Manzon Allah: Haske mai kore duhu (31)

Darasi na Talatin da Bakwai Yaudarar da Banu Kuraiza suka yi da tasirinta Banu Kuraiza sun karya alkawarin da suka yi ga Annabi (SAW), ana cikin wannan yaki ne na Khandak Shugaban Banu Nadir Yahudawan da aka kora a baya, Hayyiy dan Akhtab ya zo wurin Shugaban Yahudawan Banu Kuraiza Ka’ab dan Usaid ya shirya […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (31)

Massalacin Madina

Darasi na Talatin da Bakwai

Yaudarar da Banu Kuraiza suka yi da tasirinta

Banu Kuraiza sun karya alkawarin da suka yi ga Annabi (SAW), ana cikin wannan yaki ne na Khandak Shugaban Banu Nadir Yahudawan da aka kora a baya, Hayyiy dan Akhtab ya zo wurin Shugaban Yahudawan Banu Kuraiza Ka’ab dan Usaid ya shirya masa yaudarar ya kyautata. Sai Ka’ab ya warware alkawarin ya dawo bangaren Kuraishawa da mushirikai. Kuraiza ta kasance unguwa ce a Madina ta bangaren Kudu, Musulmi kuma na Arewacinta. Musulmi sun fuskanci matsaloli a wannan yaki amma karfin imani ya sa suka jajirce don ya zame musu kamar wani tarko da ba dama su daga saboda mugun harbin da mushirikai ke yi suna mayar musu da martani, su kuma munafukai sun yi tsammanin mushirikai za su yi nasara a kan wannan hari da suka kawo har ma su kashe Annabi (SAW), dama haka suke so. Mushirikai sun ci gaba da tsare Madina tsawon kwanuka suna ganin yawansu na jimillar mutum dubu 10, zai samu galaba ba tantama.

Ga tsananin sanyi da yunwa domin an yi fari a wannan shekara, mushirikai sun fuskanci matsala da abincin dawakansu ya kare yunwa ta dame su. Sanyin hunturu sai karuwa yake yi yana wahalar da Musulmi a kan haka Manzon Allah (SAW) ya aika wa shugabannin kabilar Gatfan, Uyaina dan Hisnu da Haris dan Awf ya nemi su janye a wannan mamayar su koma gida za a ba su daya bisa ukun dabinon Madina na tsawon shekara daya. Suka ce sai dai idan za a ba su rabi, sai Manzon Allah (SAW) ya ki yarda da haka, daga nan sai suka amince a kan yadda ya ce. Sai ga shi sun zo wurinsa a kungiyance, Manzon Allah (SAW) yana so ya san ra’ayin Sa’ad dan Mu’az da Sa’ad dan Ubada shugabannin Ansar. Da farko shi ne suka ce kai kake so ko Allah Ya yi umarni? Sai ya ce da umurni ne da na zartar da shi kai-tsaye ba zan tambaye ku ba. Kuna da zabin yarda ko rashinta. Sa’ad dan Mu’az ya ce: “Ya Manzon Allah! Mu da wadannan kabilar a da muna shirka da Allah mun bauta wa gumaka amma a lokacin ba su taba tsammanin su ci koda dabinonmu daya ba, sai fa a matsayin bakinmu ko su saya. Shi ne sai yanzu da Allah Ya karrama mu da Musulunci Ya shiryar da mu ta hanyarka Ya karfafe mu za mu ba su matsayin girmamawa? Na rantse da Allah ba mu bukatar wannan yarjejeniya abin da kawai za mu ba su kafin Allah Ya yanke hukunci shi ne takwabi!”

Manzon Allah (SAW) ya ji dadin jin haka, sai ya ce da tawagar Gatfan za ku iya tafiya yanzu, takwabi zai sasanta mu, shi kadai ne zai kawo karshen matsalarmu da ku!”

Daga nan Gatafan suka juya suka tafi. Haris dan Awf ya ce “Ba za mu tsinci komai ba a hari ga Muhammad don mu taimaki Kuraishawa, na rantse da Allah ina ganin hanyarsa ce take da fiffiko, malaman Yahudawa sun tabbatar da zuwan Annabi da yake da irin abubuwan da yake da su.”

Muminai mujahidai sun hadu da tsanani a tsarewar da aka yi musu, saboda ko hutawa ba su yi ba bayan haka ramin aka kewaye su da yaki ga gajiya ga yunwa ga sanyi. Huzaifa ya ruwaito cewa “A cikin wadannan kwanuka muna zaune, Abu Sufyan ma yana cikin askarawansa can tudun da suke, su kuma Banu Kuraiza suna kasan daya barayin, mun cika da tsoro kada su kai wa matanmu da ’ya’yanmu hari, ga duhu ko yatsunmu ba mu gani, ga iska sai ga munafukai sun zo wurin Annabi (SAW) suna neman izinin tafiya. Suka ce ‘gidajenmu suna cikin hadari,’ sai ya ba wadanda suka tambaya izini nan da nan suka tafi. Mu 300 muka yi gadin Annabi (SAW) daya bayan daya da aka zo kaina ba ni da abin kare kaina daga makiya, ba ni da abin kare sanyi sai dan wani kyalle da matata ta ba ni ko kafafuna ba zai lullube ba.’

Tun lokacin da Annabi (SAW) ya ji daga Umar cewa Banu Kuraiza sun karya alkawarinsu na ba Madina kariya da kin taimakon makiya ko wanda yake taimakarsu da rashin zartar da abin da ya shafi tsaro face da izininsa, ya aiki Zubair dan Awwam wurinsu don ya tabbatar. Yana zuwa ya ga suna ta gyara wurin da ake shamakance mata da yara don kariya idan ana yaki kuma askarawansu na shiri sai ya dawo ya tabbatar wa Annabi (SAW) abin da Umar ya fada gaskiya ne. Huyayyu dan Ahtab Shugaban Banu Nadir ya zuga Ka’ab Shugaban Banu Kuraiza ya karya alkawari. Daga nan ne Manzon Allah (SAW) ya aiki ayarin Sa’ad dan Mu’az Shugaban Awsu da Sa’ad dan Ubadah, Shugaban Khazraj da Abdullahi dan Rawaha da Hawwa dan Jubair su kara bincikarsu su yi musu nasiha don su ceto su daga abin da suka jefa kansu a ciki. Ya ce in gaskiya ce idan kun dawo ku sanar da ni ta hanyar da mutane ba za su gane ba, ni zan gane, kada ku yi bayani dalla-dalla mutane su tsorata su samu rauni. Idan kuma ba su karya ba, to, ku bayyana karara. Wadannan zababbun sahabbai suka je yankin Banu Kuraiza suka same su, suka gargade su a kan munin karya alkawarinsu kuma suka yi musu nasiha sai dai Banu Kuraiza sun yi watsi da nasiharsu karewa ma suka mayar musu cewa sun fa karya kuma “Waye ma Muhammad? Mu babu wani alkawari ko kulli a tsakaninmu.”

Wannan ayari hankalinsu ya tashi da abin da suka ji, da ma kuma akwai kullin alkawari a can kafin Musulunci a tsakanin Mu’az da Banu Kuraiza sai Mu’az a fusace ya ce, “Ina rokon Allah kada Ya kashe ni kafin in yake ku!”

Bayan sun dawo sun sanar da Annabi (SAW) sai ya ce musu ku rike sirrin, ku fada wa wadanda kawai suka san da maganar. Shi dai yaki yana bukatar taka-tsantsan da dabara!

Tsoro ya tsananta da wannan tabbaci na ha’inci Yahudawa ga kuma mushirikai na ta kawo hari ba kakkautawa.

Manzon Allah (SAW) ya samu damuwa kwarai da wannan labari ya kame a mayafinsa ya kishingida ya dade a haka sannan ya mike ya yi kabbara kuma ya yi wa Musulmi albishir na budi da samun nasara.

Daga nan Manzon Allah (SAW) ya tura Zaid dan Sabit da mutum 300 da Salama dan Aslam da mutum 200 su yi gadin Madina su rika tsaro da dare, kuma shi da kansa a ranar ya yi gadin yankin da ake zaton mushirikai za su iya kutsowa ta cikinsa. Yahudawan Kuraiza sun kai farmaki a gidan Hassan dan Sabit inda gwaggon Annabi (SAW) take, sai dai ba su samu nasara ba, sun koma a karo na biyu mutum goma suka rika harba kibau wani daga cikinsu ya yi nufin shiga, amma Safiyya ta gan shi, sai ta yi rawani ta lallaba ta kwada masa itace ya mutu. Wannan ya tsorata Yahudawa suka ce ashe akwai maza masu gadin mata da yara sai suka gudu.

Bayan abin da ya faru tsakanin Manzon Allah (SAW) da kabilar Gatafan an ci gaba da gwabza yaki wanda rami ya ratsa tsakani don haka bai samu yadda ake so ba tunda harbi ne da jifa kawai wanda ya gajiyar da mayaka ainun ga yunwa ga tsananin sanyi. Ana cikin wannan gwabzawa ce sai Nu’aim dan Mas’ud daga kabilar Gatafan ya musulunta a asirce ’yan kabilarsa ba su sani ba. Don haka ya yi amfani da wannan dama ya samu isa kusa da Manzon Allah (SAW) ya ce masa yana so ya nuna godiyarsa ta ni’imar zama Musulmi ta hanyar yi wa Musulunci aiki, me yake so yayi? Ya nemi Annabi (SAW) ya ba shi umurni sai Manzon Allah (SAW) ya ce “Kai kadai wane abu za ka iya tunkara? Amma dai za ka yi wani abu koda kai kadai ne, ka je ka raba tsakanin wadanda suka yi mana shamaki idan za ka iya! Yaki dan yaudara ne.”

 

Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141 ko [email protected]