Manzon Allah: Haske mai kore duhu (25)
Jihadin Manzon Allah (SAW) Daya daga cikin abin da addinin Musulunci yake koyarwa shi ne sanya kowane al’amari a bisa muhallinsa. Kuma hukunce-hukunce da dokoki masu yawa an tsara su ne mataki-mataki don cikar hikimar Ubangiji (SWT). Musulmi a farkon aiko da sako sun fuskanci musgunawa da tsangwama. Akwai wadanda aka gana wa azaba iri-iri, […]
Jihadin Manzon Allah (SAW)
Daya daga cikin abin da addinin Musulunci yake koyarwa shi ne sanya kowane al’amari a bisa muhallinsa. Kuma hukunce-hukunce da dokoki masu yawa an tsara su ne mataki-mataki don cikar hikimar Ubangiji (SWT). Musulmi a farkon aiko da sako sun fuskanci musgunawa da tsangwama. Akwai wadanda aka gana wa azaba iri-iri, akwai wadanda aka hallaka baki daya a dalilin karbar addinin Musulunci. Shi kansa Annabi (SAW) ya fuskanci wahalhalu masu yawa. An musguna masa, an cutar da shi, har ya kai an yi masa rauni jina-jina, duk kan isar da sakon Allah. Har sai da a karshe Annabi (SAW) da sahabbansa suka bar garin iyayensu, suka bar matansu da dukiyoyinsu, suka tafi gudun hijira don kawai sun yi imani kuma sun amsa kiran Allah. Amma duk da wadannan abubuwa, a wancan lokaci ba a dora wa Annabi (SAW) da sauran Musulmi komai ba sai isar da sakon Allah, wato yin wa’azi. Aka kuma neme su da yin hakuri game da duk musgunawar da ake musu.
Amma bayan Annabi (SAW) da sahabbansa sun kaura zuwa Madina, sun fara samun natsuwa, sun fara dandana zakin imani kuma sun kubuta daga hanun azzalumai mushirikai, to babu abin da ya rage gare su face su kare martabar addinin Allah, su kuma kare kawunansu daga cutarwa. Domin yanzu sun fara kawo karfin da za su tsaya da kafafuwansu, su kare kawunansu su kuma kare izzar addininsu. Don haka sai Musulunci ya bude musu kofar kare kai ta hanyar yaki da takobi, don ganin sun kare martabarsu kuma kalmar Allah ta daukaka a doron kasa.
An bai wa Musulmi izinin su fara kare kawunansu da makami ne a shekarar hijira ta farko, cikin watan Zul-Hajji. Wannan izini an bayyana shi karara cikin fadin Allah (SWT):
“An yi izini ga wadanda ake yakarsu da cewa lallai an zalunce su, kuma lallai ne Allah, hakika, Mai ikon yi ne a kan taimakonsu.” (Hajj:39).
Izinin da aka bai wa Musulmi da su yi fada da abokan gaba, don kare kansu, tamkar wata dama ce da Allah (SWT) ya bai wa Musulmi na kare izzar addinin Musulunci da tabbatar da wanzuwar kalmar Allah a doron kasa. Har ila yau kuma Musulmi sun samu wata dama ta shirya zukatansu da tanadin kayan yaki, kafin lokacin yakin ya zo. Amma duk da cewa an ba da izinin yin jihadi a matakin farko, sai dai ba a tilasta musu shi ba sai daga baya. Domin a wannan lokaci karfin Musulmi bai kai matsayin yadda za su iya tunkarar rundunonin mushirikai ba. Bayan wani lokaci kuma sai Allah (SWT) ya yi umarni ga Musulmi su shirya yin yaki da abokan gaban addini Musulunci, kamar yadda ya zo cikin Suratul Bakara cewa;
“Kuma ku yaki wadanda suke yakinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsokana, lallai Allah ba Ya son masu tsokana.”(Bakara: 190).
Daga wannan umarni kuma aka samu damar fita yake-yake don gwabzawa da mushirikan Makka a lokuta daban-daban. Su ma Yahudawan Madina da suka warware alkawarin zaman lafiya da Annabi (SAW) suka kuma hada baki da abokan gaba tare da yi wa Annabi (SAW) zagon kasa, sai Allah (SWT) Ya ba da izinin a yanke musu hanzari, sannan idan sun doge a kan neman cutar da Musulmi sai a yake su. Allah (SWT) Yana cewa:
“Kuma in kun ji tsoron wata yaudara daga wadansu mutane, to, ka jefar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita. Lallai ne Allah, ba Ya son mayaudara. Kuma wadanda suka kafirta kada su yi zaton sun tsere: lallai ne su, ba za su gagara ba. Kuma ku yi tattali, dominsu, abin da kuka samu ikon yi na wani karfi, kuma da ajiyar dawaki, kuna tsoratarwa, game da su, ga makiyin Allah kuma makiyinku da wadansu, baicin su, ba ku sansu ba, Allah ne Yake saninsu, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, za a cika muku sakamakonsa, kuma ku ba a zaluntarku.”(Anfal: 58-60)
Manzon Allah (SAW) ya fita filin yaki kuma ya nuna jaruntaka da karfin hali a filin jihadi. A wani Hadisi Annabi (SAW) yana cewa “An umarce ni da in yaki mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya furta kalmar ‘La ilaha illal-Lah’ to jininsa da dukiyarsa sun kubuta daga gare ni, sai dai da hakkin shari’a, kuma hisabinsa na wurin Allah.” (Bukhari da Muslim).
Don haka a matsayinsa na jagoran al’ummar Musulmi, Manzon Allah (SAW) ya zama abin misali a filin daga. Bai taba guduwa ko ja da baya ba. Kuma bai taba firgita ko nuna tsoro don ganin karfin abokan gaba ba. Gwani ne a wurin tsara dabarun yaki kuma gwani ne wajen tsara ka’idojin gunadar da yaki. Ya fito da ka’idoji na fuskantar abokan gaba wadanda hatta duniyarmu ta yau da ke tutiya da kare ’yancin dan Adam ba ta kai gare shi ba. A karkashin ka’idojin yaki na Manzon Allah (SAW).
– Babu kashe yara da tsofaffi da mata a wurin yaki.
– Babu kai hari wuraren ibadar mutane
– Babu lalata kayayyakin gonaki da sare bishiyoyi.
– Babu sanya guba a abinci ko abin shan abokan gaba ko na dabbobinsu.
– Kuma ba a karya yarjejeniyar tsagaita wuta idan an kullata da abokan gaba.
– Ana kula da hakkokin ribatattun yaki, ba za a yi musu kisan gilla ba. Har ma ana ba da damar fansa sai ga wadansunsu, kamar ta hanyar amfanar da al’umma da sauransu.
Malaman tarihi sun yi sabani a kan yawan yake-yaken da aka yi a lokacin Manzon Allah (SAW). Wadansu sun ambaci adadinsu da cewa 28 ne, wadansu kuma suka ce 17 ne ko 16, da dai sauransu. Amma Manzon Allah (SAW) shi da kansa ya jagoranci fita yaki inda aka fafata da shi har guda takwas. Wadannan yake-yake kuwa su ne;
- Yakin Badar: Wanda aka yi a shekara ta biyu Bayan Hijirar Manzon Allah (SAW), a cikin watan Ramadan. Allah Ya bai wa Musulmi rinjaye kuma abokan gaba sun sha kashi. A wannan yaki ne aka kashe manyan kafirai irin su Abu Jahil.
- Yakin Uhud: Wanda aka yi a shekara ta uku Bayan Hijira a cikin watan Shawwal. A wannan yaki Allah (SWT) ya jarrabi Musulmi sun sha wuya a hanun mushirikai, amma daga baya Allah Ya taimake su a kan kafirai. Bayin Allah sahabbai 70 sun yi shahada.
iii. Yakin Khandak: (ko Yakin Ahzab) Wanda aka yi a shekara ta biyar Bayan Hijira cikin watan Shawwal.
- ib. Yakin Banu Kuraizah: shi ma an yi shi ne a shekara ta biyar Bayan Hijira.
- b. Yakin Maraysa’i: Wanda aka yi a cikin shekara ta shida Bayan Hijira.
- b Yakin Khaibar: Wanda aka yi a shekara ta bakwai Bayan Hijira. Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa Khaibar da rundunar muminai kimanin mutum 1,400 don tunkarar Yahudawa da suka yi gangami a wajen Madina, bayan an kore su daga cikin gari. An gwabza yaki na kwanaki da dama kafin cikakkiyar nasara ta tabbata ga Annabi (SAW) da sahabbansa.
bii. Fathu Makka: Wanda aka yi a shekara ta takwas Bayan Hijira. Wannan fitowa ce ta Manzon Allah (SAW) da niyyar shiga garin Makka, inda kuma ba a fafata sosai a cikinta ba saboda mushirikai sun karaya tun kafin rundunar Manzon Allah (SAW) ta iso gare su.
biii. Yakin Hunain: Wanda aka yi a shekara ta takwas Bayan Hijira. Wannan haduwa ce tsakanin muminai da kabilun Hawazin da Sakif wadanda suka hada kai don yakar Annabi (SAW). An gwabza yaki a ranar 6 ga Shawwal, a filin Hunain da ke kimanin mil 6 daga garin Makka. A wannan karo har an yi kusa a cimma rundunar Annabi (SAW) kafin daga bisani taimakon Allah ya riske su.
***
Duk cikin wadannan yake-yaken da aka yi, mafi muhimmanci a cikin su shi ne yakin Badar wadda aka yi shi ranar goma sha bakwai ga watan Ramadhan a lokacin hijira tana shekara biyu, kasancewarsa matakin farko na sama wa Musulmi yanci, daraja da daukaka. Duk da cewa mushurikai sun nunka yawan Musulmi har sau uku, kuma sun fi su tanadin makamai, amma Allah (S.W.T.) cikin baiwarsa da izzarsa sai ya taimaki annabinsa ya runjayi wadannan azzaluman mushirikai, makiya addininsa. A cikin wannan yaki ne aka kashe manya manyan kafirai har saba’in. Daga cikinsu akwai Abu Jahal, Umayyatu dan Khalaf, Utbah da Shaybah ’yayan Rabi’ah da dai sauransu. Sannan kuma an kama ribatattun yaki har guda saba’in. Annabi (SAW) da sahabbansa sun dawo Madina cikin farin ciki da sakankancewa a kan Allah (S.W.T.) yana tare da su cikin taimakonsa. Don haka wannan al’amari ya jaddada wa wadanda suke tare da Manzon Allah cewa nasara tana tare da su har sai addinin Allah ya rinjayi duniya baki daya.