Manzon Allah: Haske mai kore duhu (28)

Yau ma cikin ikon Allah za mu ci gaba da kawo tarihin Shugaban Halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda ya jagoranci kafa addini da daular da babu irinta a tarihin dan Adam, kuma babu wani dan Adam da ya yi irin haka a tarihi. Rayuwarsa makaranta ce mafi girma a tarihin dan Adam: Darussa  a Yakin […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (28)

Yau ma cikin ikon Allah za mu ci gaba da kawo tarihin Shugaban Halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda ya jagoranci kafa addini da daular da babu irinta a tarihin dan Adam, kuma babu wani dan Adam da ya yi irin haka a tarihi. Rayuwarsa makaranta ce mafi girma a tarihin dan Adam:

Darussa  a Yakin Uhudu

  1. Musulmi sun fahimci da’ar shugaba tana da tsanani.
  2. Mushirikai da Yahudawa sun kara samun karfi ta dalilin wannan yaki har sun yi tsammanin gamawa da Musulmi.
  3. Wannan yaki ya bayyana munafukai.
  4. An ga soyayyar sahabbai ga Annabi (SAW)
  5. Illar yada jita-jita da aiki da ita.
  6. Jaruntar Annabi (SAW) ta kara bayyana.

Yakin Uhudu ya kare wanda ya faru a 7 ga Shawwal shekara ta 3 Bayan Hijira wadda ta yi mawafaka da 23 ga watan Maris shekara 625 Miladiyya.

Bayan an gama rufe matattu Annabi (SAW) da sahabbansa sun nufo Madina inda mata makusantan wadanda suka yi shahada suka fito, sun hadu da Annabi (SAW) suka yi masa ta’aziyya sai wata mata daga Bani Dinar da ta rasa mijinta da mahaifinta da dan uwanta take tambayar halin da Annabi (SAW) yake ciki. Aka ce mata yana tare da godiyar Allah, sai ta ce a nuna mata shi aka nuna mata shi, sai ta ce “Kowace musiba karama ce bayanka.”

A wannan ranar Musulmi sun yi kwanan gadi duk da halin da suke ciki na raunuka da gajiya da bakin ciki da radadi.

Manzon Allah (SAW) ya ga ba makawa a bibiyi motsin makiya.

Yakib Hamra’ul Asad

Da gari ya waye an kira Musulmin da suka halarci Uhudu kawai su fito su hadu da makiya, suka amsa da mun ji kuma mun  yi da’a, sun fita har suka kai Hamra’ul Asad kimanin mil 8 daga Madina.

Su kuma mushirikai ba su koma Makka ba sun sauka ne a Ruha’i mil 36 daga Madina, sai suke tunani da shawara a kan komawa Madina, suna takaicin yadda dama ta kubuce musu.

Ma’abad dan Ma’aba Khaza’iy ya kasance yana cikin wadanda suke nasiha ga Annabi (SAW) ya same shi a Hamra’ul Asad ya yi masa ta’aziyyar abin da ya faru a Uhud, sai Manzon Allah (SAW) ya umarce shi da ya je ya hadu da Abu Sufyan ya kaskanta sha’aninsa, sai ya same shi a Ruha’i a lokacin sun taru za su juyo Madina sai ya tsoratar da su muguwar tsoratarwa ya ce: Lallai Muhammad ya fito da wani taro da ban taba gani ba! Zai kona ku konawa, ina ganin kada ku saki jiki har sai kun ga bullowarsu. Wannan bayani ya kada su don haka sai suka gaggauta komawa Makka.

Gargadin da Allah (SWT) Ya yi wa Musulmi na taro a kansu a fadarSa:

“Su ne wadanda suka ce da jama’a lallai mutane sun tunkaro ku, ku ji tsoransu.” Bai tasirantu a zuciyarsu ba sai ma suka kara imani suka ce a fadar Allah: “Sai hakan ya kara musu imani, suka ce Ubangiji Ya isar mana, madalla da abin dogaro.”

Sun yi kwana uku a Hamra’u sannan suka koma Madina, shi ne fadar Allah.

“Sai suka juya cikin ni’imar Allah da falalarSa, babu wani abin ki da ya shafe su, suka bi yardar Allah. Ubangiji Ma’abucin falala ne Mai girma.” (Suratu Ali Imran: 172-174)

Abin da ya faru a Raji’i

Wani mutum ya taho daga Adul da wikara ga Manzo (SAW) ya fada masa cewa akwai Musulunci a cikinsu kuma ya nema da ya tura musu wanda zai koyar da su addini ya kuma karantar da su Kur’ani, sai Manzon Allah (SAW) ya aika musu da sahabbansa 10 kuma ya shugabantar da Asim dan Sabit a kansu. Da suka je Raji’i aka yaudare su. Banu Lihyan daga Hazil suka dora yi musu ihu sai mutane kusan 100 suka taru suka kewayesu a lokacin suna wani wuri da yake tudu ne, sun yi musu alkawarin su sauko ba za su yake su ba, Asim ya ki, ya ba da umarnin kada su sauka, sai suka far musu da yaki su ma suka yake su, a yakin an kashe sahabbai 7, suka rage su uku cikin goman da aka aiko. Sai kafiran suka sake yi musu wani alkawarin, sai suka sauko suna sauka suka sake yaudararsu suka daure su sai dayan sahabban ya ce wannan ita ce farkon yaudara ya ki yarda da su sai suka kashe shi, ya rage daga Khubaib dan Addiyyu sai Zaid dan Dusna sun tafi da su Makka sai suka sayar da su.

Da ma Khubayb ya kashe Alharis dan Amir dan Naufal a ranar Yakin Badar sai ’yarsa ta saye shi ko dan uwansa, aka mayar dashi fursuna na wani lokaci daga bisani aka fitar da shi zuwa Tan’im don  a kashe shi. Sai ya yi Sallah raka’a biyu sannan ya yi roko a kansu, sannan ya ce a maganarsa “Ban damu ba, idan aka kashe ni, Musulmi ta kowane gefe Allah ne abin ambatona. Bayan ya gama fadin abin da ya fada sai Abu Sufyan ya ce shin zai faranta maka a ce Muhammadu (SAW) ne a wurinmu za mu sare wuyansa kai kuma kana cikin iyalinka? Sai ya ce wallahi ba zan yi farin ciki ba a ce ina cikin iyalina kuma Annabi (SAW) yana halin da kaya za ta cutar da shi. Sai Ukubatu dan Alharis ya kashe shi.

Shi ma Zaid (Allah Ya kara masa yarda) shi ya kashe Umayya dan Muhras Ranar Badar, shi ma an yi masa kamar yadda aka ce ga Khubaib, sai Safwan dan Umayya ya kashe shi, Kuraishawa suka aika da a ciro sashen jikin Asim a kai wa Annabi (SAW). Sai dai Allah Ya aiko an kare shi, da yake ya dauki alkawari ga Allah ba zai shafi mushiriki ba, mushiriki ba zai shafe shi ba, sai gas hi Allah Ya kare shi bayan rasuwarsa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos