an amince cewa za a dauki matsayi guda a tsakanin dukkan al’ummomin, wajen al’amarin yaki ko zaman lafiya. Babu wata al’umma da za ta zartar da wani sulhu ko ta kudirta yaki ita kadai tsakaninta da abokan gaban sauran al’ummomin. Yahudawa da ke zaune a karkashin jagorancin da ke hannun Annabi (SAW) dole ne a ba su kariya daga duk abin da zai cutar da su. Suna da cikakkiyar dama tamkar kowa a Madina wajen zaman tare da kare hakkin juna. Haka abokan amincin Yahudawa dole ne a kare musu mutuncinsu tare da ba su tsaro da ’yanci yadda ya dace. Wanda kuma aka kama da laifi dole a hukunta shi kuma a yi masa horo. Amma su ma Yahudawa dole su ba da gudumawarsu wajen samar da kariya ga Musulmin da ke Madina a kan abokan gabansu. Cikin garin Madina kuma ya zama wurin aminci ga kowane bangare da ya amince da wannan yarjejeniya. Daga karshe aka rufe yarjejeniyar da cewa duk wani sabani da ya taso bisa aiwatar da yarjejeniyar wajibi ne a maida al’amarin zuwa ga Manzon Allah (SAW) don zartar da hukuncin Allah a kanta. Wannan yarjejeniya hakika ta samar da yanayi na zaman lafiya da amincewa da juna na tsawon lokaci, kafin Yahudawa su hada kai da munafukan da ke cikin Musulmi don karya ka’idojin da ke cikinta.

Za a iya samun Ustaz Aliyu Gamawa ta tarho: +2348023893141, 08095329747

email:[email protected]